MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI? - NewsHausa NewsHausa: MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI?

Pages

LATEST POSTS

Thursday 28 July 2016

MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI?

MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI ?

Tanbaya :

Assalamun alaykum Warahmatullahi wabarakatuhu bayan sallama irin ta musulunci malam inayi maka fatan alheri Allah yasa kana cikin koshin lafiya.
Tanbayata malam ya halatta mace ta yi alkalanci a musulunci,
Allah yakarawa malam lafiya.

Amsa:

Wa alaikum assalam, a wajan mafi yawan malamai mace bai halatta ta yi alkalanci ba, saboda hadisin Abu-bakrata wanda Annabi s.aw. yake cewa: "Duk mutanen da suka jibintawa mace lamuransu ba za su rabauta ba" kamar Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4425.                                                                                                                         Alkalanci yana bukatar nutsuwa da daidaiton yanayi, wannan yasa Annabi s.a.w. ya hana wanda yake cikin fushi ya yi alkalanci, kamar yadda Muslum ya rawaito, mace kuma idan ta fara jinin haila takan fita daga daidaito, ta yi abin da bai dace ba, wannan yake nuna rashin dacewarta da wannan aiki na Annabawa da manzanni.                                           

Allah ne mafi sani.

13/07/2016

DR Jamilu Yusuf Zarewa



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment