Ga raddin Marubuci Yakubu M Kumo:
"Assalamu alaikum Ban taba magana akan duk wani al’amari da ya shafi fadan ‘yan fim ba. Sai dai dole na shiga duk wani al’amari da na ci karo da shi, wanda na ke ganin yana bukatar tsokaci a kan addini (Duk da dai ni ba malami ba ne). Na ga wani post da Bello M. Bello ya yi wanda shi a tunaninsa kamar bata sunan Ali Nuhu ya ke son yi, ko kuma martani ne mai zafi ga masoyansa. Sai dai ni a gani na wannan posting din kamar izgilanci ne ga addini, ko kuma shishshigi akan kaddara da nufin Mahaliccinmu. Ya kamata Bello ya sani, Ali Nuhu dai Musulmi ne, duk abin da ya haife shi ba zai shafi Musuluncinsa ba, da shi da kai duk daya ne a wajen Allah. Banbancin kawai shi ne ...Inna akramakum indallahi atkakum...
(mafi soyuwa a wajen Allah shi ne wanda ya fi jin tsoronsa)...(Qur’an 49:13). Sannan idan ma mahaifinsa ba Musulmi ba ne ba ka da tabbacin a haka zai mutu, tun da hadisi ya karantar da mu karara, wasu sai a karshen lokacinsu su ke samun sa’ar shiga aljanna, ke nan ashe babu wanda ya san makomar wani sai Mahaliccinmu. Don haka ba wani abin fada ba ne don mutum ya kasance Musulmi sannan uba ba Musulmi ba, in har za ka zagi Ali Nuhu saboda wannan sai ka koma ka hada da Annabi Ibrahim, saboda shi mahaifinsa ba ma Kirista ba ne, Kafiri ne mai bautar gumaka (Ka karanta suratul Maryam) Don haka in har Annabi Ibrahim (AS) wanda a tsatsonsa Annabawa kamar su Annabi Musa, Annabi Isma’il, Annabi Isa da Mafificin halitta Annabinmu Muhammad (SAW) suka fito, to waye kuma Ali Nuhu. Saboda irin wannan tunanin ne Allah Ya sake kafa misali a Suratut Tahrim, inda aka nuna matar Annabi Lut ma ba Musulma ba ce, haka kuma dan Annabi Nuhu.
Sannan Allah Ya nufi matar Fir'auna da yin imani duk da Kafircewarsa. Kowa da yadda Allah Ya nufa zai zo duniya, kuma babu wanda ya isa ya kaucewa hakan, babu wanda Allah Ya shawarta a lokacin da za a halicce shi, kowa tsintar kansa ya yi a duniyar. Kawai mu yi fatan samun kyakykyawar makoma. Ba na bangaren kowa, kuma ba na fada da kowa. Bissalam"
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment