BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA
Tambaya :
Don Allah ina da tambaya: wai ma ye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya saida akan nera 8 ? Amsa : To malama riba ta kasu kashi biyu :
1. Akwae ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu. Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.
Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so idan mutum yana siyar da kaya ya saukaka, Annabi s.aw.
yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame", kamar yadda ya zo a hadisin Bhukari mai lamba ta : 2076
Allah shi ne mafi sani
Amsawa
Dr jamilu zarewa
posting by Abubakar Rabiu Yari
Copy the link below and Share with your Friends:
This comment has been removed by a blog administrator.
ReplyDelete