NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 27 June 2018

Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

A lokacin wata tattaunawar da yayi da manema labari, wani dan jarida ya tambayi dan kwallon kafar Argentina Messi ko har yanzu yana sanye da wani kambun neman sa'a da ya bashi lokacin wasan Iceland? Sai messin yace Eh.

Messin ya tattare safar kafarshi inda ya nunawa dan jaridar kambun, hakan ya farune bayan kammala wasa tsakanin Argentina da Najeriya wanda ya baiwa Argentinar nasara da ci 2-1.

Dan jaridar dai ya baiwa Messi wannan kambune wanda yace na neman sa'ane kuma shima matarshi ce ta bashi.

Wani likita ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin cin da Argentina tawa Najeriya

Wani likita ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin cin da Argentina tawa Najeriya

Wani babban likita a bangaren kula da lafiyar iyali na asibitin koyarwa dake Abakaliki (FETHA) a jihar Ebonyi, Dakta Chidi Ebirim, ya fadi matacce a jiya, Talata, bayan Najeriya ta gaza samun nasarar zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake bugawa kasar Rasha.

Rahotanni sun bayyana cewar, Dakta Ebirim ya fadi ne bayan kasar Argentina ta zura wa Najeriya kwallo ta biyu a raga.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar an garzaya da kwararren likitan asibiti bayan ya fadi, amma duk da haka y ace ga garinku nan da safiyar yau, Laraba.

“Yana kallon wasan kwallon ne a gidan sa. Amma sai kawai ya yanke jiki ya fadi bayan ya yi wata kara mai karfi yayin da aka saka wa Najeriya kwallo ta biyu a raga,” a cewar shaidar.

Mutuwar kwararren likitan ta jawo tsaiko a lamuran tiyata a asibitin, saboda dukkan likitocin dake aiki a asibitin sun shiga alhini da juyayin rtashin abokin aikin nasu.

Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) sun nuna matukar fushin su a kan wasan na jiya tare da zzargin yiwa kasar makarkashiya, ta hanyar hana ta bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kwallo ta taba hannun dan wasan baya na kasar Argentina a da'ira mai tsaron raga.

Tuesday, 26 June 2018

Wata Inyamura ta zargi Jamil M.D Abubakar, mijin Fatima Dangote da yi mata cikin shege

Wannan iyamurar me suna, Irene Chiamaka Nwachukwu na zargin cewa dan tsohon shugaban 'yansandan Najeriya, Jamil MD Abubakar kuma miji ga diyar Dangote, Fatima Dangote ya mata cikin shege kuma har ta haifeshi.

Matar tace bata da labarin cewa Jamil zaiyi aure kuma shima be gaya mata ba sai da cikinshi da take dauke dashi yakai watanni takwas, tace yanzu ta haifi jaririnta dan watanni biyu kuma yayi kama da Jamil din sosai. Tace ta bukaci Jamil din yazo ayi gwajin kwayoyin halitta dan a tabbatar da cewa danshine amma ya kiya.

Saidai wai ya biyata kudi ta tafi ta bar kasarnan da jaririn dan tayi renonshi a wata kasa can, matar 'yar shekaru 22 tace tunda ya nuna mata shi me kudine dan haka ta bukaci ya biyata miliyan dari.

Amma lauyanshi ya kiya, tace abinda jamil yace zai iya bata shine dubu arba'in duk wata ko kuma miliyan biyar daga nan karta kara nemanshi, amma tace ita taki amincewa da hakan domin miliyan biyar ko dubu arba'in duk wata babu abinda zatayi wajan kula da jaririn.

Tace ta gama hidimar daukar cikin bata yiwa Jamil maganaba dan haka bawai neman kudine yasa tace ya bata miliyan dari ba, tunda yace beson ganinta ko dan nashi to ita zata raini jaririn amma sai ya biyata kudin da tasan cewa asusun bankinta zai tumbatsa.

Ta kara da cewa yanzu lauya na biyu kenan dake kareta akan wannan lamari kuma suna mata barazana, idan bata amince da kudin da yace zai bata ba zasu kai kara kotu su kwace jaririn daga hannunta, harma sun shirya wani sako da aka aikawa matar jamil din na barazana sunce wai itace ta aikashi duk dan suyi maganinta kamar yanda sukace dan haka tace idan wani abu ya faru da ita ko jaririnta sune sila.

Kuma ta janye daga tattaunawar da suke zata tafi kotu tunda bai shirya biyanta abinda ta bukata ba.

Shugaban kasar Philippines ya zagi Allah

Shugaban kasar Philippines, Rodrigo Duterte ya fadi wasu kalaman batanci ga Allah(S.W.A), ya fadi kalamanne a bisa dalilinshi na sukar halittar Annabi Adamu da Hauwa.

Yayi wadannan kalamaine a birnin Davao kuma koda a baya ma ya taba yin irin wadannan kalamai inda yake nuna cewa be yadda da akwai Allah ba. Shugaban kasar yayi kaurin suna wajan sukar darikar katolika inda yake cewa be yadda da Allahn su ba.

Ya fada cewa, shi dai tabbas yasan akwai me gudanar da Duniyarnan amma be yadda da ko wane addini ba.

Me mafana da yawun shugaban kasar lokacin da yake kareshi yace wannan magana da shugaban kasar yayi ra'ayinshine kuma kowa na da 'yancin yi ko kuma kin yin addini asalima 'yan kasar sun san shugaban kasar akan irin wannan ra'ayi nashi shi ba me boye-boye bane tun lokacin yakin zabe ya bayyana haka.

Wannan lamari dai ya dauki hankulan mutane a ciki da wajen kasar.

Wannan kyakkyawar baiwar Allahn na tuna shekaru 7 da suka gabata lokacin da ta zama gurguwa

Wannan kyakkyawar baiwar Allahn na tuna shekaru 7 da suka gabata lokacin da ta zama gurguwa

Wannan kyakyawar baiwar Allahn da rashin lafiya ya sameta wanda yayi dalilin komawarta gurguwa, yanzu take amfani da keke guragu, ta tuna da shekaru bakwai da suka gabata, lokacin da ibtila'in ya sameta.

Tace a duk shekara idan ta tuna da wannan rana takan ji bakin ciki amma wannan karin abin zai zama na daban, ita dai wannan baiwar Allah na matukar burge mutane musamman a shafukan sada zumunta saboda karfin gwiwar ta da kuma kyan da Allah ya mata.

Wannan baiwar Allahn na neman saurayi musulmi da zai musuluntar da ita

Wannan baiwar Allahn na neman saurayi musulmi da zai musuluntar da ita

Wannan baiwar Allahn me suna Jay Teresa ta fito dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa tana neman saurayi, Musulmi kuma a shirye take ta musulunta saboda addinin yana birgeta.

Bayan data bayyana wannan aniya tata batun ya dauki hankulan mutane sosai, Teresa ta kuma fito ta gayawa masu sukarta akan wannan aniya tata da cewa su daina damunta da surutai ita fa babu abinda zai sa ta canja ra'ayinta kuma ba wanine ya sata zata musulunta ba, kawai al'adar musulunci da musulmai na birgeta ne sosai.


Sunday, 24 June 2018

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta fara baiwa 'yan sanda 'yan mata gajerun wanduna dan su rika jawo hankulan turawa masu yawon bude ido kasar, magajin garin Baroummana inda abin ya faru me suna pierre Achkar ya bayyan cewa wanan tsari da suka fito dashi sunyi ne dan canja tunanin kasashen yamma akan kasar.

Lamarin dai ya Jawo cece-kuce tsakanin 'yan kasar amma wasu na ganin cewa hakan ba komai bane.

Wani dan kasuwa da kafar watsa labarai ta Reuters tayi hira dashi yace yana da shago a bakin kasuwa kuma 'yan matan 'yansandan na tsayuwa a bakin shagon nashi suna aiki, shi bega aibun wannan abinba, ya kara da cewa duka matan sun san abinda suke, sun kuma kammala jami'a dan haka ba zasu yarda su yi abinda be dace ba.

Itama wata ma'ikaciyar 'yarsandan da aka yi hira da ita tace ba a tilasta mata yin aikin ba da kanta ta nema kuma tana jin dadin aikin.