BA YA HALATTA AYI WASIYYA DA DUKIYAR MAGADA!!! - NewsHausa NewsHausa: BA YA HALATTA AYI WASIYYA DA DUKIYAR MAGADA!!!

Pages

LATEST POSTS

Thursday 28 July 2016

BA YA HALATTA AYI WASIYYA DA DUKIYAR MAGADA!!!

BA YA HALATTA AYI WASIYYA DA DUKIYAR MAGADA ! ! !

Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullah Dr. Dan Allah zan iya yin wasiyya ga kanina  ya hakura da gadona dan mata ta tayi amfani da shi, Domin na san kanin ba zai kula da Matar tawa ba Idan na mutu?.

Amsa:

Wa alaikum assalam, wanda za'a gada ba shi da ikon hana magajinsa gado.                                                                        
Allah madaukakin sarki shi ne ya dauki nauyin raba gado ga wadanda suka can canta da kansa,ya kuma yi alkawarin narkon wuta ga dukkan wanda ya sabawa dokokin da ya sa na rabon gado a aya ta: 14 a suratun Nisa'i.                                                     
Mutukar kaninsa yana cikin magada ba shi da ikon hana shi, ko da ya yi wasiyya, ya wajaba alkali ya bata ta.                 

Dukiya tana zama mallakin magada daga zaran an tabbatar da mutuwar mamaci.                               
Idan har kanin naka ya sarayar da hakkinsa da kansa, to babu laifi tun da damarsa ce.

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr jamilu Zarewa.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment