Ta Faru Ta Kare : Hukumar Moppan Ta Yafe Wa Jaruma Rahama Sadau - NewsHausa NewsHausa: Ta Faru Ta Kare : Hukumar Moppan Ta Yafe Wa Jaruma Rahama Sadau

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 9 January 2018

Ta Faru Ta Kare : Hukumar Moppan Ta Yafe Wa Jaruma Rahama Sadau



Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ta
yafe wa fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau dukkan laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka hana ta yin fim.

Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakalla, ya shaida cewa, "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".

Afakalla ya kara da cewa sun dauki wannan
mataki ne bisa la'akari da gafarar da jarumar ta nemi a yi mata kwanakin baya.

A cewarsa, "Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan
abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta
al'umar da take ciki.

"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda
kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi", in ji shi.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment