ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA !
Tambaya:
Assalamu alaikum. Allah ya kara MA Mallam Basira.
Malam tambaya ta akan jinin haila ne. Malam an ce alaman da ake gane karshen haila shi ne idan jinin ya canza kala zuwa ruwan kasa.
Na ga alaman hakan Se nayi wankan tsarki Bayan haka Se kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu Malam tsarkin nawa yayi? Yaya matsayin sallah da azumi? Nagode.
Amsa:
To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiqhu shi ne:
Ana gane daukewar jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:
1- Kekasar kasanki-Ta yadda mace za ta ga gabanta ya bushe ko kuma tsumma ko always din da ta tare jinin da shi.
2- Fitowar farin ruwa bayan daukar lokaci ana haila.
Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga daya daga cikin wadannan alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma ba za ki dauki hukuncin masu tsarki ba, don haka azuminki da sallarki ba su yi ba. Idan kika ga ruwa mai kama da kasa bayan daukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da kika samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu Addiya ya tabbatar da hakan.
Don neman karin bayani duba: Addma'uddabi'iyya shafi na: 14.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu zarewa. 10/7/2016
No comments:
Post a Comment