- NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 6 February 2018

Bauta ko zalunci a Cikin Masana'antar Kannywood - Inji Jarumi Adam A Zango

A Yau wasu daga cikin Jarumai MAZA da MATA tsofaffi da manya da kananan da wani bangare na Maaikata a kannywood. Suka kai kara da kukan wasu manyan producers da kananan su.! Gurin Hukumar tace fina-finai. Kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da producers din suke musu.

A cewarsu mafi yawan ayyukan da suke da producers din basa biyansu ko kuma in zaa biya ka a baka kudin da ko na mota bazai kai ba. Ko ayi kwanaki ana aiki da kai, in an gama ace za'a kiraka, shikenan an cinye.

Arewafresh.com ta kara da cewa Tabbas duk abin da mutum sama da Ashirin Mata da maza suka fada, to lallai yana faruwa. Kuma hakan zalincine
Allah bazai kyaleba..

Yaku masu wannan dabiar, ku sani an wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai ya saka musu.

Kuma Wallhi sai kun biya su hakkin su a ranar da baku da komai sai abin da kuka jewa Allah dashi.
Ina rokon wasu daga cikin Directors,
Actors, Actresses, writers da producers.

Mu hadu domin kawo karshen Wannan zalinci.
Duk wanda aka samu a karbi hakkin wanda yaci kuma a hukuntashi.

 Muyi domin Allah bada nufin tozarci ko cin Zarafin juna ba.
Sai Dan tsaftace Masana'anta daga hannun baragurbi. Ka fara daga set din da kake.

Duk wanda kaji ba'a biya ba, ka dakatar da aikin har sai an biya hakkin mutane sannan a cigaba. Domin ni nasan ba'a film sai da kudi.

The Wallhi duk KABON wanda kaci ka shirya sauraran hkunci tun daga kabari.
Allah ka tsaremu da zalinci da cin dukiyar wadanda suka wahaltamana. Ameen.
#gyaran_karaya_movement

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment