Da dumi-dumi: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa - NewsHausa NewsHausa: Da dumi-dumi: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa

Pages

LATEST POSTS

Thursday 8 February 2018

Da dumi-dumi: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa

Allah ya yiwa wata surukar shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Mamman, rasuwa.

Maragayiya Hajiya Aisha Mamman ta rasu ne safiyar yau Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2018.
Shugaban labarai na karamar hukumar Daura, Alhaji Salisu Haro, ya bayyana wannan rashi a garin Daura.

Ya ce maragayiyar ta cika ne misalin karfe 11:30 na safe a babban asibitin jihar Katsina bayan gajeren rashin lafiya.

Alhaji Haro ya kara da cewa Hajiya Aisha ta kasance uwargidan marigayi Alhaji Mamman Danbaffale, yaya ga shugaba Buhari.

Hajiya Aisha ta rasu ta bar ‘yaya takwas da jikoki. An birne bisa ga koyarwan addinin Musulunci.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment