NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Friday, 21 September 2018

Karanta sabuwar dabararmar da masu kudi ke amfani da ita wajan yin lalata da mata: Sai ka rike baki

Karanta sabuwar dabararmar da masu kudi ke amfani da ita wajan yin lalata da mata: Sai ka rike baki

Duniya inda ranka zaka ji ka kuma ga abubuwan ban mamaki da yawa, a yayin da malamanmu ke ta kara jan hankalin mutane da a gujewa manyan laifuka, wasu kuwa kara fito da sabon salo suke na tsunduma cikin laifin ido rufe. Zina dai haramunce bama a addinin musulunci ba kadai, harma da sauran wasu addinai.

Duk musulmin kwarai kuwa zai guje mata. Wani lamari me kama da almarane ya faru da wata mata da wani mutum me aure ke son yin lalata da ita.

Baiwar Allahn ta dade tana rokon Allah ya tsareta daga aikata Zina, har taje aikin Hajji inda can ma ta roki Allah kada ya nuna mata ranar da zata aikata Zina, kwatsam sai ga mutumin wanda yana da mata ya sameta inda ya bayyana mata cewa shifa kawai bukatarshi yayi lalata da ita.

Ta gayamishi itafa ga irin addu'ar data ke yi ma akan neman tsari da yin Zina.

Yace mata, kar ta damu idan sukayi suka gama zai biya mata kudi ta sake komawa Makka dan ta roki Allah gafara, ko kumama suje can tare, idan suka gama sai suyi wanka su je dakin Allah su rokeshi gafara.

Shahararren me fadakarwa a shafin twitter, Mustafa da aka fi sani da Angryustaz ne ya bayar da wannan labari inda yace wadda abin ya faru da itane ta bashi labari.


Tuesday, 18 September 2018

Kalli Hotunan Rahama Sadau Tare Da Mawakiyar Kudu D'ja


Wannan hotunan dai na shahararar jarumar hausa da kudu tare da shahararrar mawakiyar kudu wato naija hip hop wanda sunka yi show a cikin garin kaduna wanda ya kayatar sosai wanda ba'a cewa komai ga hotunan kamar haka:-






Kalli zazzafan Hoton HadizGabon da ya birge

Hoton HadizGabon da ya birge

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wannan kayataccen hoton nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kalli wani hoton Zainab Indomie da Kabir A. Zango

Kalli wani hoton Zainab Indomie da Kabir A. Zango

Tauraruwar fina-finan Hausa, Zainab Indomie kenan a wannan hoton da ta dauka tare da kanin Adam A. Zango me suna Kabir, sun haskaka.

Hafsat Idris ta lashe kyatar jarumar jarumai mata

Hafsat Idris ta lashe kyatar jarumar jarumai mata

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris ce ta lashe kyautar jarumar jarumai mata ta City People Award sai kuma abokiyar aikinta, Hannatu Bashir da ta lashe kyautar me taimakawa babar jaruma tashekara.

Muna tayasu fatan Alheri da kuma Allah ya kara daukaka.

Monday, 10 September 2018

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau kenan a wadannan sabbin hotunan nata data saki inda take sannye da doguwar riga me ratsin baki-baki da fari, ta sha kwalliyar zamani ga kai babu dan kwali.





Hotunan Fati Washa da zasu birgeka saidai.....

Hotunan Fati Washa da zasu birgeka saidai.....

Jarumar fim din hausa, Fati Washa kenan a wannan hoton nata da tayi matukar kyau saidi kai babu dan kwali, Allah yasa ta gyara, domin kamar yanda suke cewa koya tarbiyya da wa'azi suke to ya kamata a gansu da alamar mutanen kirki.