Dalilin da ya sa na fito a Barauniya — Hafsa Idris (barauniya) - NewsHausa NewsHausa: Dalilin da ya sa na fito a Barauniya — Hafsa Idris (barauniya)

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 16 August 2017

Dalilin da ya sa na fito a Barauniya — Hafsa Idris (barauniya)

Jaruma hafsat idris barauniya



Hafsa IdrisHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAFSA IDRIS
Image captionHafsa Idris ta fito a manyan fina-finai da dama tun bayan fara fim dinta

Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi.
Hafsa, wacce ake kira 'Barauniya' ko 'Yar Fim a Kannywood, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahayacewa ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza.
Ta kara da cewa, "Yin fim ya fi aikin gwamnati domin kuwa abin da nake samu ma'aikacin gwamnati ba zai samu ba."
Da fim nake yin hidimomina da na iyayena da na 'yan uwana," in ji jarumar.
Ta kara da cewa ta koyi darasi da dama daga fim din "Barauniya" wanda shi ne na farko da ta fara yi a Kannywood.
Na fahimci "yadda barayi ke sata da kuma yadda satar ke tagayyara wadanda aka yi wa".
"Na nuna jarumta da rashin tausayi da dabaru irin na barayi," a cewar Hafsat idris
"A zahiri ni ba barauniya ba ce, ba ni da son zuciya amma da yake so ake a nuna yadda ake yin sata da kuma irin illarta ga al'umma shi ya sa na amince na taka wannan rawa," in ji ta.
Jarumar, wadda ta soma fim a watan Disambar 2016, dalilin yin fim din Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.
Ta ce kowanne wata tana yin fim uku zuwa hudu saboda "amincewar da furodusoshi" suka yi mata wajen taka rawa a manyan fina-finai.
Jarumar ta ce tana ci gaba da "gogewa shi ya sa ma na fito a fina-finai irin su 'Yar Fim da Rariya da Maimunatu da Wata Ruga da sauransu."
Sai dai masu sharhi na ganin akwai jan aiki a gabanta ganin yadda Kannywood ke cike da jarumai masu tashe.

Hafsa Idris ta fito a fina-finai da Ali Nuhu da Adam ZangoHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAFSA IDRIS
Image captionHafsa Idris ta fito a fina-finai da Ali Nuhu da Adam Zango
Hafsa IdrisHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAFSA IDRIS
Image captionJarumar ta ce fim ya fi aikin gwamnati samun kudi


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment