Wannan hoton sune sababbin hotunan jaruma amina amal wanda wannnan jaruma yar asalin kasar kamaru ne wanda tazo Nigeria sanadiyar shahararren dan fim mai suna adam a zango wanda wannan hotuna sun samu comments da likes sosai daga masoyanta.
Wannan hotuna sune da jarumar tayi posting a shafinta na instagram.
Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta bada wa'adin kwanaki uku domin soma rushe gidajen badala dake yankin Galadima da sauran wuraren badala dake kewaye da garin Maiduguri.
Wani kwamiti mai karfa da aka kafa kan lamarin karkashin jagorancin kwamishinan shari'a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan tare da goyon bayan ma'aikatar filaye na jihar, sun baiwa gidajen karuwan da na mashayan ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga watan Yuni da su tattara su bar yankunan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
Za a rushe wuraren ne bisa dalilai na rashin mallakar filayen ba bisa ka'ida ba ko kuma yin gini bisa muhallan da ba su dace ba. Ko kuma yin ginin ba tare da mallakar takardu ba.
Wasu daga cikin otal din dake yankin Galadima a Maiduguri sun hada da;
* New Travels Hotel. * Gondola Hotel. * paragon Hotel. * Chinners Hotel. * Pampas Hotel. * Favour land Hotel. * Blue Sport Hotel. * Sea Never Dry Hotel. * Rall View Hotel. * Okonna Hotel. * Easy Guest in Hotel. * Peace Hotel. * Chicago Hotel. * Chrbos hotel. * Benue Hotel. * New Travelers 2 Hotel. * Moonlight Hotel. * Chobados hotel. * Chiners 2 Hotel. * Wazobia Hotel.
Otal din dake kan titin Baga a yankin Maiduguri sune kamar haka;
* Barka Da zuwa 1 Hotel. * Barka Da zuwa 2 Hotel. * Loyal City Hotel. * Make we Flex Hotel. * Favour land Hotel. * Maintenance Hotel.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa babu wani daga kafa ko nuna idon sani a yayin da wa'adin kwanaki ukun suka cika.
Rahama Sadau Ta Bada labarin Yadda Ta Rasa Budurcin Ta
Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta - Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin fira da majiyar mu a satin da ya gabata - Ta ce an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama ne
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Rahma Sadau ta yi karin haske game da yadda ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba bada labarin cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba a watannin baya.Jarumar dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take yin fira da majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata karon farko tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda taje karatu.
Jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba wai tana nufin ta taba zina ba ne domin ita hasali ma ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.
Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.
Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har Naira Milyan Dari JARIDAR DIMOKURADIYYA Anyi cirko-cirko a Ofishin kungiyar mawaka tun bayan bullar rahoton mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi kwana da makuden kudade sama da nera milyan Dari.
Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna Aliyu Ningi dake jihar Bauchi shiya bayyanawa manema labaru, yace Gwamnan Jihar Zamfara shiya basu kudin bayan sun bukacin hakan kan irin gudun mawar da suka bayar a gabanin zabukan 2015 gashi kuma sun shirya bayar da gagarumar gudun mawa a zabukan 2019 dake
tafeTunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya basu nera milyan goma sha takwas inji Haruna Ningi.
Ya kara da cewar a matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Dauda bai taba yi mun maganar ba, bayan lokacin dana sake tun tuba sa sai yace har yanzu ba’a cika ragowar kudaden ba amma na kusa dashi wanda shima yana daga cikin mawakan mai suna Oris yace tuni an baiwa Rarara ragowar nera milyan Arba’in din.
To a hakan dai muka bukaci nera milyan Arba’in da biyu da suka rage a hannun shi ya kawo su azo a zauna a tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar shi na banki ya sami matsala.