Kannywood: Babban buri na shine inyi aure, in zama uwa - Rahma Sadau - NewsHausa NewsHausa: Kannywood: Babban buri na shine inyi aure, in zama uwa - Rahma Sadau

Pages

LATEST POSTS

Friday 5 January 2018

Kannywood: Babban buri na shine inyi aure, in zama uwa - Rahma Sadau

Fitacciyar jarumar nan dake yin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana wa duniya babban burin ta a rayuwa a halin yanzu.

Jarumar dai ta bayyana cewa ita yanzu bata da burin da ya wuce tayi aure sannan ta kuma haihu ta zama uwa.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne lokacin da take bayar da ansa ga masoyan ta da ta damar yi mata tambaya a shafin ta na dandalin zumuntar zamani na Instagram a kwanan baya.

An tambayeta wanda ya koyamata rawa?

Ta amsa cewa “Ali Nuhu.”

Me ta fi jin tsoro a duniya?
Ta ce “mutuwa.”

Yaushe za ta yi aure?
Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.

Shin za ta iya daina fim?
Ta ce “a’a.”

Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa
Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.”

Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta
Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate”

An tambayeta ko shekarunta nawa?
Ta ce, “24.”

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment