Ko Kun San Mutumin Da Ke Son Raba Najeriya? - NewsHausa NewsHausa: Ko Kun San Mutumin Da Ke Son Raba Najeriya?

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 16 September 2017

Ko Kun San Mutumin Da Ke Son Raba Najeriya?

Daga shafin BBC HAUSA

A yanzu Nnamdi Kanu ya samu 'yancin walwala, bayan shafe sama da shekara daya da rabi a gidan kaso, kuma ba tare da an gurfanar da shi a kotu ba, inda ake zargin sa da cin amanar kasa da kokarin ballewa tare da kafa kasar Biafra. Dan gwagwarmayar ya ja hankalin dubban mutane a ciki da wajen Najeriya.
Wakiliyar BBC Stephanie Hegarty ta yi mana waiwaye don gano shin wa ye Nnamdi Kanu? Kuma me ya sa ya ja hankali da janyo ce-ce-ku-ce a kasar?

Nnamdi Kanu dai shi ne ya fara fafutikar kafa kasar Biafra, a shekarar 2014.

Yunkurin, wanda yawacin jihohin kudu maso gabashin Najeriya, wadanda kuma yawancinsu 'yan kabilar Ibo ne suka yi maraba da shi, an fara shi ne da nufin ballewa domin kafa kasa mai cin gashin kanta.

Shirin da Kanu ke jagoranta ba wai sabo ba ne; a iya cewa kokari ne na farfado da yunkurin da aka fara tun shekarar 1967 a lokacin da shugabannin kabilar suka ayyana yankinsu da kasar Biafra. Amma bayan yakin da aka dauki lokaci ana yi tare da zubar da jini da daruruwan mutane suka rasa rayukansu sai aka karya lagon shugabannin kabilar Ibo kuma dole suka ajiye makamansu.

Lamarin ya sake tasowa ne a lokacin da Mista Kanu ya sake farfado da tsohon burin kabilar da ya fito daga ciki wato Ibo, ya kuma ci gaba da gangamin tabbatar da burinsu.

Da fari ya fara gangamin ne yankin da al'umar Ibo suka fi rinjaye, amma daga baya a shekarar 2009 ya fara watsa shirye-shirye a sabon gidan rediyonsu na Biafra, tashar da take watsa shirye-shirye da kuma kira ga al'umar Ibo a duk inda suke a fadin Najeriya su fito don hada karfi da karfen kwatar 'yancin kai, kuma suna watsa shirye-shiryen ne daga birnin London.

Duk da cewa a Najeriya aka haife shi kuma ya fara karatu a yankin kudu maso gabashin kasar a Jami'ar Nsukka, Mista Kanu ya yi kaura daga kasarsa ta haihuwa zuwa Biritaniya.

Jim kadan bayan kafa kungiyar Ipob, sai ya kira wani gagarumin taro da ya hada al'umar Ibo, tare da shaida musu cewa lokaci ya yi da ya kamata su tashi don kwatar 'yanci da kafa tasu kasar ta Biafra.

Ya kuma bukaci su fito su yaki gwamnatin Najeriya da ke yunkurin hana su cimma manufarsu.

Ya kuma shaida wa magoya bayan sa cewa ''Muna bukatar daukar bindiga mu dura mata harsashi don karbo 'yancinmu.''

A wannan lokacin ne jami'an tsaron kasar suka farga da shi.
'Shaci-fadi'
Mai magana da yawun kungiyar Ipob Amarachi Chimeremeze ta shaida wa BBC cewa an yi wa kalaman Mista Kanu mummunar fahimta "Kalaman da ya yi amfani da su, abin da suke nufi shi ne za mu yi fafutuka dan karbar 'yancin mu," in ji ta.

Idan har za a fara sauraren karar da aka shigar kan Mista Kanu a watan Yuli mai zuwa, to alkalin kotun zai bukaci a fayyace abin da kalaman suke nufi.

A watan Oktobar shekarar 2015 aka cafke shi a wani otal da ke birnin Lagos, lokacin da ya kawo ziyara Najeriya.

An kuma tuhume shi da laifin ta'addanci, shiryawa kasa makarkashiya, da barazana, da kafa wata kungiya ba bi sa ka'ida, zarge-zargen da suke da alaka da cin amanar kasa.
Amma lauyan da ke kare shi Ifeanyi Ejiofor, ya shaida wa BBC cewa duk wadannan zarge-zarge shaci-fadi ne kawai.

"An yi hakan ne don a ci gaba da tsare shi a gidan kaso, wadannan zarge-zarge ne da babu abind a suke nufi face a kassara mutum ya daure shi har sai baba ta gani."

Yadda yankin Biafra yake:
A shekarar 1967 tsohon soja wato Odumegwu-Ojukwu ya ayyana kasar Biafra.

Ya kuma jagoranci yawancin sojoji 'yan kabilar Ibo a yakin da aka kwashe shekaru uku ana yi, da kuma ya zo karshe a shekarar 1970.

Fiye da mutane miliyan daya ne suka rasa rayukansu, yawancinsu saboda tsananin yunwa a lokacin.

Shekaru da dama, bayan juyin juya halin Biafra, wasu kungiyoyi sukai ta daukar hankalin matasa da nufin taimaka mu su cimma nasara.
Sun yi zargin cewa gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin ba ta damu da zuba jari a yankinsu ba.

Sai dai gwamnati ta ce, korafin na su ai ba wai akan kudu maso gabashin kasar su ke yi ba.

Tun bayan kama Mista Kanu, kungiyoyin da ke marawa Ipob suka dinga shirya zanga-zangar iri-iri dan nuna adawa da kama shugaban nasu.

Sun kuma yi amanna da cewa kamar yadda 'yan Biritaniya suka samu 'yancin kada kuri'ar ficewar kasar daga tarayyar turai, haka su ma suna da 'yancin ballewa daga Najeriya, abin da hukumomin kasar suka ki amincewa da shi.

Har wasu daga cikinsu na cewa su ma suna bukatar Biafra ta fice daga Najeriya.

Kusan a iya cewa a duk lokacin da kungiyar Ipob ta shirya zanga-zanga, sai jami'an tsaron Najeriya sun yi wa taron kafar ungulu , inda kungiyar ke ikirarin 'yan sanda sun jiwa magiya bayansu ciwo tare da hallaka wasu daga ciki , ya yin da su kuma jami'an tsaron ke musanta hakan.

Wani abu da ya janyo hankalin mutane game da kungiyar shi ne yawan tashe-tashen hankulan da sukan yi da jami'an tsaro a duk lokacin da suka shirya gangami. 

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa Cheta Nwanze da ya dade yana gudanar da bincike kan yunkurin samar da Biafra, ya ce kama mista Kanu da gwamnati ta yi babban kuskure ne saboda babu abin da mambobin kungiyar suka daina yi.

"A lokacin da aka fara zaben shekarar 2015 farin jinin kungiyar Ipob ya dan ragu musamman gidan rediyon da suke watsa shirye-shiryensu, kuma a wannan lokacin ne ya yanke shawarar zuwa Najeriya, kuma ba a jima ba jami'an tsaro suka kama shi,'' in ji Nwanze.

Mr Nwanze ya yi amanna da cewa, Mr Kanu ya yi nasarar fitowa a wani hoton bidiyo da aka nuna shi ya na magana a kan rashin goyon baya dan ta'addancin da kungiyar Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin Najeriya, an kuma gudanar da gangamin da ya na daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wurin, 'yan watanni kadan kafin kafa kungiyar Ipob, an kuma ambato shi ya na cewa akwai bukatar a yi kokarin ganin ba a raba Najeriya gida biyu ba.

Sai dai mai magana da yawun Ipob ta ce sam lamarin ba haka ya ke ba, hasali ma Mista Kanu ya je Najeriya ne don tabbatarwa magoya bayansa cewa suna nan kan bakansu na ballewa daga kasar.

