MARTANI Duk Wani Mawaki Ko Dan Fim Da Za Ka Ji Yana kalubalantar Buhari Ko Gwamnatinsa Dan Maula Ne - Inji Saeed Nagudu - NewsHausa NewsHausa: MARTANI Duk Wani Mawaki Ko Dan Fim Da Za Ka Ji Yana kalubalantar Buhari Ko Gwamnatinsa Dan Maula Ne - Inji Saeed Nagudu

Pages

LATEST POSTS

Monday 19 February 2018

MARTANI Duk Wani Mawaki Ko Dan Fim Da Za Ka Ji Yana kalubalantar Buhari Ko Gwamnatinsa Dan Maula Ne - Inji Saeed Nagudu



Da yawa daga cikin irin su suna zuwa Abuja wajen barayin Gwamnanti musamman Gwamnatin PDP da Allah ya kawar da zalincin ta a kasar nan. Ba za mu hana ku sukar Baba Buhari ba domin kuna da ra'ayi. Amma fa ku sani shi ra'ayi ba hauka bane. 

Mene ne laifin Baba Buhari dan ya hana satar kudin talakawan da ake diba a baku a banza?

Shi ne za ku dinga sukar Gwamnanti. Duk da cewa ra'ayi kowa da irin na shi, mma ni na san da yawan  mawaka da 'an fim dake sukar Baba Buhari ba mutanen kirki bane wallahi. 

Buhari shugaban kasa ne ba wai dan wasan fim ko waka ba, kamata ya yi mu wayar da mutane abin kirki ba wai sukar Buhari ba.

A Karshe idan kuna taya iyayen gidanku barayin Gwamnanti sukar Buhari ne, mu ma masoyan shugaban kasa Muhammadu Buhari da muke kannywood ba za mu yi shiru ba, ba za mu yi shiru mu zuba muku ido ba. Yadda kuke tutiya 'yan Nijeriya ne ku, mu ma 'yan Nijeriya ne, muna da 'yancin kare Gwamnantin Buhari.

Allah ya karam wa shugaban kasa lafiya da daraja. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a Nijeriya baki daya.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment