Tarihin tsofaffin 'yan wasa da nasarorinsu - NewsHausa NewsHausa: Tarihin tsofaffin 'yan wasa da nasarorinsu

Pages

LATEST POSTS

Saturday 6 May 2017

Tarihin tsofaffin 'yan wasa da nasarorinsu


BBC ta yi duba kan sauran 'yan wasa, wadanda suka dade a kungiyoyinsu, kuma suka samu manyan nasarori.
Gwarzon dan wasan Italia da Roma Francesco Totti ya fidda sanarwar cewa zai yi ritaya a karshe kakar wasa ta bana.
Dan wasan mai shekara 40, ya ci kwallo 307 a wasanni 783 da ya yi, a shekara 24 a kungiyarsa ta Roma.

Ya samu nasarar daukar kofin duniya da kasarsa ta Italiya a shekarar 2006, ya kuma dauki kofin Serie A daya, da kuma kofin Coppa Italiya sau biyu.

Roger Milla

Dan wasan gaba na kasar Kamaru, wanda ya lashe kofin Afirka da Kamaru har sau biyu, ya kuma dauki kofin Coupe de France da Monaco da Bastia, ya kuma buga gasar kofin duniya a 1982 zuwa 1990.

Baya ga nan kokarinsa a gasar kofin duniya a kasar Italiya a wadannan shekaru, ya sanya shi zama gwarzo lokacin yana shekara 38.

Milla ya ci wa Indomitable Lions kwallo hudu, tare da taimakon Gary Lineker da kuma Lothar Matthaus.
Rawar da yake yi yayin da ya ci kwallo ta zama wata babbar sara da aka rika amfani da ita a wancan lokacin a tarihin kofin duniya.

Ya yi ritaya a shekarar 1996 yana mai shekara 44, bayan ya buga gasar kofin duniya a shekarar 1994, a inda ya kara zura kwallo, wanda hakan ya sanya shi zama dan wasa mafi yawan shekaru da ya zura kwallo a tarihin gasar.
Ya yi wasa har sau 666 a kungiyoyin Kamaru da Faransa, wadanda suka hada da Tonnerre Yaoundé, da Montpellier, da kuma St Etienne, inda ya ci kwallo 405.

Juan-Sebastian Veron

Duk da cewa bai samu kyakkyawar tarba a kungiyoyin Manchester United, da Chelsea, da ke Ingila ba, dan wasan tsakiyar na Argentina ya yi wasa a kungiyoyi tara a shekara 23 da ya yi yana wasa, inda kuma har yanzu yake taka leda.
Yanzu haka yana wasa ne a kungiyar La Plata, da ke Argentina, ya yi wasa a Italiya da kungiyoyin Parma da Lazio, da kuma kungiyoyin Boca Juniors da Brandsen da ke Argentina.

Da farko dai ya yi ritaya a shekarar 2014, amma kuma ya dawo fagen daga a wannan shekarar, yana mai shekara 41, bayan da ya alkawarta dawo wa idan magoya bayan kungiyar suka sayi kashi 65 cikiin 100 na rigunan kungiyar, wadanda kuma suka yi hakan.

Kazuyoshi Miura

Dan wasan gaba na Japan ya zama mutum na farko da ya zura kwallo yana mai shekara 50 a gasar J-League a watan Maris, lokacin da ya sanya kwallo a raga, a wasan da kungiyarsa ta Yokohoma FC ta doke Thespa Kusatsu da ci 1-0, yana mai shekara 50 da kwana 14 a duniya.

Tsohon dan wasan Japan din ya fara wasa ne a shelkarar 1986.
Ya yi wasa a kungiyoyin Santos ta Brazil, da Genoa ta italiya, da Dinamo Zagreb ta Croatia a dogon zangon shekara 31 da ya yi yana wasa.

Aleksandar Duric

An haife shi a kasar Bosnia ta yanzu a shekarar 1970, An fara sanya Duric wasa a kungiyar Yugoslav People's Army yana mai shekara 17, kafin ya fara wasansa a matsayin dan wasan gaba na kungiyar nomadic, inda ya yi wasa sau 600 a kungiyoyi 14 a Australia da Singapore.
Daga karshe dai ya samu nasarar zama dan Singapore a shekarar 2007, yana mai shekara 37.

Duric ya yi wa kasarsa wasanni 53, inda ya ci mata kwallo 24, ya kuma yi ritaya a shekarar 2014, yana mai shekara 44, bayan ya kwashe shekara hudu a kungiyar Tampines Rovers da ke Singapore, inda yanzu yake aiki a matsayin cikakken Koci - shekara 22 bayan kakarsa ta farko a kungiyar Szeged LC da ke kasar Hungary.

Socrates

Gwarzon dan wasan tsakiya na Brazil, ya yi wa kasarsa wasa har sau 60, in da yi ci mata kwallo 22, a tsawon shekara 15 da ya yi yana wasa, a kungiyoyin Botafogo da Corinthians da ke kasar ta Brazil.

Socrates ya kulla kwantiragin wata daya da kungiyar Garforth Town da ke ingila a matsayi koci, kuma ya yi wasan minti 12 da kungiyar ta kara da Tadcaster Albion a shekarar 2004.
Ya mutu a shekarar 2011, yana mai shekara 57.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment