Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin shugaba muhammadu Buhari bisa ga rashin aiwatar da kyawawan ayyuka kana ya shawarce shi da kada ya nemi zarcewa a zaben 2019.
Tsohon shugaban kasa ya bayyana ra'ayin sa game gwamnatin shugaba Buhari a wata faifan takarda wanda aka fitar ranar talata 23 ga wata janairu 2018.
Cikin takardar mai taken "The Wat Out: A Clarion Call for Coalition for Nigeria Movement", Obasanjo ya bayyana wurare da gwamnatin Buhari ta gagara samun nasara musamman a bangaren kasuwanci.
Yace shugaban yayi aiki ne kasa da yadda jama'a suka yi tsammani bisa ga haka ya dakatar da anniyar sa na zarcewa a zaben 2019.
Tsohon shugaban kasa wanda yayi mulki tsakani 1999 zuwa 2007 yayi kira ga shugaba Buhari da ya zamanto mai bayar da taimako a shugabancin kasar nan gaba domin yin haka zai fi muhimmanci a kasar dama sauran kasashen duniya.
Bugu da kari Obasanjo ya soki shugaban bisa ga akidar nuna fifiko a gwamnatin sa tare da irin dabi'ar rikon-sakai- na ksashi na shugaban ke nuna ga muhimman abubuwa dake wakana a kasar.
Daga karshe Obasanjo yace shugaba Buhari baya da kwakwarar ilimin siyasar kasar kuma bisa ga wannan dalilin ya haifar da rarrabuwar kai a fadin kasar.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment