Bayan da tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi taji labarin wannan yaron dan shekaru tara da haihuwa dake aikin karfi dan ciyar da mahaifiyarshi da kuma kannenshi biyu, ta bayyan cewa tana son ta taimaka mishi.
Wata baiwar Allahce ta saka hoton yaron a dandalinta na sada zumunta na Twitter inda tace sunan Yaro Isma'il kuma shekarunshi tara, tun yana dan shekaru shidda da haihuwa mahaifinshi ya rasu wannan yasa yanzu yake aikin karfi dan ciyar da mahaifiyarshi da kuma kannenshi guda biyu.
Da Nafisa ta ga wannan labari sai ta bayyana cewa duk me labari akan yanda za'a samu wannan yaro ya aikamata da cikakken bayani ta sakon sirri dan kuwa tana so ta taimakeshi.
Muna fatan Allah ya sa a dace ita kuma Nafisa ya saka mata da Alheri.
Kalli wani bature na murnar nasarar da Najeriya ta samu
Wannan wani baturene sanye da rigar Super Eagles yake murnar nasarar da suka samu akan kasar Iceland a gasar cin kofin Duniya da ake yi a kasar Rasha, kwallaye biyu Najeriyar taci Iceland ta hannun Ahmad Musa.
Abun al’ajabi: Wata mata ta haifi ’ya’ya 17 a sa’o’i 29
Wata mutuniyar kasar Amurka Catherine Bridges ta kafa tarihi inda ta haifi yara 17 cikin awanni 29 a asibitin Indianapolis Memorial da ke Amurka.
Dakta Jack Morrow likitan da ya karbi haihuwar matar ya ce, a lokacin da Catherine Bridges ta fara haihuwa jariran na ta fitowa daya bayan daya.
Likitan ya bayyana haihuwar tata a matsayin abin tsoro inda yace yaa dade banga irin wannan haihuwar ba a duniya.
Catherine Bridges da Maigidanta sun dade tare amma ba su samu haihuwa ba, a shekarar da ta gabata ne dai suka ziyarci wani asibiti a garin Rhodes Island don ba su shawarwari a kan yadda za su iya samun karuwa.
An samu nasara a kan shawarwarin da Likitocin asibitin suka ba ma’auratan inda suka samu ’ya’ya maza 17 a jere masu kama da juna.
An dai rada wa jariran suna masu kama da juna wadanda suka hada da: James da Jacob da Jarod da Jarbis da Jason da Jeffrey da Jeremy da Jerome da Jesse da Jimmy da Joachim da Jonathan da Jonas da Joseph da Julian da Jimbo da kuma Darth.
KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE
A tafsirin Al-Qur'ani Maigirma wanda Babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yake gabatarwa a darasin jiya Talata 20 ga watan Ramadan, wani bawan Allah ya rubuto takarda yake rokon Malam akan ya yiwa 'dan uwansa nasiha sakamakon bijirewa mahaifiyarsa da yayi har yace babu shi babu ita, kuma sunyi iya kokarin da zasuyi domin yaje ya baiwa mahaifiyarsa hakuri amma yaki Da malam ya tashi gabatar masa da nasiha sai ya fara da cewa ashe har ana iya yin fada da iyaye a kaurace musu?
Babbar magana!, bil hakki ni dai tun da muka shiga Ramadan ban taba jin wata fitina da ta kai wannan girma ba ace mutum da iyayensa yayi fada har an rokeshi don ya basu hakuri amma yaki Daga nan Malam ya kawo bayanan ayoyin Qur'ani da Hadisai na Annabi (saw) wanda suke nuni da falalar yiwa iyaye biyayya musamman mahaifiya, sannan ya kawo wata kissa wacce daga karshe sai da Malam ya fashe da kuka Kissar itace kamar haka:
A zamanin sahabbai wani mutum ne yana neman budurwa sai ya kasheta saboda taki aurensa, sai yazo wajen Ibnu Abbas (ra) sai yace masa nayi zunubi maigirma, ban san me zanyi Allah ya gafarta min ba, ban san me zanyi ba a rayuwata na shiga damuwa Sai Ibnu Abbas ya tambayeshi mai ya faru gareka? Sai yace wallahi budurwa nake nema taki aure na sai na kashe ta, Ibnu Abbas yace Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ka aikata? yace eh!, yanzu don Allah yaya za'ayi Allah Ya yafe min? Tambayar farko da Ibnu Abbas ya masa shine shin mahaifiyarka tana raye? sai mutumin yace masa a'a bata raye, sai Ibnu Abbas yayi shiru, bayan tsawon lokaci sai yace to kaje kayi ta tuba kayi ayyukan alheri.
Sai daliban Ibnu Abbas sukace masa me yasa ka tambayeshi ko mahaifiyarsa na raye kuma da yace bata raye sai kayi shiru? Sai Ibnu Abbas yace Wallahi ban san wani aiki na nagarta da mutum zaiyi ya nemi gafarar Allah Ya yafe masa ba kamar BIYAYYA ZUWA GA MAHAIFIYA, yace ban san wani aikin dake kaffara na zunnubai a duniya ba kamar biyayyan da mutum yake yiwa Mahaifiyarsa.." daga nan wajen ne sai Malam Isah Ali Pantami ya fashe da kuka har ma ya kasa cigaba da bayanin kawai sai ya umarci Alarammansa Malam Abdullahi Abba Zaria ya karanto ayoyin Qur'ani.
Ni kuma nace Malam Ya tuna da tashi mahaifiyar wacce Allah Yayiwa rasuwa watannin baya shi yasa yake kuka, ga wani kuma tashi mahaifiyar tana raye amma yayi fushi da ita (Allah Ya sauwake) Wanda yake da bukatar karatun ya nemi tafsirin Qur'ani na ranar 20 ga watan Ramadan wanda ya gabata jiya talata Gaskiya duk wanda Mahaifiyarshi take raye ashe yana da wata babban alfarma wanda zai iya gyara lahirarsa da ita.
Mu kyautatawa iyayenmu da suke raye domin mu gama da duniya lafiya mu kuma hadu da Allah lafiya Allah Ka shiryar damu ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu, wadanda suka rasa nasu iyayen Allah Ka jikansu Ka basu Aljannah don RahamarKa Amin Sarauniya.
Wani mutum da ba a tantance ba ya fado daga saman kololuwar Masallacin Ka'aba a Makkah a daidai lokacin da mutane ke dawafi.
Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ambato 'yan sandan kasar na cewa nan take mutumin ya mutu bayan fadowarsa. Sai dai ba a bayyana abin da ya yi dalilin fadowarsa ba daga kololuwar saman masallacin na Haram a Makkah ba.
"An tafi da gawarsa zuwa asibiti, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalinsa da kuma abin da ya haddasa fadowarsa daga sama duk da an kewaye saman da waya" kamar yadda SPA ya ruwaito.
Kamfanin dillacin labaran Saudiyar kuma ya ce ana tunanin mutumin ya kashe kansa ne domin ba wannan ne karon farko ba da hakan ta faru a Masallacin na Ka'aba, yayin da Addinin Islama ya haramta kisan kai.
Al'amarin ya faru yayin da musulmi ke azumin Ramadan, a lokacin da kuma dubban al'ummar musulmi ke gudanar da Ibadah a Masallacin mai tsarki a Makkah. A bara wani ya yi kokarin cinna wa kansa wuta a gaban Ka'aba, kafin jami'an tsaro suka hana shi. BBCHausa.
Wakar da mata ke rawa sanye da hijabi ta jawo cece-kuce
Wata waka da wani mawakin Najeriya me suna Falz yayi na kara daukar hankulan mutane sosai, saboda irin sa'insar da ake samu tsakanin mawakin da kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya me suna MURIC, mawakin dai ya saka mata sanye da hijabi suka yi wata rawar zamani da ake kira da shaku-shaku wanda kungiyar MURIC tace hakan badalane be kamata yayi amfani da hijabiba.
Haka nan MURIC ta zargi mawakin da batawa addinin musulunci suna da sanya kiyayyarshi a zukatana mutane, inda suka bada misali da wani da aka nuna a bidiyon wakar sanye da kayan fulani da yaje yana kashe wani mutum, MURIC tace wannan bata sunane, me yasa mawakin be nuna yanda suma fulanin ake kashe su ba da shanunsu musamman a yankin jihar Benue.
A karshe dai MURIC ta baiwa mawakin kwanaki bakwai daya janye wannan waka daga kasuwa ko kuma su kaishi kotu. A martaninshi, Falz yace da gangan ya saka mata sanye da Hijabi sun rawar ta Shaku-shaku sannan kuma hakan yana nuna irin 'yan matan Najeriya da Boko Haram suka sace ne.
Ya kuma kara da cewa irin ci mishi tuwo a kwarya da lamuran Najeriya ke yi ne yasa ya shirya wannan bidiyo. A wani yanayi na goyon bayan mawakin, masu yiwa mawakin tsare-tsare sun fitar da sanarwar cewa ba zasu janye wakar ba idan MURIC ta damu ta kaisu kotu.