"Ya zo ne don ya tabbatar musu duk abin da ya dade ya na fada da gaske yake yi. Sai ga shi hukumomin Najeriya kamar suna karantar shiga da ficensa kawai sai suka kama shi,'' in ji Misis Chimeremeze.

'Jikokin yahudawa' Duk da sanin halin mista Kanu na samar da kungiyar 'yan a ware, da burin samar da kasar da 'yan kabilar Ibo za su wataya a cikin ta, kungiyoyin kare hakkin bil'adam da manyan 'yan siyasa sun dade suna kira ga gwamnatin Najeriya ta sake shi, inda suka kara da cewa kamen da aka yi masa da tsare shi ba tare da an gurfanar da shi gaban shari'a ba ya sabawa ka'ida.

Kamar yadda aka saba gani a bangaren shari'ar kasar, ana dadewa kafin a gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifi hakan ce ta faru da Nnamdi Kanu.

Shekara daya da rabi da kama shi, amma babu alamar gwamnati za ta yi wani abin a zo a gani. A bangare guda kuma wasu kotunan kasar na ta kiran a bayar da belin wanda ake zargin, saboda dalilai na rashin lafiya da ya ke fama da ita. Sai a makon da ya gabata ne aka yi nasarar bayar da belinsa.

To sai dai kuma sharuddan da aka kafa kafin bada belin shi sun yi tsanani: Shugaban kungiyar ta Ipob dai an haramta masa gabatar da wani jawabi a bayyanar jam'a, ko tattaunawa da 'yan jarida , ko zama cikin mutanen da suka wuce 10.

Har wa yau kotu ta bukaci Mista Kanu ya gabatar wani fitaccen mutum na kabilar Ibo, da attajirin da ya mallaka gidan alfarma a birnin tarayya Abuja, da kuma wani babban malami bayahude, da tsabar kudi N100m ga kowannen mutanen da za su karbi belin nasa.

Shugaban kungiyar ta Ipob dai ya sha fadar cewa shi dan kabilar Ibo ne kuma bayahude, wadanda aka yi amanna da cewa jikokin yahudawan Isra'ila ne.

Da wuya ka tantance manufar yunkurin da Ipob ke yi da kuma shugabanninta.

Duk da cewa yawancin 'yan kabilar Ibo sun dawo daga rakiyar kokarin kafa kasar Biafra tun bayan yakin da ya hallaka da dama daga cikinsu a shekarar 1967, har yanzu zukatan wasu daga cikinsu na fatan ganin wata rana an cimma burin da aka fara lokaci mai tsaho da ya wuce.

Su na ganin cewa kamar an maida su saniyar ware a Najeriya, ba kuma ayi musu adalci.

Wasu da dama na ganin matakin da shugaba Muhammadu Buhari ke dauka dan taimaka musu bai taka kara ya karya ba. Hasalima ai yana daga cikin sojojin da suka karya lagon sojojin da suka yi yunkurin ballewa dan kafa kasarsu ta kashin kai a wancan lokacin.

Shi kuma mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo ya fara kokarin samun karin bayanin ainahin abinda ya faru a yakin Biafra.
Babu dai wanda zai bugi kirji ya fadi makomar Mista Kanu da 'yan kabilar Ibo.

Ana hasashen cewa ta yiwu kungiyar Ipob ta samu kanta kwatankwacin halin da kungiyar Mossab wadda ita ce ta fara yunkurin kafa kasar Biafra, inda a hankali ta dinga rasa magoya bayanta da masu fada a ji. Kungiyar ba ta kara yin tasiri ba tun bayan sako shugabanta da ya dade a tsare a shekarar 2005.

A wannan shekara ne za a cika shekaru 50 da yin yakin Biafra.
Kuma shi ya kawo shekaru 50 da kasa cimma manufar samar da kasar Biafra, wadda mutane irinsu Nnamdi Kanu ke gwagwarmayar tabbatar da ita



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment