Tambaya?
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu, tambaya ita ce yaya za'a raba gadon budurwa wacce ba tayi aure ba, ba uwa da uba sai Yan'uwa da uwansu daya, maza 3 da mata 3, sai kuma wanda ubansu 1, mata 4, da maza 3? Dan Allah malam a taimaka bukatar hakan ya taso ne.
Amsa
Wa alaikum assalam
Za'a raba abin da ta bari gida uku: a bawa 'yan'uwan da suka hada uwa kawai kashi daya, su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da mace, ragowar kashi biyun kuma sai a bawa 'yan'uba su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
22/2/2017
Dr Jamilu Zarewa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment