IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44,IDDARTA TA CIKA? - NewsHausa NewsHausa: IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44,IDDARTA TA CIKA?

Pages

LATEST POSTS

Thursday 28 July 2016

IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44,IDDARTA TA CIKA?

IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44, IDDARTA TA CIKA ?:

Tambaya:

السلام عليكم ورحمة الله
Malalm don Allah a taimakamin da amsar wannan tambayar:

Mace ce mijinta ya rasu ya barta da ciki wata daya, bayan sati 2 da rasuwarshi sai cikin yazube to anan ya iddarta take?

1. iddar ta kare?

2. ko zata kirga wata 4 da kwana 10?

in kuma kirgar zat ai daga yaushe zata fara, ranar rasuwarshi ko ranar da cikin ya zube?
na gode.

Amsa:

Wa alaikum assalam,

Mutukar cikin na ta bai wuce kwana : 44 ba, ba za ta kammala iddar takaba da yin barinsa ba, tun da halittar mutum ba ta fara bayyana ga dan-tayin ba.                                                 
Mafi karancin lokacin da halittar mutum take fara bayyana yana farawa ne daga kwana: 80 zuwa 90.                                                                             
Idan haka ta faru da ita za ta yi idda da wata hudu da kwana goma.                                                            
Allah ne mafi sani.d
Dr Jamilu Zarewa.                                                         20/7/2016



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment