Firsuna 367 sun rubuta jarabawan JAMB yau - NewsHausa NewsHausa: Firsuna 367 sun rubuta jarabawan JAMB yau

Pages

LATEST POSTS

Saturday 13 May 2017

Firsuna 367 sun rubuta jarabawan JAMB yau



- A yau ne ranan gudanar da jarabawan JAMB

- An bada rahoton cewa yan gidan yari samada 300 zasu rubuta jarabawan

Shugaban kwamitin labaran hukumar gudanar da jarabawan shiga jami’o’in Najeriya wato JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya bayyana cewa firsuna 367 harda guda 60 daga gidan yarin Kirikiri da ke Legas, zasu rubuta jarabawan a yau.

Shugaban hukumar, Is-haq Oloyede, yayi bayani a wata hira da manema labarai cewa sakonnin da ke yawo cewa an daga jarabawan bogi ne. saboda haka, dalibai su shirya zaman jarabawan kuma su isa wajajen da aka shirya musu da wuri.


Firsuna 367 sun rubuta jarabawan JAMB yau

Yace hukumar ba zata gudanar da wani jarabawa bag a wadanda basu daman yi da gangan ba.


Yace an damke wani mai shagon yanar gizo a Abuja wanda ke karban N10,000 hannun dalibai domin fitar musu da takardunsu. Yace kada kowai dalibi ya biya wani kudi a wajen jarabawa kafin ya rubuta.

Rahoto:naij.com

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment