Gane Mini Hanya : Hukumar SUBEB ta Hana Wazifa a Makarantun Tsangayar Bauchi - NewsHausa NewsHausa: Gane Mini Hanya : Hukumar SUBEB ta Hana Wazifa a Makarantun Tsangayar Bauchi

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 20 February 2018

Gane Mini Hanya : Hukumar SUBEB ta Hana Wazifa a Makarantun Tsangayar Bauchi

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kula da ilimin bai daya wato SUBEB sashinj jihar Bauchi ta bukaci makarantun Tsangaya da su daina yin wazifa ko karanta salatul fatihi a hidimar makarantar.

A cewar hukumar hakan baya daga cikin tsarun makarantun a fadin jihar da ma tsarin hukumar UBEC ta fitar akan karatun Tsangaya.

Wannan bayani na tattare ne a wata takarda da shugaban hukumar ta SUBEB Yahaya Ibrahim Yaro ya fitar da sanya hannun sakataren hukumar Mahmeed A. Kari.


An saki wasikar ne a ranar 5 ga watan Fabairu mai taken wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.



Hukumar ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi.

Jaridar Leadershin ta rahoto cewa wannan mataki bai yi wa mamallakin wannan makarantar Tsangayar Sheikh Dahiru Bauchi dadi ba.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment