MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA - NewsHausa NewsHausa: MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Pages

LATEST POSTS

Monday 28 November 2016

MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !

 

 

Tambaya :
Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai na ji mijina ya danne ni, na yi ta kokarin na kwace amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna azumi, don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanyawa zuriyarka albarka

 

 

Amsa :
To 'yar'uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to babu kaffara akan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah




amma shi kuwa ya sabawa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadhana, 

 

kuma dole ya yi kaffara, ta hanyar 'yanta kuyanga, in bai samu ba, sai ya yi azumin sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin, kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta : 616.

 

 

Allah ne mafi sani.

     Amsawa

Dr jamilu zarewa



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment