Sharhin: IDRIS SULAIMAN BALA
A kowacce sana’a ta duniya akwai abin da a ke kira da ka’ida da dokokin gudanarwa. Wannan ba wai kawai ya takaita ga sana’o’i ba ne, abu ne wanda a ke samun shi hatta a wasu bangarorin rayuwa. Wannan walau a harkar wasan kwaikwayo na fim ne ko makamantansa.
Duk da cewa, ni ba sana’ar fim na ke yi ba kuma ban san abubuwa da dama a cikinta ba, musamman siyasar da ke cikin masana’antar, amma a matsayina na mai sharhin ya da kullum a kusan kowane irin fanni, Ina da dama da hakkin yin nazari musamman kan sana’ar da ta ke da dangantaka da harshena, wato Hausa.
Na kuduri aniyar yin sharhin nan ne domin yin lalube tare da nemo mafita duba da yadda abubuwa su ke faruwa a masana’antar shirin fim din Hausa, wato Kannywood; masana’antar da ta kumshi masu shiryawa, gabatarwa, tsarawa da kuma wadanda ke fitowa a cikin finafinan Hausa.
A duk lokacin da a ka samu taron mutum sama da daya, wadanda su ka hadu domin samar da wani abu domin amfanin al’umma, a ka’ida ta hankali wadannan mutane na bukatar wasu shimfidaddun ka’idoji da dokokin da za su rika daidaita lamurransu.
Kwararru a cikin al’umma, irin likitoci da lauyoyi duk su na da nasu shimfidaddun ka’idoji da dokoki, wadanda da zarar an samu wani ya balle ko ya saba daga jerin wadannan ka’idojin za a hukunta shi. a wasu lokutan ma, hukuncin ya kan yi tsananin da korar mutum a ke yi daga aikin gabadaya, ba wai kawai dakatarwa ko cin tara ba.
Kafin zuwan wadannan fannoni na zamani, ma’ana irinsu likitanci da aikin lauya, mun san cewa akwai wasu ayyuka da a ke bayar da gudunmawa da su domin ci gaban al’umma. A irin wadancan ayyukan, kakanninmu sun doru ne a bisa turbar kiyaye ka’ida da dokoki.
Alal misali; masunta su na da ka’idojinsu. Ba haka nan kawai da rana tsaka mutum zai kwashi jiki ya tsunduma cikin ruwa ba, a’a, ka na bukatar ka zauna da su, su sanar da kai dabarun aiki da dokoki da ka’odojin sana’ar kafin a fara kiran ka da masunci.
Mu yi dubi ga sana’ar kira; ba kawai don mutum ya wayi gari ya rura wuta shikenan ya zama makeri ba, kuma shikenan idan a ka samu matsalar gobara ko kunar wuta, zai iya bayar da magani ba.
Akwai matakai da ka’doji shimfidaddu da dole sai ya kiyaye su, kafin ya cimma wannan mataki.
Wannan ya ishi mai hankali ya iya fahimtar cewa tuntuni mu Hausawa al’umma ce mai kiyaye ka’ida a duk abubuwan da mu ke yi. Hatta a harkar bori da tsafi, ba haka nan kawai a ke wayar gari a fada mu su ba, sai ka san me a ke yi, kuma ya a ke yi.
Dukkan wadannan abubuwan da na lissafo a babin misali, su na da nasu matakan da a ke dauka a kan mutum idan ya kauce hanya. Ba wai kara zube su ke gudanarwa ba.
Kamar yadda rana tsaka ba zai yiwu mahaucin da ya kware a fidar dabbobi ya yi tsammanin cewa zai iya fede mutum ba. Duk kwarewarka a fidar dabba, babu wani nau’in haukan da zai gamsar da kai cewa za ka iya yin amfani da waccan kwarewar ta fidar dabba wurin fidar mutum. Wannan aikin likita ne; don haka dole a bar ma sa.
A ka’ida, har zuwa makon da ya gabata, gamayyar kwararru a aikin likita sun haramta wa duk wani likita yin amfani da damar da ya ke da ita wurin taimaka wa marar lafiya ya kashe kanshi.
Akwai yanayin cutar da marasa lafiya kan bukaci likitoci su taimaka mu su don su mutu; irin wannan bukatar na tasowa ne a lokacin da ciwon ya ki ci, ya ki cinyewa, kuma an rasa samo mafita gare ta.
Duk likitan da a ka samu da aikata irin wancan laifi da na kawo, za a janye mi shi shaidar zama likita. Daga wannan rana ya tashi daga matsayin kwararre, kuma bisa wannan dalili, babu wani asibiti da zai iya zuwa a dauke shi aiki, balle ya kara tafka makamancin wannan aika-aika.
Sana’ar fim wata sana’a ce mai muhimmancin gaske a cikin al’umma, domin shi mutum a rayuwarsa da dabi’arsa yana bukatar tarihi, ya na bkatar nishadantarwa, ya na bukatar darussa wadanda za su rika daidaita mi shi yadda mu’amala ta ke da yadda zamantakewa ta ke a al’ummarsa.
Wannan dalilin ne ya sa a finafinan da a ke da su, sai ya zama kowanne yanki na duniya sun yi kokarin su samar da wata inuwa wacce ita ce za ta rika lura da irin sakonnin da finafinansu za su rika fitarwa. Misali; akwai Nollywood, Bollywood, Hollywood, Kannywood da sauransu.
Ba zai yiwu alkiblar finafinan Hollywood su koma ba su da aiki sai sanya maza da mata su na tika rawa a fim ba, kamar dai yadda su kuma Bollywood zai yi wahala su sake fim ba tare da an tika rawa tsakanin namiji da mace ba. Wannan bambancin da na kawo, ya ishi zama misali gare mu gane irin mabambantan al’ummomi da mu ke rayuwa a cikinsu.
Duk da ya ke a harkar Kannywood akwai kwafe-kwafe da kwaikwayo daga bangaren Bollywood, wannan ba ya na nufin cewa kuskure a ke yi dari bisa dari a Kannywood din ba, domin ko ba komi, yanzun masu kallon finafinan Hausa sun saba, idan ma ka yi fim ba tare da sanya waka a ciki ba, ba dole ba ne ka ja hankalinsu..
Matsalolin Kannywood sun girmi a kalle su ta fuskar wai an kwaikwayi Bollywood ko Hollywood. Matsaloli ne na cikin gida wadanda tuntuni su ke addabar masana’antar finafinan Hausa, kuma har zuwa yau din nan, a sabuwar shekarar 2018, ’yan Kannywood ba su iya sun magance wa kansu wadannan matsalolin ba.
A wuri daya ka ke iya gane karfin ’yan fim din Hausa, shi ne idan su ka fara fada a tsakaninsu. Ba su iya tada jijiyar wuya a lokacin da a ka danne mu su hakkinsu ko a ka cuci daya daga cikinsu ba, sai a lokutan da za su yi wa juna tonon silili da terere a cikin al’umma.
Wasu kalaman batancin ma da su ke jifan juna da su, kwakwalwa ba za ta iya sauwalawa ba. Sun gaza fahimtar cewa, don ka zagi abokin sana’arka da cewa ba ya sallah, kai ma mai yin wannan yarfen a haka al’umma za su rika kallon ka, balle kuma ka zargi wani abokin sana’arka da cewa ya na aikata mummunar dabi’ar luwadi. A fili fa, abin da ka ke nunawa masu bibiyarku shi ne, ku ’yan fim din nan na Kannywood ’yan luwadi ne kenan.
Abinda ya sa na kawo wannan misali shi ne, saboda ba abu ne da a ka aikata shi a sirri ba, domin a cikin makon nan da ya kare ne a ka ga yadda sabanin da ya shiga tsakanin manyan jaruman Kannywood din nan guda biyu, wato Ali Nuhu da Adam Zango, ya haifar da irinsu Jarumi Bello Muhammad Bello (BMB) da sauransu su ka fito bainar jama’a su na yin yarfen luwadi ga Ali Nuhu.
Karara hakan ya nuna cewa, masana’antar Kannywood ba ta da cikakkiyar alkibla ko dokoki ko ka’idoji na zamantakewa da ladabtarwa, domin duk inda kungiyar kwararru ta ke lallai ta na kiyaye mutuncin sana’ar da masu yin ta. Don haka ko da za a zargi mai sana’ar da wani abu da zai shafi mutuncin sana’ar, sai dai wani daga waje ya aikata irin wannan zargi, amma ba dai dan halak din cikin gidanta ba, domin idan ya aikata hakan tabbas ya san cewa, kungiyarsa za ta iya hukunta shi.
Amma irin wannan tabarar da wasu jaruman Kannywood su ka aikata kan wancan sabanin, tabara ce wacce ta ke nuni da cewa, har yanzu ’yan Kannywood ba su hankalta ba. Ba da jimawa ba hotuna da bidiyo irin na su Maryam Hiyana, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi da sauransu su ka barar da mutuncin Kannywood a idanun duniya, sai kuma ga irin wannan ikirari na zahiri da su Jarumi BMB su ka yi ya biyo ba.
Shin me ya sa hakan ke cigaba da faruwa? Watakila saboda wadanda su ka aikata laifukan bayan ba a yi mu su hukuncin da ya dace da su ba ne ta yadda wadanda su ka biyo baya za su dauki darasi su ji tsoron aikatawa, saboda daga irin bayanan da na ke samu, duk wadancan jaruman da su ka aikata laifukan da a ke zargin su da shi (wato kamar Rahama, Nafisa da sauransu) a lokacin da a ka yi yunkurin hukunta su, an samu wasu jiga-jigai da ke goyon bayansu, saboda kawai su na da alaka da su ko kuma don ba su shiri da shugabannin da su ka yi hukunta su.
Wani abin misali a kwana-kwanan nan shi ne, yadda shugaban hukumar tace finafinai na jihar ta Kano, Isma’il Na’abba Afakallahu, ya halarci taron bikin zagoyawar ranar haihuwar daya daga cikin wadancan jarumai da hotunan badalarsu ya taba bayyana har a ka hukunta su, wato Nafisa Abdullahi, kuma a wajen bikin har wai ta kai ga ba shi abinci a baki.
Idan hakan ta tabbata, shin in har yanzu kamar shi Afaka bai hankalta ba, to ina Kannywood ta dosa kenan? Kada a manta fa, Malam Afakallah na daya daga cikin shugabannin kungiyoyin Kannywood kafin ya zama shugaban hukumar tace finafinai na jihar.
Abinda yakamata gabadayan ’yan Kannywood su gane shi ne, kare sana’ar tasu bakidaya daga zubewar mutunci shi ne abinda dukkansu su ke bukata, amma ba kare muradin aboki ko kawa da wasu makusanta ba.
Hakika lokaci ya yi da ’yan Kannywood za su hankalta! Idan kuma ba haka ba, nadama na nan tafe!!! Allah Ya kiyaye!!
source from Leadership Hausa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment