Duk wanda zai shiga aikin da'awa ,da kiran mutane zuwa ga gaskiya,dole ne ya shirya wa duk wani kalu-bale ,ya sani cewa, za a fuskance shi da tambayoyi daban-daban ,wasu da niyyar neman karuwa,wasu kuma da zimmar kure da muzantawa ,Don haka dole ne mai da'awa ya kasance mai yawan karance-karance domin ilimantar da kansa da kuma fuskantar irin wancan kalu-balen .
Dubi yadda kuraishawa suka tasa Annabi (S.A.W) gaba da tambaya game da labarin zul-karnaini don su kure shi su tozarta shi. Allah yace ,
"Suna ta tambayarka game da zul-karnaini .kace, ba da dadewa ba zan karanta muku labarin sa".[Al-kahfi,83].
Dan Allah kuyi share zuwa ga yan uwa musulmi domin kai ma ka samu lada ya da Alkhairi.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment