December 2016 - NewsHausa NewsHausa: December 2016

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 31 December 2016

Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3

Ayau Ne Ranar Lahadi 01/01/2017 Allah Ya Hukunci “Dauda Kahutu Rara” Da Fitar Da Sabuwar WakarSa mai Suna “Ga Kidan Murna Saura Kiris”
itadai Wan nan Waka Ya Shirya Tane Ga “Inwa Dan Yahaiya” Dake Garin “GwamBe” Allah Ya Nuna Masa An Kwato Karagar Mulkin Gwamnati Gwambe Daga Tsohon Gwamna Gombe “Alh Umar Tanko Almakura” hakan Yasa Rara yayi masa Sabuwar waka Don Nuna Murnar Sa Da Jin Dadinsa a Karkashin Jamiyar #APC,
Yanzu kuma Muna Leken Jahar Taraba Inda Jam Iyar APC Taci Zabe Ankayi Magudi Ankabawa Jam Iyar PDP.
.
Sai ku Kasance Damu a A wan nan ShaFi Don Samun Cikakun Labaran Siyasa Da Wakokin Siyasa
.
Ga link Na Wakar Na Kasa Kuyi Download Kiji.
Note:- Make Sure You Hit Share To Facebook Blow. Thank Download

sabuwar waka Rarara kutare burgu ya gudu maganar jiya ta dawo,part 2 ,waya gayamaka borno gabas take

Barkan Ku Da Yau ‘yan Uwa Maziyarta Wan nan Shafi Na sadeeqmedia.com.ng. hakama Yau Muna Dauke Da Wata Sabuwar Waka Da Shahararren Mawakin Nan Na “APC” Yayi Mai Suna Dauda Adamu
Abdullahi Wanda Jama’a Suka fi Sani Da Dauda Kahutu Rarara waccen Waka Wadda Yayi “kutare Kutare Burgu Ya Gudu ” Haka Kuma Yanzu Ya Sake Yin Wata . mai Taken ” Kai Kutare Mana Burgu Nan Ga Maganar Jiya Ta Dawo” Part (2)
duk Wa’yan Nan Wakokin Ya Shiya Su Ne Ga Tsohon Gwamnan Katsina Shema
Domin Sauko Da Ita Click Download Blow To Listen And Share To Your Friends Thank you….
Download

Friday, 30 December 2016

BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!!

TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahamatullah, dan Allah inaso a amsa min wannan tambayar:-shin kowata irin rantsuwa ce ake yin mata  kaffara kokuwa ba kowace bace ake yiwa kaffara ba ? na gode.
AMSA:
Wa alaikum assalam, ba kowacce rantsuwa ake yiwa kaffara ba,  rantsuwoyi a fiqhun musulunci iri uku ne:
1. Rantsuwar da aka yi akan karya, wannan tana iya turbutsa mutum zuwa wuta, ba ta da kaffara sai istigfari, saboda girman zunubinta.                                                                                                                                            
2. Rantsuwar da ta zo baki yayin magana ba tare da nufi ba, wannan Allah ya yi afuwa akanta, kamar yadda ya bayyana a aya ta: 224 a Suratul Bakara.          i                                                                              
3.Rantsuwa akan wani abu da zai zo nan gaba, kamar ya ce : wallahi gobe zan je wuri kaza, in bai je ba, zai yi mata kaffara, kamar yadda aya ta: 89 a suratul Ma'ida ta tabbatar da hakan.                                                                                                                 
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa

ADDU'AR ZIYARAR MAKABARTA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*ADDU'AR  ZIYARAR MAKABARTA*

*Tambaya:*
SLM Malam wacce addua'a mamaci yafi bukata ? ko kuma Idan an ziyarci kabarin sa wacce addu'a za'a masa ?
*Amsa:*
Wa alaikum as salam, Annabi saw ya shar'anta ziyarar makabarta saboda tana tuna lahira, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 3237, kuma Albani ya inganta shi.
In mutum ya je kabari an shar'anta ya fadi wannan adduar :
السلام عليكم أهل الديار من المؤمنين  والمسلمين، وإنا إن شاء الله  للاحقون، أسأل الله لنا ولكم العافية.
Assalamu alaikum Ahlad diyaar minal Mu'umineena wal Muslimeena, wa innaa insha Allahu La laahiquuna, as'alullaha lanaa wa lakumul 'aafiyah, Muslim a hadisi mai lamba ta : 2302.
Allah ne mafi sani
04/11/2015
*Amsawa*
Dr. jamilu yusuf zarewa

TAYI AURE DA CIKIN SHEGE | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE ? ?*

*Tambaya:*
Assalamu alaikum.  Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

*AMSA :*
Wa alayku assalam Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini  wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.                             
Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.                    
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud : 1847. Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79
A fahimtata,  fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren,  saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa,  kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.
Allah ne mafi sani.
27/2/2016
*Amsawa*
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

Thursday, 29 December 2016

WADATAR ZUCIYA MP3 DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Wannan wata muhadara ce wacce Dr. Jamilu yusuf zarewa ya gabatar a gidan radion freedom kano mai suna wadatar zuciya
sai kayi danna ko latsa wanannan link domin kayi download wanannan muhadarah


Ayi sauraro lapia
NB:domin karin bayyani sa ka tuntubemu ta wanannan number 09032038203ko ka ajiye comment dinku a inbox namu na comment

FATAWAR RABON GADO (86) |DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (86)

Tambaya?
Assalamu alaykum.
Tambayata shine idan mamaci ya rasu ya bar yara mata guda4 da mata 1 sai mahaifiyarsa bai da yaro namiji ko daya shin dan uwansa wato yayansa xa.a iya rava gadon da shi?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
za'a raba abin da ya bari gida: 24, sai a bawa matarsa kashi: 3, 'ya'yansa Mata kashi: 16, mahafiyarsa kashi: 4. Idan dan'uwansa da ka ambata shakiki ne ko li'abbi sai ya dauke kashi dayan, in uwa daya kawai aka hada da shi ba zai yi gado ba, tun da mamacin yana da 'ya.
Allah ne mafi sani
18/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA

SOKOTO INDIGENES TO ENJOY FREE REGISTRATION FEES AT SOKOTO STATE UNIVERSITY.

SOKOTO INDIGENES TO ENJOY FREE REGISTRATION FEES AT SOKOTO STATE UNIVERSITY.
When a leader did well then he must be commended on that, I must begin with Commending on the effort of Governor Aminu Waziri Tambuwal on his affirming the payment of Registration fees of the indigene Student of Sokoto State University, as the Government being paying for our colleagues in the Sister University (UDUS) and other Institutions in the State.
It has been a long time since the Student complained and waited for the free Registration, but God planned everything and it's time, today His Excellency gift us with this good news we've been waiting for at the 3rd Founders Day Lecture of Sokoto State University.
At the same time he commented on the Staff Quarters of the University which will be finished and distributed as soon as possible as well as be used accordingly. His Excellency made some good points which I admire so much. Of course Sokoto State University will be great if this efforts keeps moving on.
Also creation of New College for Medical Courses (MBBS) is a development to our World Class University as well as making Murtala Muhammad Hospital as the teaching Hospital for the College. This is a great addition to our University and the State as well.
I will use this medium to extend my appreciation to His Excellency Aminu Tambuwal and his Government on these great job they did to us. Indeed if a leader may be accused on his wrongs then he must be appreciated on his good jobs, Kudos Your Excellency, will keep my eyes open on the effort you will make to our beloved State.
Congratulations to my Colleagues in Sokoto State University as well as The Management of the University. God bless our State and Our Nation.
Fahad Longman.
Student, SSU.

Wednesday, 28 December 2016

MAI YASA BAHAUSHE YAKE DA SAURIN SAKIN AURE ?DAGA MATAN KO MAZAN. ? | SHEIKH AMINU DAURAWA

MAI YASA BAHAUSHE YAKE DA SAURIN SAKIN AURE ?

DAGA MATAN KO MAZAN. ?
Sakamakon bincike da muka gudanar akan wasu
zawarawa dubu hudu, ya nuna mana hausa-fulani,
sune na biyu, a wajen sakin aure, a duniya, bayan
wata kabila a India, Binciken mu ya nuna mana abubuwa arbain (40) sune
mafi yawan dalilan da suke jawo yawan saki, a wajen
hausawa
1- Rashin ilmin zamantakewa ta aure
2- Al'adu
3- Bidi'o'i 4- matsalar miji
5- matsalar mata
6- matsalar iyayan miji
7- matsalar iyayen mata
8- matsalar dangin miji
9- matsalar dangin mata 10- Rashin tsafta
11- Rashin iya kwalliya
12- Rashin iya magana
13- Rashin ciyarwa
14- Rashin iya kwanciyar aure
15- matsalar rashin adalci 16- Mace goyan kaka
17- Aure kisan wuta
18- Matsalar gidan haya
19- Ruwan ido wajen zabin abokin zama
20- Cin Amanar Aure
21- Auren bariki 22- Auren mace dan kudinta
23 Auren kiyayya
24- Matsalar talauci
25- matsalar kawaye
26- matsalar Zafin kishi
27- Kin haihuwa 28- tsiwa da rashin ladabi
29- Shan kayan maye
30- kannan miji
31- Abokan miji
32- mace mai sata
33- Annamimanci da gulma 34- tsananin talauci
35- Matsalar wayar sadarwa
36- Rashin lafiyar namiji wajen gamsar da mace
37- Rashin lafiyar mace wajen gamsar da miji
38- Sharrin bokaye
39- Rashin tatttaunawa da bin matakai wajen warware matsala
40 Mace mai aikin gwabnati
A ganin ku da mata da maza wa yafi yawan jawo
dalilin rabuwa ?

SANYA BAKAKEN TUFAFI DA DUKAN JIKI A RANAR ASHURA DA SUNAN BAKIN CIKI DA RANAR DA AKA KASHE HUSAINI (RA). |Dr mansur sokoto

SANYA BAKAKEN TUFAFI DA DUKAN JIKI A RANAR ASHURA DA SUNAN BAKIN CIKI DA RANAR DA AKA KASHE HUSAINI (RA).

Babu shakka ranar Ashura rana ce wacce Allah subhanahu wata'ala ya girmama jikan Manzon Allah (saw) da samun shahada, wacce ta qara nuna girmansa da darajarsa a wajen Allah.
Sayyadina Husain mutum ne mai daraja, manzon Allah (saw) yana kaunarsa shi da yayansa Alhassan, kuma yana kusanto su zuwa gare shi, har ma ya fada game da su cewa su ne shugabannin samarin Aljanna.
Allah subhanahu wata'ala ya kaddara ma sa shahada bayan da mutanen KUFA (babbar cibiyar shi'anci a wancan lokacin) su ka yaudare shi suka ce ya zo za su yi ma sa mubaya'a a matsayin khalifa shi kuma ya gaskatasu ya amsa gayyatarsu. A gefe guda kuma manyan masoyansa Abdullahi bin Umar da Abdullahi bin Abbas su na ta kokarin hana shi tafiya tunda sun fahimci yaudarar da ke cikin gayyatar.


Al Imam ibn Kasir ya hakaito cewa bayan Abdullahi bin Abbas (ra) ya bawa sayyadina Hussain (ra) shawarar kar ya amsa gayyatar shi kuma ya dage kan sai ya tafi, sai Ibn Abbas (ra) ya sake dawowa bayan kwana biyu wajen Sayyadina Husain (ra) ya ce da shi: “Ya dan baffa na, na yi qoqarin na haqurqurta da raina kan tafiyarka amma na kasa haquri, ina matuqar ji ma ka tsoron wannan tafiyar, domin mutanen Iraq mayaudara ne, don haka kada ka rudu da su, ka yi zamanka a nan Makkah har mutanen Iraq su gama da abokan adawarsu sannan sai ka je mu su, idan kuma ka dage sai ka tafi, to ka tafi yaman domin a can akwai jama'ar da za su baka kariya, kuma mahaifinka ya na da magoya baya a can, kuma idan ka je can din ma ka yi nesa da su, ka fara aika mu su da wasiqar manufar zuwanka, idan ka yi haka ina sa ran za ka sami abin da ka ke so." 

Sai Sayyadina Husain (ra) yace da Ibn Abbas (ra) “Ya kai dan baffa na, haqiqa na san kai mai nasiha da tausayawa ne a gare ni, amma na riga na daura niyyar tafiya." Sai Ibn Abbas (ra) yace da shi: “tunda ka dage sai ka tafi to dan Allah kar ka tafi da 'ya'yanka da matanka, domin wallahi ina ji ma ka tsoron kada a kashe ka a gabansu kamar yadda aka kashe Sayyadin Usman (ra) a gaban matansa da 'ya'yansa."

Abdullahi ibn Zubair (ra) y ace da Sayyadina Husain (ra): “Yanzu za ka tafi wurin mutanen da su ka kashe babanka su ka soke dan uwanka?" sai sayyadina Husain yace: “gara a kashe ni a guri kaza da azo ma ka a hantata."
Shi ma Abdullahi ibn Umar (ra) da ya ji labarin Sayyadina Husain (ra) zai tafi sai ya garzayo ya same shi bayan ya yi tafiyar kwana biyu ko uku, ya ce da shi: “Ina zaka?” sai sayyadina Husain (ra) yace: “Iraq" sai ya fito da tulin takardu ya nuna Ibn Umar (ra) y ace: “wadannan wasiqun su ne da su ka aiko min su na yi mini mubaya'a." sai Ibn Umar (ra) ya ce da shi ka da ka je. Sai ya qi, sai Ibn Umar (ra) yace bari na gaya ma ka wata magana: “haqiqa Mala'ika Jibril (A.S) ya zo wajen manzon Allah (saw) ya kuma ba shi zabi tsakanin duniya da lahira sai ya zabi lahira bai zabi duniya ba, kai kuma tsoka ce da jikin manzon Allah (saw) don haka babu wanda zai jibinceta a cikinku, kuma Allah bai kawar da ita daga gare ku ba sai don ya zaba muku abinda ya fi ta alheri." Duk da haka Sayyadina Husain (ra) ya dage sai ya tafi, sai Abdullahi ibn Umar (ra) ya rungume shi ya na kuka ya na yi ma sa ban kwana. - Ibn Kasir, al-Bidaya wannihaya, (11/496-498), madaba'ar Hajar-Aljiza. Shekarar bugawa 199.

Allahu akbar! KADDARA TA RIGA FATA! Sayyadina Husain (ra) ya tafi Iraq, su kuma mutanen kufa su ka tsare shi a wurin da ake kira KARBALA, su ka hallaka shi. Allah Ya qara Rahama a gare shi.
Dama Allah ya kan jarrabi bayinsa ne gwargwadon karfin imaninsu, kamar yadda ya tabbata daga Mus'ab bn Sa'ad (RA) yace na tambayi manzon Allah (saw) na ce: “Ya ma'aikin Allah! su waye su ka fi shiga cikin tsananin bala'i? sai yace: “Annabawa, sannan wadanda su ke jin tsoron Allah mataki bayan mataki. Ana jarrabar mutum gwargwadon addininsa, idan addininsa mai karfi ne sai bala'insa ya tsananta. Idan kuma addininsa mai rauni ne sai a jarrabe shi gwargwadon addininsa. Bala'i ba zai gushe ga bawa ba, har sai ya kasance yana tafiya a kan kasa ba shi da wani zunubi a kansa." (Tirmidhi: 2398. Kuma yace Hadisi ne Hasanun Sahih)

Su kuma Alhasan da Husain (RA) su na daga cikin wadanda Allah ya kaddara mu su matsayi madaukaki, kuma an haife su a lokacin da musulunci ya tsaya da kafafunsa, kuma sun taso a cikin buwaya da karamci, dukkanin sahabbai su na girmama su, kuma manzon Allah (saw) ya koma ga Allah tun su na kanana. Domin Allah ya cika mu su ni'imarsa a gare su sai ya jarrabe su a karshen rayuwarsu, ta yadda aka yi mu su kisan gilla Allah ya azurta su da shahada.

Don haka duk musulmi na gari yana jin ciwon kisan gillar da aka yi wa Sayyadina husaini RA) kamar yadda yake jin ciwon kisan gillar da aka yi wa Sayyadina Aliyyu da sayyadina Umar da Sayyadina Uthman Allah ya kara yarda a gare su.
Sai dai mumini idan musiba ta same shi maida lamarinsa yake yi ga Allah. kamar yadda Allah yace:
“…. Ka yi wa ma su hakuri bushara, su ne wadanda idan musiba ta same su, suke cewa lallai mu daga Allah muke, kuma lallai mu ma su komawa ne gareshi. wadananan suna da daraja da rahma daga ubangijinsu kuma wadannan su ne shiryayyu". (Baqara 155-156).

Sannan kuma hadisi ya tabbata daga Annabi (saw) yace: “Babu wani musulmi da za'a jarrabeshi da wata musiba yace Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, ya Allah ka bani lada a cikin wannan musiba da ta same ni ka musanya mini da mafi alkhairinta. Face Allah ya musanya ma sa da mafi Alkhairinta." (Muslim:1525)
Wannan shi ne abinda ya kamata kowa ne mumini ya yi yayin da kowace irin musiba ta same shi amma maimakon haka sai shaidan ya jefa mutane cikin bidi'oi ta sababin wannan mutuwar.

Bidi'a ta farko ita ce: Bakin ciki da kuka da marin fuska da hargowa da jiyar da kai kishirwa.

Bid'ah ta biyu kuma ita ce: sanya bakaken kaya da jima kai rauni da wakokin nuna jimami wadanda sukan kai ga zagin manyan sahabbai wadanda su ke da rigaye da falala a cikin wannan addinin da la'antarsu da shigar da wanda ba shi da laifi cikin laifi, da karanta labaran yadda aka kashe shi wandanda su ke cike da tatsuniyoyi da karerayi.

Babbar manufar wadanda su ka shirya wadannan abubuwan ita ce bayarda kofar fitina da rarraba kan al'umma. Domin dukkan musulmi sun yi ijima'i kan abinda su ke yi ba wajibi ba ne ko mustahabbi. Bari ma dai raki da kukan kera saboda musibar da ta riga ta faru, yana daga mafin girman abinda Allah da manzonsa suka haramta.

Kuma da hakan yana da wani asali to da mahaifinsa sayyidina Aliyu (RA) ya kamata a fara yiwa wannan tunda shi ma kashe shi aka yi, kamar yadda kowa ya sani. Kuma mutuwar manzon Allah (saw) ita ce mafi girman masifa ga al'ummarsa, amma ba mu taba jin cewa wani daga cikin sahabbai ko ahlil baiti sun yi taro a kowace shekara don nuna jimami da baqin cikin wannan babban rashi ba, wanda da hakan alheri ne da sun rigaye mu. Tunda ba su yi ma sa ba kuwa, to lalle yi wa wanda bai kai matsayinsa ba bidi'a ce mummuna abar kyama, musamman ma idan muka yi duba da cewa manzon Allah (saw) ya hane mu yin koke-koke da marin fuska yayin musiba kuma yace yin haka aiki ne na mutanen jahiliyya wadanda basu san addini ba. Manzon Allah (saw) yace:
“Baya cikinmu wanda ya mari kuncinsa ko ya yaga wuyan rigarsa ko ya yi da'awa da da'awa irin ta jahiliyya." (Bukhari: 1294)
Haka nan hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Mas'ud (RA) yace: “hakika ni babu ruwana da wanda manzon Allah (saw) ya nuna babu ruwansa da shi.

“Lalle manzon Allah (saw) babu ruwan sa da mai kururuwa yayin musiba, da mai aske kansa yayin musiba, da mai keta tufafinsa ko jikinsa yayin musiba." (Mulim:104)
Saboda wadannan dalilai ne muke kira ga al'ummar musulmi da su guji irin wadannan tarurrukan da su ka sabawa littafin Allah da karantarwar manzon Allah (saw) da fahimtar magabata na kwarai wadanda babu abinda yake cikinsu sai rudani da yaudarar ma su qarancin ilmi wadanda ba su fahimci addininsu ba.
Don haka ya kamata wadanda suke riqar ashura ranar biki ko idi su sani da yahudawa suke koyi ba da manzon Allah (saw) ba. Domin manzon Allah (saw) AZUMI ya yi, kuma ya kwadaitar da al'ummarsa falalar yinsa, kamar yadda ya zo a cikin sahihi Muslim cewa: an tambayi Manzon Allah (saw) game da azumin ashura sai yace: “Yana kankare zunuban shekarar da ta gabata." (Muslim: 1162)

Amma sanya baqaqen tufafi a wannan ranar ko kuma watanta daga cikin ranaku da sunan ibada; wannan ba shi da asali a cikin addinin musulunci. Bari ma dai litattafan shi'a Rafida sun kushe sanya baqaqen tufafi a matsayin wata alama ta addini.
Ga misalign kadan daga maganganun malamansu akan hakan:

1. Assaduk ya rawaito da isnadinsa zuwa Ja'afar Assadiq (A.S) yace: “Allah ya yi wahayi ga wani annabi daga annabawansa, (yace da shi) kace da muminai kada ku sanya tufafin maqiyana, kada ku ci abincin makiyana, kada ku bi tafarkin maqiyana sai ku zama maqiyana kamar yadda su ke maqiyana." (Duba Alfaqih(1/252), da Wasa'ilish shi'ah (4/384), da Biharul Anwar (2/291).
Don sanin wadanne irin tufafi ne tufafin makiyan Allah da su ke cewa kada a sanya duba littafinsu mai suna "Uyunul Akhbar" daga Sayyadina Aliyu daga manzon Allah (saw) yace: “Lallai tufafin makiya na su ne bakake." (Duba Uyunul Akhbar 1/26).

2. Haka nan an rawaito daga Abi Abdillah (A.S) wani mutum ya tambaye shi ko zan iya yin sallah da baqar hula? Sai yace:
“Kada ka yi sallah da ita domin ita tufafin 'yan wuta ne." (Duba Alwasa'il (3/281) Babi na 20, Hadisi na 3 cikin Babu Libasil Musalli. Da Alfaqih, na Assaduq (2/232).

3. Alhurrul amili ya rawaito daga saduq daga Sayyadina Aliyyu (RA) yace da sahabbansa: “Kada ku sanya bakaken tufafi domin haqiqa su tufafin FIR'AUNA ne." (Duba Man La Yahduruhul Faqih, (1/251), da Alwasa'il, (3/278) cikin Abwabul Libas.)
Wadannan 'yan dalilai da su ka fito daga litattafan jagororin ma su sanya bakaken kaya a matsayin wata alama ta addini sun isa su sa ma su yi su gane batancin abinda suke yi. Allah ka bamu ganewa amin.

- Daga littafin ZARARREN TAKOBI AKAN BIDI'O'IN WATANNIN SHEKARA Na Sheikh AbdulWahhab Abdallah.

AMFANIN ZOGALE GOMA SHATAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM

AMFANIN ZOGALE GOMA SHA
TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM
==========================
Ana Bukatar Jama'a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al'umma domin Qaruwa da Juna.
.
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a
sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
.
2- Ana shafa danyen ganyen zogale
akan goshi
domin maganin ciwon kai.
.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen
ganyen zogale
inshaAllah jinin zai tsaya.
.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya
hada garin
zogale da man zaitun ya shafa.
.
5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko
gembo domin saurin warkewa.
.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci
yana
maganin hawan-jini da kuma karama mutum
kuzari.
.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa 'yar
kadan domin maganin ciwon
shawara.
.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga
ruwan
danyen zogale, haka ma mai fama da
ciwon
kunne.
.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da
zuma dan karin nono.
.
10-Wanda ke fama da yawan fitsari
wato cutar
Diyabetis ya rinka shan furen zogale
da citta kamar shayi.
.
11-Idan aka tafasa furen zogale da
albasa aka
sha kamar shayi yana maganin
sanyi.
.
12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin
tsutsar ciki ga yara.
.
13-Ana daka ganyen zogale da
'ya'yan baure a
sha da nono ko kunu yana maganin
ciwon hanta.
.
14-Ga mai fama da sanyin kashi ko
wani kumburi
zai soya 'ya'yan zogale a daka su
sannan a hada
da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
.
15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke
ciki tare da karanfani, citta, masoro
da kuma
kimba domin karin karfin da namiji
da sa masa
kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
.
16-A daka saiwar zogale da 'ya'yan
kankana a
sha da nono yana maganin tsakuwar
ciki
(Apendis).
.
17-Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon
Aids zogale kan radadinshi ta hanyar
shan ruwan
dafaffen zogale.
.
18-Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria
da kuma ciwon basir ko shawara, zai
iya yawaita
shan ruwan dafaffen zogalen domin
samun sauki.
.
Ana Bukatar Jama'a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al'umma domin Qaruwa da Juna.
.
Allah ya kara mana lafiya kuma ya bamu ikon
gode masa da ita ta hanyar aikata
umurninsa da
nisantar abinda ya hana

Latest Airtel 0.00kb Free unlimited Browsing Settings Via Psiphon | Airtel Live

Assalamu alaikum warahamatullah yan uwana kamar yadda kunka sani wanannan site an ginashi domin fadakarwa ta fanin addinin musulunci naga ya dace ku samu wanannan garabasa ta airtel free browsing domin yana taimakawa mutum

GA YADDA ZAKA SAITA PSIPHON

Yadda zaka setting din APN
Name: Zain NG 
APN: internet.ng.zain.com 
Proxy: blank 
Port: blank 
Username: internet 
Password: internet

yadda zaka setting na handle dinka
✔ Tick Remove Port
✔ Proxy Type: No proxy
✔ Proxy Server: Airtellive.ng
✔ Real Proxy Type: Default
✔ Real Proxy Server: Leave Empty
✔ Real Proxy Port: 80

yadda zak setting na configuration
ma'ana more options
Tick connect through an HTTP proxy
Then tick use the following settings and apply below variables appropriately.
Host address : 172.24.248.150
Port : 8080

shikenan sai ka dawo bayya kayi tap na connecting

  • idan  baka da psiphon kayi click  a nan

  • Allah yasa adace

Domin karin bayyani
sai ka tuntubemu ta namu wanannan lambar  09032038203

Tuesday, 27 December 2016

FATAWAR RABON GADO (86) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (86)

Tambaya?
Assalamu alaykum.
Tambayata shine idan mamaci ya rasu ya bar yara mata guda4 da mata 1 sai mahaifiyarsa bai da yaro namiji ko daya shin dan uwansa wato yayansa xa.a iya rava gadon da shi?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
za'a raba abin da ya bari gida: 24, sai a bawa matarsa kashi: 3, 'ya'yansa Mata kashi: 16, mahafiyarsa kashi: 4. Idan dan'uwansa da ka ambata shakiki ne ko li'abbi sai ya dauke kashi dayan, in uwa daya kawai aka hada da shi ba zai yi gado ba, tun da mamacin yana da 'ya.
Allah ne mafi sani
18/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA

Yadda zaka magance matsalar not Received apk a wayar android

Assalamu alaikum warahamtullah
barkamu da asuba da fatan kowa yana cikin koshin lafiya
yau zanyi bayyani akan yadda wayar  android phone suke wahalar da mutane akan apks
Received application
zakaga wani idan anka turamasa application a Bluetooth baya shiga sai kabi wani hanya
ka karbi wayar wanda zai turamaka application sai kayi rename na application din misali

sai ka mayar da shi
xender.mp3
sai ka tura, idan ka tura ya shiga sai sai kaje kan wayarka a cikin memory or internal sai ka shga Bluetooth folder
sai ka danna kan application da katuro zai nuna maka rename
sai kayi rename zuwa

shikenan sai kayi installing
domin karin bayyani sai ka tuntubi wanannan number 09032038203

ME YASA AKE KAFIRTA 'YAN SHI'A | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

ME YASA AKE KAFIRTA 'YAN SHI'A

Tambaya :
Assalamu alaikum, ina yiwa malam fatan alkairi, Allah ya hadamu a Aljannar da koramu suke gudana a cikinsa, tambayata shi ne: Don Allah malam wanne abubuwa ne wanda 'yan Shi'a suke aikatawa wanda ya fitar da su daga musulunci ?
Amsa:
To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai manyan abubuwa wadanda suke warware musulunci:
1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi da yawa a cikin alqu'ani, duk wanda ya ce mafi yawancin sahabban Annabi s.a.w. sun kafirta tabbas ya karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a fili yake.
2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa : Alqur'anin da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa : Allah ya tabbatar : zai kiyaye shi, har abada.
3.Suna riya cewa : an yi kuskure wajan baiwa Annabi S.a.w. Annabta, sayyadi Aliyu ya kamata a bawa, sai mala'ika Jibrilu ya yi kuskure ya bawa Annabi Muhammad S.a.w, tabbas wannan maganar ta kunshi nuna gajiyawar Allah da kuma karyata shi.
4.Rafidha 'yan shia sun tafi akan cewa Nana A'isha Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi guda goma a suratun Nur.
Ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za'a kira shi da kafiri, dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.
Yana daga cikin ka'idoji a wajan malaman AHLUSSUNNAH ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin 'yan shi'a da gama-gari wadanda suka shiga shi'a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirata su ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa da suka gabata, amma wanda ya aikata daya daga cikin su da ilimi to malaman musulunci da yawa sun dora masa KAULASAN.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Ashshifa'a Na Kadhi IYadh 2\286 da Al-kifaya :67
Dr. Jamilu Zarewa
24\12\2015

Monday, 26 December 2016

YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE ?

YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE ?

Tambaya?
Assalamu alaykum. Tambaya malam saurayi da budurwane shaidan yashiga tsakaninsu har yakaiga saurayin ya tsotsi qirjin budirwan har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru ba so dayaba ba biyu ba amma bata taba ganin ruwanba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu, ya halatta suyi auren?
Kuma minene hukuncin shan Ruwan da yayi
Amsa:
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa wannan abin da suka aikata mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taba jikin matar da ba ka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina, idan mutum ya tsotsi nonan mace bayan ya girma Amma babu ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma idan akwai ruwa a ciki, to
malamai sun yi sabani akan hakan
zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure
shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru
biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha
saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102,
ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga
nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan
ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba
zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita
ce maganar mafi yawan malamai.
2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare
shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci matar Abu-
huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a
gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a
hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a
lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake
nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi
tasiri wajan haramcin aure. Zancen da ya fi karfi
shi ne nonon da mutum ya sha bayan ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba shi.
Don neman Karin
bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saba masa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
26/12/2016
*Dr Jamilu zarewa*

Sunday, 25 December 2016

ZAMA BA AURE, BAYAN MUTUWAR  MIJI ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*ZAMA BA AURE, BAYAN MUTUWAR  MIJI ?*

*Tambaya?*
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakaatuhu, Don Allah Mallam zan iya zama ba tare da na sake aure ba kasancewar mijina ya rasu kuma inaso Allah Ya hada ni da shi a matsayin mijina a aljannah?
*Amsa :*
Wa alaikum assalam,
in har kina da bukatar auran zai fi kyau ki yi, Tunda Allah zai iya ba ki Wanda ya fishi alkairi, sannan za ki iya haifar 'ya'yan da Za su zama sababin shigarki Alanna.                                                Amma in har ba ki da bukata kuma za ki iya daurewa, kina kuma fatan shiga aljanna, to kina iya jira kamar yadda matar Abuddarda’a ta ki aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu’awiya ya nemi ya aure ta, taki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da Abudarda’a sahabin Annabi s.a.w. a lahira.                                                                    A duba
silsilasahiha hadisi mai lamba ta: 1281.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍
*DR JAMILU YUSUF ZAREWA*

  • 11/12/2016

FATAWAR RABON GADO (85) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (85)

*Tambaya*
  Assalam dan Allah ya rabon gadon wanda ya mutu ya bar uwa da uba da mata da 'ya'ya maza da mata zai kasance ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, za'a raba gida 24, sai a bawa uwa kashi 4, uba kashi 4, matar kashi:3, ragowar kashi:13  sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
10/12/2016

Saturday, 24 December 2016

[MP3]Wa'azin Kasa A Garin Gombe 2016​

​Wa'azin Kasa A Garin Gombe 2016​
����������������������
✔ ​Wannan Shine Wa'azin Kasa da Kungiyar Jama'atil Izalatil Bid'ah Wa'iqamatis Sunnah Ta Shirya Gabatarwa  Yau a Stadium na Fantami dake Cikin Garin Gombe.​
​GA YADDA WA'AZIN YA GUDANA​
____________________________________
1⃣ Dr Abdulmutalkib Gidado Kano
http://darulfikr.com/s/11244
2⃣ Malam Muhammad Barkindo
http://darulfikr.com/s/11245
3⃣ Dr. Mansur Isa Yelwa
http://darulfikr.com/s/11246
4⃣ Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
http://darulfikr.com/s/11248
5⃣ Sheikh Muh'd Kabir Gombe
http://darulfikr.com/s/11250
6⃣ Jawabin Mai Girma Gwamna
http://darulfikr.com/s/11249
7⃣ Sheikh Abubakar Giro Argungu
http://darulfikr.com/s/11252
8⃣ Dr. Jamil Zarewa
http://darulfikr.com/s/11253
9⃣ Shugaba Abdullahi Balalau
http://darulfikr.com/s/11255________________________________

💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳
   *WA'AZIN RANAR LAHADI DA SAFE*
💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳

1⃣ Sheikh Muhammad Alkali http://darulfikr.com/s/11260

2⃣ Sheikh Umar Jega
http://darulfikr.com/s/11261

3⃣vu Sheikh Ali Mustapha Maiduguri
http://darulfikr.com/s/11262

4⃣ Sheik Muh'd Kabir Gombe
http://darulfikr.com/s/11263

5⃣ Sheikh Abubakar Giro Argungu
http://darulfikr.com/s/11264
 ku
Kasancewa Damu A www.sadeeqmedia.com.ng Domin Samun Updates
24/03/1438 Ah.
24/12/2016 C.E

FATAWAR RABON GADO (85) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (85)

*Tambaya*

  Assalam dan Allah ya rabon gadon wanda ya mutu ya bar uwa da uba da mata da 'ya'ya maza da mata zai kasance ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam, za'a raba gida 24, sai a bawa uwa kashi 4, uba kashi 4, matar kashi:3, ragowar kashi:13  sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*

*DR Jamilu Yusuf Zarewa*

10/12/2016

FA'IDOJIN RUWAN ZAMZAM 36 | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO

FA'IDOJIN RUWAN ZAMZAM 36

1 ZAMZAM, MALAIKA JIBRILU, YA TONA SHI.
2 ANNABI ISMAILA YA FARA SHAN ZAMZAM.
3 ZAMZAM SHINE ASALIN KAFUWAR BIRNIN MACCA
4 DA ZAMZAM AKA WANKE ZUCIYAR ANNABI SAW.
5 BABU RUWAN DA YA FISHI DARAJA, A DORAN KASA. 6 ANNABI SAW YA SHA RUWAN ZAMZAM.
7 ANNABI SAW YA ZUBASHI A JIKINSA.
8 ANNABI SAW YAYI GUZIRIN SA ZUWA MADINA.
9 ANNABI SAW YACE ,RUWAN ZAMZAM ZAKA SAMI
BUKATAR DA KASHA SHI, SABODA ITA.
10 NANA AISHATU RA, TANA GUZIRIN ZAMZAM. 11 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM, MALAMAI
SUKAYI SABANI, GAMAI DA WANKA DA SHI, DA
ALWALA DA TSARKI DA WANKE NAJASA.
12 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM MALAMAI
SUKAYI SABANI, DA SHI DA RUWAN KAUSAR A WANNE
YAFI? 13 MAL IBN HABIB BAMALIKAI, YACE ANSO GA WANDA
YAYI HAJJI, YA YAWAITA SHAN ZAMZAM, SABODA
SAMUN ALBARKA, YAYI ALWALA YAYI WANKA.
14 SHAIK ALBANIY YACE, YA KAMATA ALHAJI, YAYI
GUZURI DA ZAMZAM, DOMIN NEMAN ALBARKA,DOMIN
ANNABI YAYI GUZIRIN SA A CIKIN GORA DA SALKA ZUWA MADINA, YANA ZUBAWA MARASA LAFIYA YANA
SHAYAR DA SU.
15 MAL ANNAWAWIY, YACE , MAZAHABARMU KAMAR
TA JAMHURIN MALAMAI, BABU LAIFI AYI WANKA DA
ZAMZAM, KUMA AYI ALWALA.
16 MAL WAHAB IBN MUNABIH YACE: ZAMZAM ABIN SHAN MASU NAGARTA, YANA TSAYAWA A MATSAYIN
ABINCI DA ABIN SHA, KUMA WARAKA DAGA LARURA.
17 MAL KHALIL, A CIKIN MUKTASAR YACE : YANA DAGA
CIKIN ABINDA AKE SO GA ALHAJJI, YA YAWAITA SHAN
ZAMZAM.
18 ACIKIN SHARHIN AN SANHURIY YACE: YANA DAGA CIKIN ABINSO, YAWAITA SHAN ZAMZAM, DA ALWALA,
DA WANKA, DA YAWAITA ADDUA A LOKACIN SHAN
ZAMZAM GA ALHAJI.
19 AL IMAM SHAFII, YACE: MUSTAHABBI NE YAWAITA
SHAN ZAMZAM.
20 MALAMAI SHAFIAWA SUNCE: MUSTAHABBI NE SHAN ZAMZAM, DA YAWAITA SHAN SA, KUMA ANSO MUTUM
YA SHIGA CIKIN INDA RIJIYAR ZAMZAM TAKE, YA KALLI
RUWAN, YA DEBO DA GUGA, YA SHA YA ZUBA AKANSA.
DA FUSKARSA, DA KIRJINSA, KUMA YAYI GUZURI DA
SHI.
21 MAL HASANUL BASARI YACE: IDAN AN SHA RUWAN ZAMZAM AYI ADDUA, YANA CIKIN GURARE 15 DA AKE
SA RAN KARBAR ADDUAR MASU AIKIN HAJJI, SUNE
WAJAN DAWAFI, MULTAZAM, KARKASHIN INDARARO,
CIKIN KAABA, ZAMZAM, KAN SAFA, KAN MARWA,
CIKIN SAAYI, BAYAN MAKAMU IBRAHIM, MUNA, FILIN
ARFA, MUZDALIFAH, JAMRA GUDA BIYU TA FARKO DATA BIYU ANA TSAYAWA AYI ADDUA.
22 ABDULLAH DAN ABBAS RA, IDAN YA SHA ZAMZAM
SAI YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH KA BANI ILMI MAI
AMFANI , DA ARZIKI MAI YALWA, DA WARAKA DAGA
DUKKAN LARURA.
23 ABDULLAH DAN MUBARAK IDAN YA SHA ZAMZAM SAI YA KALLI GABAS YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH
MANZON ALLAH SAW YACE, RUWAN ZAMZAM ZAKA
SAMI BUKATAR DA KASHA SHI SABODA ITA, TO GANI
NA SHA, KA RABANI DA KASHIRWA RANAR
ALKIYAMA.
24 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN ZAZZABI DA MASHASHARA.
25 RUWAN ZAMZAM YANA ZAMA DALILIN KANKARE
ZUNUBI WANDA YASHA DA NIYAR TUBA
26 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN HADDA,
WANDA YAKE SHA DA NIYAR HAKA, KAMAR YADDA AL
IMAM SUYUDIY YAYI YA ROKI ILMIN FIQHU DA HADIS. 27 RUWAN ZAMZAM YAN KARA KARFIN MUTUM WAJAN
MU'AMALA DA IYALI,
28 SHAN ZAMZAM ALAMACE TA IMANI.
29 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN YAWAN JIRI,
30 WANKE FUSKA DA ZAMZAM YANA KARA KARFIN
IDO. 31 SHAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN ZUCIYA.
32 SHAN ZAMZAM YANA TAFIYAR DA YAWAN FIRGICI
DA TSORO.
33 SHAN RUWAN ZAMZAM YANA RAGE GIRMAN KAI.
YANA HORE ZUCIYA.
34 KALLON RUWAN ZAMZAM YANA DA AMFANI. 35 MAL ALBANIY YACE: YA GAMU DA WATA LARURA
WANDA LIKITA YACE SAI ANYI MASA AIKI, AMMA
KAFIN ZUWAN RANAR AIKIN, DA YA DUMFARI SHA
RUWAN ZAMZAM, DA LOKACIN AIKIN YAYI, SAI AKA CE
BABU CUTAR YA WARKE, SILSILA
36 MAL IBNUL QAYYIM YA KAWO A CIKIN LITTAFIN SA. ZADUL MAAD, CEWA: YA GAMU DA LARURA A MACCA
YA RASA LIKITA, SAI YA DEBI RUWAN ZAMZAM YANA
KARANTA FATIHA YASHA, NAN TAKE YA WARKE.
DUBA WANNAN LITTAFIN DOMIN KARIN BAYANI
ﻒﻴﻟﺄﺗ ﻪﻟﻮﻟﺍﻭ ﺶﻫﺪﻟﺍ ﺔﻟﺍﺯﺇ
ﻱﺭﺩﺎﻘﻟﺍ ﺲﻳﺭﺩﺇ ﻦﺑ ﺪﻤﺤﻣ ﺶﻳﻭﺎﺸﻟﺍ ﺮﻴﻫﺯ ﻖﻴﻘﺤﺗ
ﻲﻧﺎﺒﻟﻷﺍ ﺦﻳﺮﺨﺘﺑ
37 AKWAI BINCIKE DA WATA CIBIYA TA KASAR TURE
TAYI AKAN ZAMZAM, DA FA'IDOJINSA A ZAMANANCE,
A DUBA WIKIPEDIA .

Friday, 23 December 2016

KA TABA YIN ZINA? |SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

KA TABA YIN ZINA ?

Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan
shariun da Allah taa'la ya saukar sun hadu akan
haramcin zina,
Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi saw, da
dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina, Kofofin zina guda biyar ne
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar da ba muharrama ba,
5- Shaawa Mai karfi babu aure Allah taala yace: " kada ku kusanci zina"
Manzon Allah saw yace : Mai zina ba zaiyi zina ba,
yayin da yake zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace : Duk Al'ummar da
take zina, ta jawo wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa biyar, sune : Addini, Dukiya, Rayuka, Hankali, Mutunci,
Nasaba, amma zina ita kadai, tana rusha wadannan
duka,
Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa,
mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku, shedu guda hudu, Mutun yayi ikirari da kansa, samun mace da
ciki, babu aure, ko shubha. Bisa sharudda da aka
sanyawa ko wanne.
Zina wata babbar musifa ce da bala'i da dukkan
sharri, da take ruguza al'umma, take wargaza iyali,
take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da
annoba, a cikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da
unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya
baki daya,
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun
dukkan sharri kamar : 1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci 7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa 13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa zina, wadanda suke yi Allah ya shirye su.

Wednesday, 21 December 2016

(mp3)sabuwar wakar Rararah buhariyya da masariyya nufin na gyara ne

Assalamu Alaikum warahamatullah yan uwana sadeeqmediaers barkada fatan kuna lapia 
a yau kuma nazo muku da waka ta shahararen mawakin siyaya wato Dauda kahuta Rarara da wata waka mai suna buhariyya da masariyya domin kayi download  sai kayi click here



Ayi sauraro lapia

Tuesday, 20 December 2016

FATAWAR RABON GADO (84)*| DR JAMILU ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (84)*

*Tambaya*
  Assalam dan Allah ya rabon gadon wanda ya mutu ya bar uwa da uba da mata da 'ya'ya maza da mata zai kasance ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, za'a raba gida 24, sai a bawa uwa kashi 4, uba kashi 4, matar kashi:3, ragowar kashi:13  sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
8/12/2016

HAKKOKI 35 NA MUSULMI AKAN DAN UWANSAMUSULMI.MUNA KULA KUWA? | SHEIK AMINU IBRAHIM DAURAWA

HAKKOKI 35 NA MUSULMI AKAN DAN UWANSA

MUSULMI.
MUNA KULA KUWA?

1 Yayi masa sallama idan sun hadu
2 Yayi masa murmushi da faraa
3, Ya mika masa hannu su gaisa
4, Idan ya kira shi ya amsa
5, Idan BASHI da lafiya yaje ya dubu shi.
6, Idan ana binsa bashi ya taimaka masa wajan
biya
7, Ya dinka kyautata atata masa zato
8, Ya zauna dashi lafiya.
9, Ya bashi abinci idan yana Jin yunwa.
10, Ya girmama dattijo musulmi
11, Ya tausawa yaro musulmi.
12, Ya cika masa alkawari idan sunyi alkawari.
13, Yayi masa sulhu Da wanda suka sami rashin
jituwa.
14, Kada ya dinka tuhumar musulmi.
15, Ya nema masa alfarma idan yana da wata
bukata
16, Ya dinka girmama malamai da masu Ilmi
17, Yayi masa addua idan yayi atshawa
18, Idan ya nemi agajinka ka agaza masa.
19, Ya dinka yi masa addua da fatan alkhairi.
20, Kada ya zalunce shi
21, Kada ya tabar dashi
22, Kada ya dinka yi masa hassada akan wata
niima da Allah yayi masa.
23, Ya girmama shi idan yazo masa a matsayin bako.
24, raka janaizar sa. Idan ya mutu.
25, Ya je kabarinsa domin ziyara da addua.
26, Ya so masa abinda yake sowa kansa
27, kada ya cuci musulmi
28, ya zama Mai tawadiu ga kowa. 29, kada yayi gulmar sa. Ko yayi masa
annamimanci
30, kada ya kaurace masa fiye da kwana uku.
31, Ya kyautatawa dan uwansa musulmi.
32, Kada ya shiga gidansa sai da izninsa
33, Ya umarceshi da kyakyawan halaye ya hanashi mummunan hali.
34, Kada yayi ciniki akan cikinsa.
35, Kada ya nemi aure akan auransa.
36. Kada ya dinka yi masa bincike da bin
diddiginsa.
37, ya kubutar dashi idan yayi rantsuwa.
38, Ya kiyayi mutunci da dukiya da jini na musulmi.

Monday, 19 December 2016

SHAWARWARI 50 KAN MATAR DA ZAKA AURA | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO


SHAWARWARI 50 KAN MATAR DA ZAKA AURA
SHAWARWARI 50 KAN MATAR DA ZAKA AURA

1 mai ya sa kayi aure

2 Ka zabi mai addini

3 Mai kaunar Ka

4 Mai haihuwa

5 Mai saukin hali 6 Mai Tarbiyya
7 Mai kamewa

8 Ka ni sanci mai hali 6 mai mita.mai gori. Mai hange
hange. Mai Kwadayi. Mai rainuwa.

9 Mai hakuri

10 Daidai da kai. 11 Ra'ayinku yazo daya

12 Ka binciki halayanta da kyau
13 Ka bayyana mata manufofinka.
14 karbar kaddara yadda tazo. Bayan kayi iya
yinka

15 kada kayiwa matar da zaka aura karya 16 Ka bincika lafiyar juna akawai ciyukan da ake
dauka.

17 Ka gane kuna da banbanci da matar Ka.

18 Ka dinka yiwa matar Ka kyautar ba zata.

19 idan tayi kwalliya ko girki Ka yaba mata.

20 Ka bata lokaci na hira da tattaunawa 

21 Ka dinka tafiya da ita lokaci Bayan lakaci.

22 Ka dinka jaddada soyayya da kalamai masu
dadi.

23 kada Ka kuskura Ka sabawa Allah Don Ka
farantawa matarka.

24 Ka zama mai juriya da shanye kananan matsaloli.

25 Ka ginka girmamma raayin matarka.

26 kada Ka zama mai kama karya
27 mace sai hakuri.
28 Ka dena kangama kananan abubuwa.

29 Ka dena gwasile matar Ka ko kushe ta . 

30 Ka kula da tsaftar kanka mata basason miji
kazami

31 kanka dinka ado da kwalliya
32 Banda cin Amanar aure.
33 Ka kiyayi saurin fushi
34 Banda duka da zagi da cin fuska 35 Ka dena lissafa abinda ya wuce
36 Ka zauna da matarka a matsayin miji kawai ba
malami ko mai kudi ko mai mulki ba.

37 Ka dauki aure a matsayin ibada.
38 kada Ka dinka auna rayuwar Ka ta aure da
wani. 

39 Ka dena gayawa mutane rayuwar Ka da
iyalanka.

40 Ka nisanci zargi sai da hujja mai karfi
41 kada Ka yankewa matar Ka hukunci da zato ko
jita jita

42 Ka dena gaggawar furta kalmar saki 

43 komai yana iya cangawa Don haka kada Ka
nunawa matarka rayuwa iri daya .

44 kada Ka zargi matarka akan wasu abubuwa da

suke faruwa. Wasu kaine dalilin faruwar su
45 kar Ka zama kullum kada gida Ka dinka basu
iska 

46 Munin alakar Ka da Allah tana shafar auranka .
47 kaba matarka hakuri idan Ka muzanta mata.

48 Ka dinka tausawa mata
49 Rayuwa jarrabawa ce. Ka lura da wannan

50 Ka yawaita zikri da addua da karatun Alkurani
mai girma.

FATAWAR RABON GADO (83) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (83)

Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullah wabarakatuh.
Malam inada tambaya ne ataimaka man da amsar ta don Allah, tambayar itace kan gado mutum ne ya rasu baiyi aureba yabar mahaifiya, da ya'ya mace uba daya, sai kanwa da suka hada uba daya, sai kannai maza da mata da suka hada uwa daya, to yaya gadon zai kasance. Allah yakara basira a huta lafiya.

Amsa :
Wa alaikum assalam,
Za'a raba abin da ya bari gida: 7, (Auli daga:6) sai a bawa Mahaifiyarsa kashi daya, 'yar'uwansa mata da suka hada uba daya kashi hudu, :4, 'yan'uwansa da suka hada uwa daya kawai kashi biyu.
'ya'yan uwa za su raba abin tsakaninsu, babu bambanci tsakanin namiji da mace.
Allah ne mafi sani.
5/12/2016
DR JAMILU ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (82)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (82)

Tambaya?
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Tambaya akan rabon gado.
Yaya Rabon gadon matar da ta mutu ta bar Mijinta, da uwatta da ubanta da kuma yan uwanta shakikai da li'abbai da li'ummai?
Allah ya bada ikon taimakawa.

Amsa :
Wa alaikum assalam,
Za'a raba abin da ta bari kashi shida, a bawa mijinta kashi uku, banbanta kashi biyu, mahaifiyarta kashi daya.
Allah ne mafi sani.
2/12/2016
DR JAMILU ZAREWA

Sunday, 18 December 2016

FATAWAR RABON GADO(81) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (81)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, malam  Tambaya ce dani dan Allah,, mahaifinmu  ne yarasu ya bar mata biyu kuma da ya'ya' guda 32, maza16 mata 16.yaya rabon gadon zai kasance?
*Amsa*
  Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida takwas, a bawa matansa kashi daya, ragowar kashi bakwan sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau RABON mata biyu.      
Allah ne mafi sani
12/11/2016
Amsawa
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*

KADAN DAGA DARAJOJIN ANNABI SAW(.40 ) |SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

KADAN DAGA DARAJOJIN ANNABI SAW(.40 )
1 SHINE SHUGABANNI YAN ADAM BAKI DAYA
2 SHINE MAI TUTAR YABO RANAR ALKIYAMA
3 SHINE WANDA TUN DAGA ANNABI ADAM SAW,
HAR ZUWA KASA SUNA KARKASHIN TUTAR SA
RANAR KIYAMA. 4 SHINE FARKON MAI NEMAN CETO
5 SHINE FARKON WANDA ZAA BAWA CETO.
6 SHINE AKA YAFE MASA ABINDA YA WUCE DA
ABINDA ZAIZO ( IDAN MA YAYI)
7 SHINE ALLAH YAYI RANTSUWA DA RAYUWAR SA
8 SHINE WANDA ALLAH TAALA BAYA KIRANSA DA SUNAN KAI TSAYE, (SAW) , SAI YA ANNABI YA
MANZO YA MAI LULLUBA
9 SHINE WANDA YA JINKIRTA ADDUAR SA CETO GA
AL'UMMAN SA RANAR ALKIYAMA
10 SHINE WANDA DUTSE YAKE YI MASA SALLAMA.
11 SHINE WANDA KUTUTTURAN DABINO YAYI KUKA SABODA RABUWA DA SHI.
12 SHINE WANDA RUWA YA FITO TA TSAKANIN
HANNUNSA.
13 SHINE WANDA AKA CIREWA WANI SAHABI IDO A
WAJAN YAKI YA MAYAR MASA NAN TAKE. KUMA YA
WARKE NAN TAKE .
14 SHINE WANDA YAFI KOWA KYAWUN HALITTA
15 SHINE WANDA YA FADI KOWA KYAWUN HALI
16 SHINE WANDA ZAA DOSA RANAR ALKIYAMA,
BAYA ANJE WAJAN KO WANNE ANNABI, YA BADA
UZRI
17 SHINE AKA AIKO GA DUK DUNIYA, AMMA SAURAN ANNABAWA GA AL'UMMAR SU KAWAI.
18 SHINE WANDA KASA ZATA FARA TSAGEWA YA
FITO RANAR ALKIYAMA.
19 SHINE WANDA MAI WASEELA DA FADEELA
20 SHINE MAI TAFKIN KAUSARA.
21 SHINE WANDA ZAI FARA SHIGA ALJANNAH DA AL'UMMAR SA.
22 SHINE WANDA MUTUM DUBU
70 ZASU SHIGA
ALJANNAH BABU HISABI DAGA AL'UMMAR SA.
23 SHINE LITTAFIN SA YAFI DUKKAN LITTAFIN DA
AKA SAUKAR.
24 SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL'UMMAR SA GANIMA BAYAN TA HARAMTA GA WADANDA SUKA
GABATA.
25 SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL'UMMAR SA
SUYI TAIMAMA DA KASA
26 SHINE WANDA AKA SANYAWA AL'UMMAR SA
KO'INA YA ZAMA MASALLACI IN BANDA MAQABARTA DA BANDAKI
27 SHINE WANDA AL'UMMAR SA TAZO A KASHE,
AMMA TAFI WADANDA SUKA GABATA DARAJA
28 SHINE WANDA YAYI ISRA'I DA MI'IRAJI HAR
SUKA YI MAGANA DA ALLAH TAALA, HAR YA KARBO
SALLAH 29 SHINE WANDA YAFI ANNABAWA YAWAN
MABIYA DA YAWAN LADA
30 SHINE WANDA AKA NINKAWA AL'UMMAR SA
AIKIN LADA DAYA, ZUWA GOMA
31 SHINE MU'UJIZAR SA BATA YANKEWA DA
WUCEWARSA
32 SHINE WANDA DUK YA BISHI ZAI SHIGA
ALJANNAH WANDA YA SABA MASA BAYA SO
33 SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALATI DAYA,
ALLAH ZAIYI MAKA GOMA.
34 SHINE WANDA ALLAH YA SANYA MAKULLAN
TASKOKIN KASA A HANNUNSA.
35 SHINE WANDA YAFI KOWA SAN ALLAH, KUMA
ALLAH YAFI SON SA.
36 SHINE WANDA SAI KAFI SON SA, FIYE DA
IYAYANKA, DA YA'YANKA, DA KANKA, DA DUK
DUNIYA BAKI DAYA.
37 SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALLAMA, ALLAH YAKE DAWO MASA DA RANSA YA AMSA MAKA
SALLAMAR KA.
38 SHINE WANDA AKA SIFFANTA AL'UMMAR SA DA
ADALCI DA SHEDAR DA ZASU YIWA ANNABAWA,
AKAN SUN ISAR DA SAKO.
39 SHINE WANDA AL'UMMAR SA BATA HADUWA AKAN BATA.
40 SHINE SAHIBUL MAKAMIL MAHMUD SAW.
ALLAH YA KARA MANA SON ANNABI DA BIYAYYA A
GARESHI.
ALLAH TSINEWA MASU TABA DARAJAR ANNABI
SAW.

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE
Shawarwari 60 ga matan aure domin samun
zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka,
kamar yadda muka Bawa maza suma shawara 60.
1.Ta rike masa amana,
2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon
Allah bane.
3. Ta kula da dukiyarsa
4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman
lafiya
5. TA girmama shi a gaban idansa
6. TA kare girmansa a bayan idansa
7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a
wajenta
8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane
awajenta
9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.
10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga
gareshi
11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .
12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi
13.Idan ya bata kadan taga yawansa
14.Idan ya bata da yawa tayi godiya
15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
16.Sai yayi bacci kafin tayi
17.Tayi hakuri idan yayi fushi
18 Tayi taushi idan yayi tsauri
19.Ta lallashe shi idan ya hasala
20.kada ta nuna raki a gabansa
21.kada tayi kuka alhali yana dariya
22.kada tayi dariya alhali yana kuka
23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu
24.kada ta matsa masa da bukatu
25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida
26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai
27.kada ta dinka kushe tsarinsa
28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta
29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta
30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau
31.Ta dinka boye abu mummuna
32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake
shi ya warware ta
33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina
34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa
35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki
36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya
37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako
38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu
39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin
da ya dawo
40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi
41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta
42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge
43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro
44.Tayi ado karshen iyawarta
45.Ta bayyana halaye masu kyau
46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai
47.Ta bayyana kanta a matsayin mace
48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta
50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so
51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata
mummuna
52.Ta yafe masa idan ya munana mata
53.Ta karbi uzurinsa
54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa
55.kada ta dau azumi sai ya sani. 56.kada ta fita daga gida sai ya sani.
57.Ta iya girki kala-kala.
58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.
59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.
60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai
Allah ya zaunar damu lafiya da iyalan mu.