`A yau Litinin, 5 ga watan Junairu, 2018 ne aka koma shari'ar Maryam Sanda a kotu bisa ga zargi da tuhumar kisan mijinta da makami.
Lauyan Maryam Sanda, Joseph Daudu, ya laburtawa alkalin kotun cewa mai laifin na dukae da juna biyu na tsawon watanni uku saboda haka yana bukatar kotun ta baiwa mai laifin beli.
Kasancewan Maryam Sanda na tsare kurkuku kuma daga nan ake kawo ta kotu, lauyanta ya nemi alfarman kotu da ta ba maryam damar cigaba da halartar kotu kan karar ta daga gida ba domin kula da juna biyun da take dauke dashi.
Joseph Daudu ya sha alwashin tabbatar da zuwan Maryam Sanda kotu duk duk lokacin kotu ke bukatan ganinta.
Alkalin kotun, Yusuf Halilu ya daga karar zuwa ranan 7 ga watan Fabrairu domin zartar da hukunci kan bukatar da ta nema.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment