Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid - NewsHausa NewsHausa: Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid

Pages

LATEST POSTS

Friday 16 February 2018

Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid

Dan wasan gaba na Kungiyar Tottenham Harry Kane ya
cimma yarjejeniya da Real Madrid kan sauya sheka zuwa
gareta idan aka bude kasuwar ‘yan wasa ta gaba.

Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Spain 'Don
Balon' ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa
Real Madrid hannu kan yarjejeniyar murza mata leda tsawon
shekaru 5.

Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan
Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin
Madrid din da kuma Tottenham kan farashin Harry Kane.

An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya
sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta
dada haskawa a fagen zura kwallaye.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment