Sababbin hotunan rahama sadau a yanxu haka cikin university wanda a yanxu haka take chilling a jami'a ga abinda tace: "Günaydin 💫 @ayeesha_sadau @teejayys_collections 💛 @ Eastern Mediterranean University". Ga hotunan kamar haka
Tsohuwar fitacciyar jarumar shirin fina finan Kannywood, Rukayya Dawayya ta bayyana matsalolin data fuskanta a rayuwar aure da suka yi sanadin mutuwar auren nata da tsohon mijinta.
Dawayya ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da jaridar Blue Print, inda tace tayi danasanin auren tsohon mijinta Adamu Teku, saboda bata yi cikakken bincike ba game da shi. Auren Dawayya ya mutu ne kimanin shekaru hudu bayan auren, a lokacin da ta kai ma mahaifiyarta ziyara bayan dawowarta Najeriya daga kasar Saudiyya, duk kuwa da sadaukarwar da ta dinga yi don ganin auren ya zauna lafiya. “Allah na gani na yi iya bakin kokarina don ganin aurena ya zauna lafiya, amma hakan bai yiwu ba, saboda mijina auri saki ne, kafin ni ma ya saki mata sama da 15, don haka ba kai na farau ba. Yarona Arafat ne na 11 a cikin yayansa.
“Banda matan da ya saka kafin su haihu a gidansa, Uwargidarsa ta bayyana min cewar kafin ita ma ya auri mata guda 6, itace ta 7 a yanzu. Kuma gaskiya ban yi bincike game da shi ba a sosao kafin aurenmu, iyakar binciken da nayi shine a Abuja, amm banke kauyensu ba a jihar Adamawa.
“Don har babbar yarsa sai da bayyana min dukkanin halayyarsa, har ma a kauyensu ana cin mutuncin yayansa da sunan wai mahaifinsu baya iya rike matan aure, wanda hakan ya sanya yayan nasa basa iya cudanya da jama’an kauyen.” Inji ta.
Bugu da kari da aka tambayeta game tsawon lokacin da suka yi suna soyayya kafin aure, sai Dawayya tace gaskiya watanni biyu suka yi kacal suna soyayya, sakamakon a wannan lokacin aure kawai take son yi ruwa a jallo, don haka ta rungumeshi ba tare da bata lokaci ba, har suka yi aure.
Daga karshe Dawayya tace tun bayan da ta samu juna biyu ne Adamu ya fara nuna mata fushinsa, saboda wai shi baya son haihuwa, don haka ya gindaya mata munanan sharudda, amma ta cije, har sai ranar da ta kai ma mahaifiyarta ziyara, inda ya aiko mata da sakon saki ta wayar hannu.
Mai alfarma sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar na uku ya yi kira ga sauran Musulmi su rika nuna halayen kwarai a rayuwar su, wanda hakan zai sanya al'umma amincewa da su, kuma ya jawo hankalin wadanda ba Musulmi ba ga kyakkyawar tarbiyya da addinin Musulunci ke koyarwa.
Wannan na daga cikin sakon da Sarkin Musulmin ya aika wajen mika gudunmawar al'ummar Musulmi ga Malam Bashir Usman Idris mutumin da ya tsinci wasu makudan kudade har naira dubu 582 da dari 450 a cikin Keke Napep din da yake aikin haya da shi a Jos, wanda kuma ya mayar da kudaden ga matar da ta manta da kudade, Maman Ijima wacce 'yar kabilar Igbo ce dake harkar kasuwanci a kasuwar dare.
Da yake gabatar da sakon ga wannan bawan Allah, mai martaba Sarkin Wase wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jama'atu Nasril Islam, Dr Muhammad Sambo Haruna, ya bayyana cewa an ba da wannan gudunmawa ne domin karfafawa Malam Bashir da sauran Musulmi gwiwa ga ayyukan alheri.
Ya ce, mai alfarma sarkin Musulmi da wasu mutane tara su ne suka hada kudi kimanin naira miliyan daya da dubu dari daya, don agazawa rayuwar sa, sakamakon halin kuncin rayuwa da yake fuskanta shi da iyalinsa.
Sakataren watsa labarai na kungiyar Jama'atu Nasril Islam a jihar Filato Alhaji Sani Mudi ya sanar da cewa, an yi amfani da kudaden wajen saya masa sabon Keke Napep da kudin sa ya haura naira dubu dari 6, da kuma firji na sayar da kayan sanyi da injin din markade, wanda aka bai wa matar Malam Bashir, Malama Hajara Dauda, saboda kokarin ta na karfafa masa gwiwa don ya mayar da kudaden.
Sannan an ba shi naira dubu 120 don biyan kudin makarantar yaransa da kudin hayar da ake bin sa bashi.
Bayan an mika masa sabon Keke Napep din dakamatsaya masa an kuma ba shi naira dubu 50 wacce zai yi amfani da ita wajen sayen lamba da yin rijista. Ita ma kuma matar sa an bata naira dubu 20 don ta ja jari a sana'ar da za ta yi.
Malam Bashir Usman wanda ya karbi kayan cikin hawaye, ya yi godiya ga mai alfarma sarkin Musulmi da daukacin wadanda suka taimaka masa, tare da kira ga abokan aikinsa da sauran Musulmi su zama masu halaye na kwarai, kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
Halima Mamman Shata tace ta gaji mahaifin ta a bangaren siyasa kuma zata fito takara domin wakiltar yankin Funtua a majalisar dokoki na jihar Katsina a zabe mai gabatowa
Daya daga cikin yaran marigayi Alhaji Mamman Shata, fitaccen mawaki kuma wanda ya raya kasar hausa da wakoki wato Hajiya Halima Mamman Shata ta bayyana anniyarta na fitowa takarar majalisar dokoki na jihar Katsina. Hirar ta da jaridar RARIYA Hajiya Halima tana mai cewa ta gaji mahaifin ta a bangaren siyasa don haka zata daukaka wanan gado na fitowa takara domin wakiltar yankin Funtua a zaben 2019 dake nan tafe.
Ta bada dalilan daya sa zata fito takara kamar haka; "Na fito domin in bada guddumuwa ga cigaba karamar Hukumar Funtua da kawo kudurorin da za su kawo cigaban Matan da inganta rayuwar su a jihar Katsina da kasa baki daya. "Mata suna da rawar da za su taka, a harkar siyasa amma mun yi barci an bar mu a baya musamman a arewacin Nijeriya, kalilan ne ke fitowa takara, saboda wadansu dalilai. Kuma mu mata mune muka fi fitowa a ranar zabe, kuma kullum mune ake bari a baya. Idan Allah ya bani nasara zan tabbatar da an yi dokoki da za ta inganta rayuwar matan jihar Katsina da kuma karfafa rayuwar su". Halima Shata ta kara da cewa "koda yaushe ina kara samun kwarin gwiwa a harkar siyasa saboda mahaifinmu dan siyasa ne, Amma ni na taso naga yana harkokin siyasa wadda har ya taba zama shugaban jam'iyyar da kuma takarar shugabanci kasar nan kuma cikin yayansa ina alfahari da na gaje shi bangaren siyasa, kuma zan cigaba da jajircewa domin ita ce matakin nasara.
Daga karshen yar gidan shaharen mawakin tayi ma Gwamna Aminu Bello Masari godiya bisa kokarin yake na bude kofofi ga mata don fitowa a dama dasu a harkar siyasa.
A daren shekaran jiya ne wani mummunan al’amari ya afku a garin Birnin Gwari, inda aka yi garkuwa da Amarya da wasu mutum 10. Amaryar wacce aka dauke ta domin a kai ta dakin mijinta, sun gamu da azal ne bayan da ‘yan bindiga suka tare su, sannan suka yi garkuwa da dukkanin ‘yan tawagar kai amaryar. Wannan danyen lamarin ya auku ne da misalin karfe 8:00 na dare, wanda ya jefa al’ummar yankin cikin taraddadi da rashin tabbas. Yayin da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, wani tsohon Shugaban karamar hukuma wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce, masu garkuwar sun jima su na cin karensu ba babbaka a yankin domin ba wanda ya isa ya tunkare su. A cewar sa, masu garkuwar sun dakatar da motar wacce ke dauke da Amaryar, inda suka yi awon gaba da ita da kuma ‘yan rakiyar ta su goma. Ya ce, lamarin ya auku a tsakanin kilomita 55 daga garin na Birnin Gwari. Sai dai rahotanni sun ce, uku daga cikin wadanda aka yi garkuwar dasu sun samu damar arcewa, inda suka dawo garin a jiya da safe. Hanyar ta Birnin Gwari da ake bi zuwa karamar hukumar Funtuwa ta jima da zama tarko ga matafiya wadanda ke bin hanyar sakamakon ta’asar da masu garkuwar suka jima suna tabkawa. A wata sabuwa kuma, a ranar juma’ar da ta gabata masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wani matashi a lokacin da yake tafiya akan Babur dinsa daura da kauyen Uduwa a cikin garin na Birnin Gwari. Har ila yau, masu garkuwa da mutane, sun yi yi garkuwa da dan Mataimakin Liman na Masallacin kauyen Uduwa, inda suka nemi a basu kudin fansa har naira miliyan uku. Wani shugaban ‘yan sintiri dake kauyen mai suna Hussaini Iduwa ya tabbatar da aukuwar lamarin, a hirar da aka yi dashi. Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, Aliyu Muktar ya bayyana cewar labarin bai riski rundunar ba.
GASA! GASA!! GASA!!! A cigaba da haska fim din #TAQADDAMA dake wakana yanzu haka a film House dake cikin choprite, kamfanin ATC General Merchant Ltd dake kasuwar kantin kwari sun dauki nauyin bayar da kyauta. Wanda akwai leshina da kuma tiket ga duk wanda ya iya amsa tambayoyin da za su biyo baya kamar haka.
1. Fadi sunayen fina finan da Alhaji sheshe ya shirya ,Ali nuhu ne a ciki,kuma Alee Gumzak ne ya bayar da umarni.
2. Fadi sunayen fina finai guda Hudu wanda Ali Nuhu da Aminu Momo suka yi tare.
3- Fadi sunayen fina finai guda goma wanda Abubakar mai shadda ya shirya kuma Ali nuhu ne a ciki.
Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa Adam A. Zango ya kori yaransa baki daya, inda ya bayyana cewa daga yanzu ba shi ba su. Rahotannin sun kara da cewa baya ga hadiman nasa da Adamu Usher ya sallama har da wasu daga cikin abokansa. Majiyar ta kara da cewa daga cikin dalilan da ya sa Adam Zango yanke wannan hukuncin shine sau da yawa yaran nasa na ji kuma suna gani ana ci masa mutunci amma ba za su iya kare masa hakkin sa ba, inda a wasu lokutan ma da su ake haduwa a bata masa suna, duk da cewa yana biya musu bukatunsu daidai gwargwado.