Nnamdi Kanu Ba Shi Da Bambanci Da Muhammad Yusuf (shugaban boko haram) - NewsHausa NewsHausa: Nnamdi Kanu Ba Shi Da Bambanci Da Muhammad Yusuf (shugaban boko haram)

Pages

LATEST POSTS

Monday 28 August 2017

Nnamdi Kanu Ba Shi Da Bambanci Da Muhammad Yusuf (shugaban boko haram)


Daga Muslim M Yusuf

Tun farko gwamnatin Najeriya bai kamata ta yi sakacin sakin tsagera irin Nnamdi Kanu ba. Domin Nnamdi Kanu ba shi da bambanci da tsohon shugaban Boko Haram, Muhammad Yusuf.

Haka su ma wadanda suka tsaya masa wajen karbar belin sa a kotu ya kamata a kamo su.

Illar Nnamdi Kanu ta fi muni fiye da na jagoran Boko Haram Muhammad Yusuf, kudirinsu iri daya ne, su tarwatsa kasa su mutu su bar al'umma da bala'i. Amma gwamnatin Nijeriya ta yi shiru ba ta cewa komai a game da shi har yana nunawa gwamnati yatsa, amma an kasa cewa uffan, ko saboda ba dan Arewa bane ya sa aka kyale shi?

Bayan ya ketare duk dokokin da aka gindaya masa daga kotu kafin a bayar da belin sa, suma wadanda suka tsaya masa su kansu an kyale su ko tuntubar su ba a yi, bayan an ba su sharudda suma.

Idan kuwa har za a iya kyale shi ya ci gaba da wannan abin, to lallai gwamnati ta saki jagoran mabiya Shi'a Sheik Ibrahim Zakzaky.

Fatan mu Allah ya kawo mana sauyi nagari.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment