An bayyana sakin yara ratata da Al'ummar musulmin Nijeriya musanman na yankin Arewa keyi da sunan Almajiranci da cewar ba dabi'ace ta Musulmi ko kuma karantarwar addinin Musulunci ba, kuma hakan yana bata sunan Musulunci da Musulmi a tarayyar Nijeriya.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa'adu Abubakar a yayin da yake jawabin bude taro wanda Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta shirya da yake gudana yanzu haka a babban zauren taro na Kungiyar dake kan Titin Ali Akilu a garin Kaduna Jiya Lahadi.
Sarkin Musulmin ya kara da cewar nauyi ne wanda ya rataya a wuyan shugabanni suga cewar sun tashi tsaye wajen yakar talauci a tsakanin jama'a, wanda hakan ne ya sanya Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmin fitar da wani tsari na Zakka da wakafi, domin kai dauki ga jama'a musanman wadanda talauci ke addaba, domin tsamar dasu daga halin kunci da suke ciki, kuma domin samun kyakkyawar Al'umma Musulma wacce kasa zatayi alfahari dasu.
A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa'I ta bakin wakilin shi Kwamishinan ayyuka na musanman Alhaji Shehu Balarabe, ya tabbatar da cewar gwamnatin Jihar ta shirya tsaf wajen tsaftace Jihar daga fitinan Mabarata, da kuma tabbatar da samuwar 'ya'ya nagari a jihar wadanda zasu zama abin kwatance a fadin kasar gaba daya.
SOURCES:AMINIYA
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment