...ficewar Kwankwaso daga APC babbaar baraka ce a Kano, cewar Aminu Dabo
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai ci, Rabi’u Musa Kwankwaso zai gana da magoya bayansa na darikar Kwankwasiyya a daren yau don tattauna batun ficewarsa tare da dubban magoya bayansa da ke a ko’ina a fadin kasar na daga jam’iyyar APC, kamar yadda majiyarmu ta 'Daily Nigeria' ta rawaito.
Tun ba yau ba ne dai Kwankwasawa ke ta yin kiraye-kiraye ga madugunsu da ya fice daga jam’iyyar APC sakamakon hanasu rawar gaban hantsi da mabiya darikar Gandujiyya ke yi a jihar Kano tun bayan da dangata ta yi tsami tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Rahotanni na nuna cewa dama dai Kwankwaso ya shirya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC a ziyarar da ya nufi yi a ranar 30 ga watan Janairu, wanda ala dole ya soke ziyarar sakamakon al’amura na tsaro da jami’an tsaro suka ce zuwan nasa ka iya gurbatawa.
Rahotanni da ke zuwa mana shi ne na cewa ba bayan Kwankwaso, akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da su ma za su bar jam’iyyar.
Tuni dai tuntuba ta yi nisa kan batun sauya shekar Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal daga APC zuwa PDP da nufin ya tsaya takarar shugabancin kasa.
Ko a baya ma dai Shugaba Muhammadu Buhari ne ya dakatar da Kwankwaso daga ficewa daga jam’iyyar APC inda ya yi alkawarin kawo karshen tsamar da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Sai dai, bayanan da suka samemu shi ne na cewar Kwankwaso da magoya bayansa za su gana a daren yau Lahadi a Abuja inda za su tattauna batun ficewa daga APC.
Majiyarmu ta bayyana cewa Kwankwaso zai bayyana jam’iyyar da shi da magoya bayansa za su koma bayan ficewarsa daga APC.
A wata hira da Aminu Dabo, wanda na hannun damar Kwankwaso ya gabatar a Abuja, ya gargadi Shugaba Buhari da shugabanci jam’iyyara APC na kasa cewa, ficewar Kwankwaso daga APC zai jawo faduwar jam’iyyar APC a jihar Kano a zabe mai zuwa domin shugaba Buhari zai rasa magoya baya a jihar.
A hirar da Aminu Dabo ya yi da manema labarai jiya Asabar a Abuja, ya bayyana cewa, Gwamna Ganduje ya kashe siyasarsa a Kano kuma yana kokarin kashe jam’iyyar APC da siyasar Shugaba Buhari a jihar.
“Gwamna Ganduje ya fahimce cewa rikicinsa da jagoranmu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jawo masa bakin jini a jihar Kano, wannan ne ya sanya shi saka uwar jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari a rikicin don ya samu tsaro daga wajensu, daga farin jininsu, amma in ba su yi sa’a ba, wannan rikici zai jawo musu matsalar da maganceta zai gagaresu. Domin kan su farga tuni abubuwa sun dade da lalacewa.
“Goyon bayan Ganduje da fadar Shugaban kasa da uwar jam’iyyar APC ke yi zai tabbatar da faduwar Buhari a jihar Kano a zabe mai zuwa kuma hakan ba karamin al’amari bane kasancewar Kano ce mafi girman cibiyar siyasar Buhari,” inji Aminu Dabo.
Dabo ya ci gaba da cewa “Rikicin Kwankwaso da Ganduje ba rikici ne da son rai ko wani abu na kashin kai ya haifar ba, musamman daga bangaren Kwankwaso. Dalilin rikicin shi ne kasancewar Ganduje ya sabawa tsari da akidar darikar Kwankwasiyya, kuma an yi ta ja masa kunne ya dawo kan hanya amma ya yi kunnen uwar shegu. Saboda haka rikici ne wanda cin amana da butulci ya haifar. Gandujen da Kwankwaso ya yi wahala wajen dasawa a gwamnati na samun kulawar da ake yi wa agolan siyasa ko bare a gwamnatin Kano. Ya kori duk wani makusancin Kwankwaso daga kusa da shi ya kawo nasa. Ya mayar da mu baki a siyasa da gwamnatin da muka kafa”
“In ba haka ba mene ne na hana mutum mai matsayin sanata zuwa ganin magoya bayansa? Muna da tabbacin cewa hukumar ‘yan sanda, fadar shugaban kasa da kuma Ganduje ne suka shirya makarkashiyar hana Kwankwaso zuwa Kano a ranar 30 ga watan Janairu,”
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment