- Jarumar ta haska a wasan Hausa mafi tsada, Gwaska
- Jarumar ta ce tana matukar kaunar tufa
Hajarah Isah, sabuwar jarumar wasan Hausa, na samun karuwar farinjini da daukaka a masana'antar Kannywood bayan rawar da ta taka a shirin wasan kwaikwayon Hausa mafi tsada, Gwaska.
Masu nazarin wasanni masana'antar Kannywood sun tabbatar da cewar ba'a taba kashewa wani shirin fim din Hausa kudi ba kamar yadda aka kashe a shirin wasan Gwaska ba.
Sabuwar jaruma Hajarah Isah
Jaridar Premium Times ta tattauna da jarumar a Abuja. Mun tsakuro maku daga cikin tattaunawar.
An tambayi jarumar yadda ta fara shiri a masana'antar Kannywood da taka rawa a cikin fitaccen shiri kamar Gwaska.
Jarumar, mai shekaru 22 a duniya, ta ce "Gaskiya na yi matukar sa'a da masu shirya fim din Gwaska su ka ga cancanta da dacewa ta a cikin shirin. Shine shirina na farko. Adam Zango ya kashe fiye da miliyan bakwai wajen shirin fim din Gwaska."
Hajarah ta kara da cewar ta fito a cikin shirin a matsayin 'yar sanda, ta nuna gamsuwar ta da matakin da aka dora ta a fim din domin a cewar ta fitowa a shirin Adam Zango ba kankanin abin alfahari ne, kowanne irin mataki mutum ya taka a shirin.
Jarumar ta bayyana cewar babu abinda zai dakatar da ita daga cigaba da fitowa a shirin wasan Hausa, "burina na zama zabin kowanne Furodusa a masana'antar Kannywood tunda ina da karancin shekaru," a cewar Hajarah.
Hajarah ta ce burinta a masana'antar Kannywood ta zama shahararriyar jaruma kamar Jamila Nagudu da Hadiza, jaruman da ta ce su na matukar burge ta.
Hajarah ta ce tafi kaunar tufa a cikin nau'in abinci.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment