Me 'yan Nigeria ke cewa kan alƙawurran Buhari? - NewsHausa NewsHausa: Me 'yan Nigeria ke cewa kan alƙawurran Buhari?

Pages

LATEST POSTS

Sunday 28 May 2017

Me 'yan Nigeria ke cewa kan alƙawurran Buhari?


Yayin da Nijeriya ke cika shekara biyu a ranar Asabar da hawan Muhammadu Buhari karagar mulki, wasu 'yan ƙasar tuni sun fara yanke kauna, ganin ya cinye rabin wa'adin mulkinsa ba tare da cika wasu manyan alkawurran da ya yi ba.

Da dama dai na zargin cewa wasu mutane ƙalilan ne suka yi baba-kere a gwamnatin Muhammadu Buhari, yayin da wasu ke cewa ko a iya nan shugaban ya tsaya, ba shakka ya taka rawar-gani.

Batun taɓarɓarewar tsaro da karayar tattalin arziki da uwa-uba cin hanci da rashawa na daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya lokacin da Buhari ya karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Shugaban dai tun lokacin yaƙin neman zabe, ya faɗa wa 'yan Nijeriya cewa ya ji ya gani, kuma zai iya, har ma ya nanata irin waɗannan alƙawarrun a yayin rantsuwar kama aiki, abin da ya ƙarfafa gwiwoyiin `yan ƙasar da dama tare da sanya ɗumbin fata.

Boko Haram

Rikicin boko-haram za a iya cewa shi ne gaba-gaba a tsakanin matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya, wanda ke haddasa asarar dubban rayukan jama`a, kuma Shugaba Buharin ya ɗauki matakin yankan shakku kan aniyarsa ta yaƙi da 'yan tada-ƙayar-baya.
Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin mai da hankali kan yaƙi da Boko Haram, inda ya mayar da shalkwatar rundunar sojin ƙasar zuwa birnin Maiduguri, inda mayaƙan suka fi karfi.

Wannan mataki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka na yin fito-na-fito da Boko Haram, kamar yadda mahukunta da ɗumbin `yan Najeriya ke cewa ya taimaka wajen karya-lagon 'yan ƙungiyar.
Dakarun sojin Nijeriya sun sake kwato yankunan ƙasar waɗanda 'yan tada-ƙayar-bayan a shiyyar arewa maso gabas suka mamaye a baya.

Sai kuma nasarar da gwamnatin ta cimma wajen ceto wasu daga cikin `yan matan sakandaren Chibok, duk da yake wasu `yan kasar na ci gaba da jayayya kan salon musayarsu da wasu kwamandojin Boko Haram.

Cin hanci da rashawa

Wani abin da ake yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari a kai shi ne rawar-ganin da take takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Wasu dai na ganin an samu nasara, don kuwa a karon farko an gurfanar da wasu manyan jami`an gwamnati da alkalai har ma da shugabannin siyasa da ake zargin sun tafka almundahana da dukiyar ƙasa a gaban kotu.

Amma wasu na zargin cewa yaƙin ya fi karkata a kan `yan adawa ko waɗanda ba sa ɗasawa da sabuwar gwamnati.
Sai dai shugaba Buhari ya ce bai kullaci kowa ba, don haka ba shi da niyyar ramuwar gayya.

Shugaban Nijeriyar ya yi yunkurin sauya tsarin kyautata rayuwar al`ummar yankin Niger-delta mai arzikin mai.

Sai dai wannan albishir na inganta rayuwar al`ummar Niger-Delta bai ratsa zukatan masu ta-da-kayar-baya ba, idan aka yi la'akari da irin luguden bama-baman da suka yi ta yi a kan bututan mai da iskar gas da ke yankin.

Hakan dai ya haddasa asara mai yawa tare da rage yawan man da Nijeriya ke fitarwa, ga kuma jefa al`ummar ƙasar a cikin matsalar ƙaranci ko rashin wutar lantarki.
Ko da yake, za a iya cewa harin ya lafa a ɗan tsakanin nan, bayan wani rangadi da muƙaddashin shugaban ƙasar Yemi Osinbajo ya kai yankin.

Samar da ayyuka musamman ga matasa

Shirin bunkasa noma da Npower da wasu makamantansu na cikin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta bijiro da su don samar da hanyoyin dogaro da kai a tsakanin matasa.

Za a iya cewa matasa da dama sun samu tallafi, amma har yanzu akwai wasu miliyoyi da ba su da aikin yi a Nijeriya.

Yayin da gwamnatin shugaba Buhari ke lissafa irin nasarorin da ta samu wajen sauke alƙawuran ta yi wa `yan Nijeriya, wasu kuma na ganin cewa akwai wasu manyan alƙawurran da shugaba Buhari ya yi, waɗanda har yanzu ba su gani a kasa ba.

Ko da yake, mahukunta na zargin cewa harin da masu fafutukar `yanta yankin Niger-Delta ke kai wa na shafar ƙoƙarin inganta hasken lantarki.

Har ila yau, akwai masu zargin cewa shugaban ƙasar ya mai da wani ɓangare saniyar-ware ta fuskar naɗin muƙaman gwamnati, alhali yana iƙirarin cewa shi na kowa ne:

Sarkin kabilar Ibo mazauna Kano Eze Dr Boniface ya ce Buhari mutumin kirki ne shi ya sa mutane suke binsa, amma kuma inda ya gaza shi ne rashin tafiya da 'yan kabilar Ibo a gwamnatinsa.
"Laifinsa, ina gani bayan ya ci zaɓe sai ya bar 'yan kabilar Ibo a baya, bai ba su mukamai ba."
Sai dai shugaban Nijeriyar ya yi watsi da wannan zargin, inda ya ce gwamnatinsa ba ta nuna bambanci.
Yanzu dai shugaba Buhari ya cika shekara biyu a kan karagar mulki, wato ya ci rabin wa`adin mulkinsa, kuma `yan Magana kan ce juma`ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta.

Ko me `yan Najeriya za su ce game da tafiyar?

Wannan ya ce: "Mun zaɓi Buhari don buƙatar zaman lafiya, gaskiya ina nan a kan bakata na son mulkin Buhari."
Shi ma wani cewa yake yi: "Buhari! Ni, ina goyon bayansa ɗari bisa ɗari, i(da)n Allah ya yarda zan sake zaɓensa''
"Gaskiya na zaɓi Buhari, amma shekara biyu ban ga wasu abubuwan ku zo ku gani ba, gaskiya yanzu na dawo daga rakiyarsa," in ji wani ɗan Nijeriyar.

Shi kuwa wannan: "Gaskiya ni ma masoyin Buhari ne amma a da, sai dai yanzu ina ganin mun samu canji ne irin na rigar mahaukaci, ya cire ta jikinsa ya ɗauko ta bola ya saka."

Mahukunta dai na cewa shekara biyu ba ta kai mizanin da za a yi kididdige tasirin mulki da ita ba, a ƙasa mai tarin matsaloli irin Nijeriya, amma masu sukar gwamnati na cewa gwamnati Muhammadu Buhari ta ƙare gudu saura zamiya, lokaci ya ƙure, don kuwa a cewarsu shekara biyun da ta rage, ta ruguntsumin siyasar babban zaɓe ce.

Rahoto:bbchausa_com

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment