– Ministan Sufuri Rotimi Amaechi na cikin matsala a game da harkar kasafin kudi – Majalisar Wakilai tace idan ba ayi wasa ba Ministan ba zai samu kaso a kasafin kudin bana ba – Har yanzu dai ba a amince da kasafin wannan shekara ba
Hausaloaded.com na samun labari cewa Majalisar Wakilai tace idan ba ayi wasa ba Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ba zai samu kaso a kasafin kudin bana ba da ke hannun Majalisar a yanzu haka.
‘Yan Majalisar da ke jagorantar kwamitocin da ke karkashin ma’aikatar sufuri ta Amaechi sun ce bayanan da su ke samu akwai kunbiya-kunbiya a cikin sa.
Muhammad Bego daya daga cikin ‘Yan Majalisar ya bayyana haka sa’ilin da ya kai ziyara a ma’aikatar.
Honarabul Bego yake cewa ma’aikatar ba ta kashe kudin ta na bara ba wanda ya haura Naira Biliyan 200.
Majalisar tace hakan na sa a iya hana ma’aikatar wani kudi a wannan shekarar. Majalisar tace yayin da wasu ke neman kudi ita ma’aikatar ta gaza kashe na ta.
Kwanaki Amaechi ya bayyana wasu ayyuka da za a kammala wancan shekarar yake cewa don haka a jira sai nan da shekaru hudu sai a duba ayyukan da Gwamnatin Buhari tayi ba yanzu ba da ba a ko wuce shekaru biyu ba.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment