Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa. - NewsHausa NewsHausa: Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa.

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 1 August 2017

Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa.



Biyo bayan wasu rahotanni da suka mamaye kafafen sadarwar zamani a daren jiya, kan batun dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren jiya ko safiyar yau Laraba, sashin watsa labarai na fadar shugaban kasa sun ce basu da masaniya kan wannan batu.

Batun dawowar shugaban kasar dai ya zafafa ne bayan rahotannin da aka samu na cewar jirgin dake jiran shugaban kasa wacce kwanaki baya aka dauko hoton ta a filin fakin na filin saman birnin London ta tashi zuwa Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce shi bashi da masaniya akan wannan rahoto. Haka zalika shima Femi Adesina ya ce idan har shugaban kasa zai dawo ana sanar dasu, amma izuwa yanzu basu da wani rahoto dangane da batun.

Yanzu dai ta tabbata cewar babu wani ingantaccen bayani kan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a yau Laraba

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment