MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE? - NewsHausa NewsHausa: MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE?

Pages

LATEST POSTS

Thursday 28 July 2016

MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE?

MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE ?

Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakaatuhu :
Miji ne ya je saduwa da matar sa sai ya kuskure ya saka mata a dubura shin mene ne hukuncinsa?

Amsa:
Wa alaikumus salam wa rahamatullahi wa barakaatuhu, In har da kuskure ya saka mata a dubura, sai ya yi maza ya zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin ba ne Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba.                                                                        A karshen suratul Bakara "Ya ubangijinmu kar ka ka kamamu in mun manta ko mun yi kuskure" Muslim ya rawaito hadisi cewa: Allah ya zartar da hakan.                                                                                                                                            Ibnu-majah ya rawaito hadisi, Annabi s.a.w. yana cewa: "Allah ya yafewa al'umata abin da suka aikata cikin kuskure".                                                                                                                        Cigaba da jin dadi a wurin bayan gano kuskuren, yana daga cikin zunubai.                                                     
Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

11 Shawwal, 1437 (16/07/2016).



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment