A karo na biyu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai halarci taron majalisar zartarwa da ake yi duk ranar Laraba ba, abin da ya kara jefa fargaba kan halin da yake ciki.
'Yan kasar da dama na ganin shugaban bai halarci taron ba ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wasu na nuna damuwa kan halin da yake ciki.
Sai dai ministan watsa labarai na kasar Lai Mohammed, ya ce shugaban na ci gaba da hutawa ne a gidansa.
Tun bayan da shugaban na Najeriya ya koma kasar daga jinyar da ya kwashe kusan kwana 50 yana yi a birnin London, ya ce ba zai rika yin aiki sosai ba saboda yanayin jikinsa.
Tun bayan da shugaban ya dawo kasar dai, ba kasafai yake bayyana a bainar jama'a ba.
Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al'amura.
Sai dai mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa babu wani abu da ya tsaya a harkar gwamnati saboda matakin da shugaban ya dauka.
"Ya fada da bakinsa cewa bai taba yin jinya wacce ta ba shi wahala kamar wacce ya yi a birnin London ba," kuma ya fada cewa zai ci gaba da huta wa, in ji Garba Shehu.
A lokacin jinyar da ya yi dai, sai da likitoci suka kara masa jini, ko da yake bai fadi larurar da ke damunsa ba.
A lokacin, shugaban na Najeriya ya ce yana samun sauki sosai, "amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti".
Shugaban dai yakan fito masallaci da ke fadarsa duk ranar Juma'a domin halartar salla.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment