Mai-dakin marigayi Firayim-Ministan Nijeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa ta ce marigayin ya samu labarin cewa za a kashe shi gabanin juyin mulkin farko da aka yi a kasar.
Sai dai Hajiya Jummai ta shaida wa BBC Hausa cewa marigayin bai dauki wani mataki ba ne saboda ya fawwala komai ga Allah.
Hajiya Jummai ta gaya wa wakilinmu, Is'haq Khalid, irin abubuwan da suke tunawa game da Sir Abubakar Tafawa Balewa:
Ta kara da cewa sun samu labarin rasuwarsa ne daga wajen wazirin Bauchi, Alhaji Yakubu Wanka, mako guda bayan an kashe Sir Balewa a Legas, tana mai cewa a lokacin ita da wasu iyalinsa suna Bauchi.
Hajiya Jummai ta kara da cewa, "Da farko an zo an gaya mana cewa an kashe Sardau, amma shi Firayim Ministan ba a san inda yake ba. Wannan shi ne farkon tashin hankalin da muka shiga. Sai bayan sati daya aka ga gawarsa, mu a lokacin ma ba mu sani ba."
Ta kara da cewa marigayin ya mutu ya bar mota biyu da gida guda biyu na kasa, tana mai cewa kudin da ya bari fam goma ne kawai.
Sai dai ta ce gwamnati ta gyara musu gidan da suke ciki, kuma wasu daga cikin yaransa suna taimaka musu.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment