NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Sunday, 18 February 2018

Ba Zamu Yarda A Mai Da Nijeriya Kasar Izala Ba __Cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi


Jiya Juma’a 16/2/2018, babban shehin malamin darikar Tijjaniyyah a tarayyar Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga shugaban kasan Nijeriya da Antoni Janar na kasa da duk wanda abin ya shafa da ba zasu yarda a haramta masa wannan “freedom of religion” da tsarin mulki ya basu ba ta hanyar hana ‘yan tijjaniyyah yin wazifa da karatun salatul fatih da taron Maulidi a makarantun gwamnati ba.

Shehin malamin yana cewa:
 “A kawo mana dokar Nijeriya wadda ta hana wazifa a Nijeriya, wadda ta hana yin karatun Salatul Fatih a Nijeriya, a kawo mana mu ga numba ta nawa ce, ta wacce shekara ce. Kawai don muna da kunya, muna da mutumci muna yin shiru! Sai a mai da kasar kasar IZALA? Wallahi ba zamu yarda ba.” 
Malamin yayi ishara ga gwamnati da ta lura sosai ka da ‘yan a bata su bata ma ta gwamnati ta hanyar jefa ta cikin rikimar da ba zasu iya mata maganinta ba. Yana cewa;
 “ …Ga rigimar makiyaya da manoma, yanzu kuma ‘yan tijjaniyyah a hana masu ‘yancin addini a makarantu bayan an rubuta “freedom of religion”, LAKUM DINIKUM WA LIYAD DIN. Lallai muna jan kunnen wa’yanda abin ya shafa.”

Malamin ya cigaba da cewa:
 “ Wacce doka ce aka kawo sabuwa ban da “freedom of religion”? Mu bama son tashin hankali, bama goyon bayan tashin hankali amma in an kore mutum ya rasa yanda zai yi, to, dole zai dauki doka a hannunsa. Allah Ya kiyaye, Allah Ya kiyaye.”

Shehin malamin ya kara da yake cewa su basu yarda wannan gwamnatin IZALA ce ba :
 “ Su ‘yan izala suna cewa wannan gwamnatin gwamnatin IZALA ce, bamu yarda ba, gwamnatin Nijeriya ce. Amma ana so a tabbatar ma mutane wannan gwamnatin gwamnatin IZALA ce. Ta soma hana wazifa, ta soma hana salatul fatih, ba zamu yarda ba wallahi. Ko gwamnatin soja tayi mana haka ba zamu yarda ba. Ai ba gwamnati sai da mutane, kuma mutane Alhamdulillahi muna da mutane wanda duniya take kallo da mutumci da addini da ilimi. A cikinmu ne fa akwai Sheikh Sharif Ibrahim Sale wanda shi abin nunawa ne a cikin dukkan duniya gabaki daya bare Nijeriya. Bayan sanin Alkur’ani da sanin hadisi da sanin riwaya da sanin ilimin addini shi Sharifi ne a wajen baba, Sharifi ne ta wajen mamanshi…..”

Shehi ya gargadi gwamnati yana cewa:
 “..Lallai gwamnati da duba wannan, saboda hakurinmu ya kare. Cin mutumcin da ake ma mutanen mu a makarantu a hana su wazifa, a hana su karatun salatul fatih, alhali kuwa dukkan makarantun na gwamnati ne, ban a IZALA bane.”
 “ Abin da aka dauko na cewa wannan gwamnatin IZALA ce, ta hana wazifa, ta hana karatun salatul fatih a bincika daga ina wannan hukunci ya fito. Ba zamu yarda ba wallahi.”
A karshe shehim malamin yayi wa kasar Nijeriya addu’a

Saturday, 17 February 2018

Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Khudubar Ranar Juma'a

Mai taken Sulhu Alheri ne.

Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

 Daga Masallacin Juma'a na Dorayi Kano

22/5/1439 = 9/2/2018


Download Audio Here

Source Darulfatawa.com

Kalli hotunan Abinda Muhammad tare da mijinta Mustapha Abubakar

Tsohuwar jarumar masana'antar kannywood kenan abida muhammad tare da mijinta mustapha Abubakar Allah ya bada zaman lafiya.




Duniya Makaranta: Hotunan Wata kyakkyawar Macen Soja Ta Shirya Auren kanta Da kanta A Kasar America


Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama

 Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika

Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama da ba mahalukin da ya taba kai karshen su har ya koma ga mahaliccin sa. Haka nan kuma abubuwan mamaki a kullum faruwa suke ta yi.




Yau ma kuma gamu dauke da wani labarin ban al'ajabi, mamaki da kuma takaici ma a wajen wasu inda muka samu cewa wata kyakkyawar macen soja ta sha alwashin auren kan ta da kan ta.

Ita dai wannan macen mai suna Shaunice Safford tana kuma da adreshin dandalin sada zumunta na Instagram ne (@drsafford) inda ta kudruri aniyar cigaba da wanzar da rayuwar ta tare da ita kanta din bayan auren da ta yi.



A cewar ta, Macen sojan Shaunice Safford ta bayyana cewa ba tun yanzu ba ta dade tana muradin ranar da zata yi aure ta zauna cikin kwanciyar hankali da lumana amma hakan bai samu ba sai a ranar 14 ga wannan watan da muke ciki.

Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika kuma rayuwar ta ta kammala cika da farin ciki da jin dadi, hade da walwala.

VIDEO : huzzynewlh - warning freestyle


The best artist of the year congratulations for your award. The singer release the warning freestyle  video by Huzzynewlh.


Download video here

ALBUM : Basakkwace New Album 2018

Your welcome to hausalaoded blog today iam coming you with another artist from sok city with  new latest song's 2018 by "Basakkwacen". Release new brand 7 tracks 2018.He is good brilliant rapper 

One of the hit Music "Story about me and  and my music game":-

Story about me and my music game us a story that touched.. Tony's pain.. Sleepless nights with a pad and a pen..going up and down in search of fame..stress in my brain.. Dirt in my name.. 
Am tired of this living am looking for a change.. I just a different day but the shit is the same.. Baka gama ganiba idan dai da ranka..wani saiyaci mutuncinka gabanka..xaya tsokaneka nigga dandai ka tanka..

All he ever wanna see is bacin ranka..Duniya makaranta..Duniya kullun da sabunta..Duniya tanata rudinka...

Duniya kanasonta xaka barta..yoh.. Lord am down on my knees.. Ka taimakemu me and my Gz...munata nema ka bamu cheese.. When the death come mu kwanta in peace.. 
Tell me what you see  when you looking at me nigga..albarka da yawa idan dai ka qirga..Ba wani malan mamana na riqa..hamsal salawati ibadun duk nacika.

Those are the following 7 tracks list

1. 100 Percent-basakkwacen Ft Zuru Boy

Download music here


2. basakkwace-16 bars   


Download music here


3. basakkwacen-fura juice  




Download music here



4. basakkwacen-story about me & music   



Download music here



5. huzzynewlh ft basakkwacen-parkwell   




Download music here



6. BMG Ft Yasir Tunchi- Buga Lokaci- pro by Bz sound   



Download music here



7. uncle-K of yanfu yanfu-international   



Download music here

Friday, 16 February 2018

Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid

Dan wasan gaba na Kungiyar Tottenham Harry Kane ya
cimma yarjejeniya da Real Madrid kan sauya sheka zuwa
gareta idan aka bude kasuwar ‘yan wasa ta gaba.

Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Spain 'Don
Balon' ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa
Real Madrid hannu kan yarjejeniyar murza mata leda tsawon
shekaru 5.

Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan
Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin
Madrid din da kuma Tottenham kan farashin Harry Kane.

An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya
sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta
dada haskawa a fagen zura kwallaye.