Farare Da Kyawawan Mata Ake Sawa A Fim Yanzu inji Maryam A Baba (Sangandali) - NewsHausa NewsHausa: Farare Da Kyawawan Mata Ake Sawa A Fim Yanzu inji Maryam A Baba (Sangandali)

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 16 September 2017

Farare Da Kyawawan Mata Ake Sawa A Fim Yanzu inji Maryam A Baba (Sangandali)


Maryam A Baba wacce akafi sani da Maryam Sangandali na ɗaya daga cikin mawakan Hausa na zamani da tauraruwarsu ke haskawa a wannan karnin, itama ta halarci taron marubuta na duniya da aka gudanar cikin makon da ya gabata.

Sangandale tace ta zaɓi salon waka cikin ruwan sanyi ne wanda tace hakan ya fi gamsar da masu sauraro tare da nishaɗantar da masu sauraro.

Da aka tambayeta ko me ne dalilin da ako da yaushe akafi ganinta da Aminu Alan waka, sai ta amsa da cewar “ko shakka babu fahimta ce tazo ɗaya dashi, musamman idan aka dubi shima irin salon rera wakarsa kenan, kuma yana taimakamin wajen gyaramin wakokina tare da yimin gyara, wani lokaci ma ya rubuta min yace ga yadda wakar zata kasance. Wannan tasa ake ganin muna Kamanceceniya cikin wakokinmu”. Inji Sangandale

Sannan Maryam A Baba (Maryam Sangandale) ta bayyana cewar tun ina firamare nake sha’awar wakoki, saboda haka na kudurce a zuciyata cewar idan na gama makaranta nima zan bayar da tawa gudunmawar.

Haka kuma an tamabayi Sangandali shin me yasa bata fita a fina-finan Hausa?

Sai ta ce “gaskiya iyaka cina waka kawai, kasan su fim ana ɗaukar kyawawan mata kuma farare ne, to mu da muke haka sai mu tsaya iya wakar kawai.

Akarshe Maryam Sangandali ta bayyana gamsuwarta da wannan taro.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment