NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Tuesday, 8 November 2016

BREAKING :Masu tada kayar baya sun fasa bututun mai a Niger Delta

Masu tada kayar baya sun fasa bututun mai a Niger Delta
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce masu tada kayar baya sun fasa wani bututun mai mallakar jihar Delta a garin Warri.
Wasu masu gadi a Bututan man na kamfanin Trans Forcados, sun sha da kyar bayan da mayakan sa kan suka bude musu wuta, kamar yadda Dickson Ogugu shugaban al'ummar Batan ya shaida wa AFP.
Rahotanni daga kamfanin dilancin labaran ya ce wani jami'in soja ya tabbatar da harin.
A makon da ya gabata an fasa bututun bayan shugaba Muhammad Buhari ya gana da wakilan kungiyar masu tada kayar baya na yankin Niger Delta a wani yunkuri na kawo karshen rikicin yankin.
Kungiyar dai ta bukaci gwamnati ta kashe akasarin kudin da Najeriya ta ke samu daga mai wajen magance matsalar talauci, kuma ta dauki matakai wajen kawo karshen malalar mai da ke lalata muhallan yankin.
Me zakuce akan hakan?

Monday, 7 November 2016

HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya,mace ce bayan mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka Sai jini  ya xo mata ya xa ta yi wanka, shin gabadai xatayi niyya ko kuma wannan na biyun xa tayi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta yi wanka daya kawai.                           
Yana daga cikin ka'idojin SHARIA Idan ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda daya, sannan za'a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta shiga cikin dayar.
Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da WANKAN karshe, saboda saukin musulunci da kuma daukewa jama'a abin da zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj ta tabbatar  da hakan.            
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.

BA'A GAYYACE NI BA BIKIN SARKIN MUSULMI - Bafarawa

BA'A GAYYACE NI BA BIKIN SARKIN MUSULMI - Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alh. Attahiru Dalhatu Bafarawa yace bai je wajen bukukuwan cikar Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar na III shekaru goma saman karagar mulki domin ba'a gayyace shi ba.
Jami'in Yada Labarai na Jam'iyyar PDP a jahar Sokoto Yusuf Dingyadi ne yayi magana adadin Bafarawa "Har zuwa ranar bikin babu wani katin gayyata daga gwamnati ko kuma kashin kai da aka aikowa Bafarawa domin ya halarci taron. Bafarawa ya baro Abuja tun mako daya kamin bikin da tunanin cewa za'a kira shi domin gudanar aikinsa a matsayin Garkuwan Sokoto"
Ya zargi wadanda suka shirya bikin na kin girmama Bafarawa da kowace dama, wanda hakan ne ya sanya shi kuwa bai halarci bikin ba domin kaucewa tozarta da hakan kan iya janyo wa.
Dingyadi ya kara da cewa duk da haka, Bafarawa zai cigaba da kasancewa mai son cigaban Sarkin Musulmi da kuma Daular Usumaniyya.
Sakkwato Birnin Shehu
7th November, 2016

Sunday, 6 November 2016

MIJINA YA SADU DA NI,  KAFIN NA YI WANKAN HAILA?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MIJINA YA SADU DA NI,  KAFIN NA YI WANKAN HAILA?
Tambaya?
Assalamu alaykum, malam inada tambaya, malam mi ar hukuncin mace taqare haila batayi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne: ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a aya ta 222 a suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da yankewar jinin  haila kawai.                                                                           Riko da mazhabar farko shi ne ya fi saboda Allah ya kira haila da cuta.
Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan yankewar jinin haila.
Allah ne mafi sani:
2/11/2016
DR JAMILU ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (73)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA


FATAWAR RABON GADO (73)
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam tambaya ta ita ce mutum ne ya mutu ya bar 'ya'ya, hudu maza,  Biyu mata , sai mahaifiyar sa, Yaya rabon gadon zai kasance?
Amsa:
Wa alaikum assalam,  za'a raba gida  6, a bawa mahaifiyarsa kashi daya, Ragowar a bawa yaransa, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani:
4/11/2016
DR JAMILU ZAREWA

Wednesday, 2 November 2016

FATAWAR RABON GADO (72)|DR JAMILU YUSUF ZATEWA

 FATAWAR RABON GADO (72)
Tambaya?
Assalamu Alaikum Dr, don Allah yaya za'a raba gadon Macen da tabar magada kamar haka : Uwa kadai, ba yara sai 'yan uwa, namiji guda da mata shidda wadanda suka uwa daya?
Amsa :
Wa alaikumussalam,
Za'a raba gida:3, (saboda Raddi) sai a bawa uwa kashi daya, Ragowar kashi biyun sai a bawa 'yan'uwan su raba, babu bambanci tsakanin namiji da mace in za'a raba.
Allah ne mafi sani
31/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

KARATUN ALQUR'ANI, SABODA NEMAN BIYAN BIKATU !|DR JAMILU ZAREWA

.KARATUN ALQUR'ANI, SABODA NEMAN BIYAN BIKATU ! !
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam ya halatta mu taru muyi karatun Alqur'ani don Allah ya kawo mana sauqi kan matsaloli daban daban?
Amsa :
Wa alaikum assalam, Ya halatta a karanta Alqur'ani ayi tawassuli da shi wajan tunkude bala'o'i, saboda shi karatun aiki ne nagari, kuma aiyuka nagartattu ana iya tsani da su wajan neman biyan bikatu kamar yadda hadisai suka tabbatar.                      
Anas Dan Malik daga cikin sahabban annabi s.a.w. ya kasance yana tara iyalansa ya yi addu'a Idan ya kammala karatun  Alqura'ni, wannan sai ya nuna babu laifi yin hakan, saboda aikin sahabi hujja ne, in ba'a samu wani sahabin ya saba masa ba.                                                                       Don neman Karin bayani duba Fataawa Arkanil  Al-Al-Islam N.a. Ibnu Uthaimin: 354.                                                   
Allah mafi sani.
30/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA