HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI Tambaya : Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai . Amsa : To dan'uwa Allah ya ba mu dacewa gaba daya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki, saidai sun kasu kashi uku : 1. Akwai wadanda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta" , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a hadu da wadanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu'u 3\306 . 2. Akwai wadanda suka ta tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma'ad 1\527 3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja'afar dan Abu-dalib Annabi s.a.w. ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa : ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi s.a.w ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri" Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299. Wadannan malaman suna cewa : Za'a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu : A. Fadin nana A'isha cewa : ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa : yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi. B. Kasancewar bai hana matan Ja'afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su. Wannan magaanar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya,, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303 Prof. Khalid Al-mushakih (daya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, saidai za'a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman : 1. Yawaita yin abinci, da masu karbar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa. 2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi'o'in da ba su da hujja. 3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata. Duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 75 Allah ne mafi sani.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment