WANDA YA GANNI A MAFARKI ZAI GANNI A FILI ! !
Tambaya:
Akramakallah shin akwai hadisin da ya tabbata daga manzon Allah(S.A.W) cewa yace '' man ra'ani fil manami fasayarani fil yaqza'' wato wanda ya ganni a mafarki to tabbas zai ganni a fili. To shin malam hakan tana yiwuwa, kuma har ma Annabin ya bada wata falala? Almajirinka daga Beli.

Amsa :
Dan'uwa wannan hadisi ne tabbatacce daga Annabi s.a.w, kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 6592
Dan'uwa wannan hadisi ne tabbatacce daga Annabi s.a.w, kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 6592
Saidai malamai sun yi sabani game da lafazin zai ganni a fili, wasu sun ce : ma'anarsa: zai gan shi ranar alkiyama da sifa ta musamman ,
wasu kuma sun ce zai gan shi a duniya, saidai wannan zancen yana da rauni sosai, tun da hadisi ya tabbata cewa annabawa suna cikin kabarinsu, wasu malaman kuma sun ce hadisin yana Magana ne akan wadanda suka zo a zamaninnsa, ma'ana duk wanda ya gan shi a mafarki, to zai hadu da shi.
Malamai suna cewa abin da ake nufi shi ne ka gan shi da siffofinsa wadanda suka tabbata a hadisi,
inda za ka gan shi bakikkirin ba gemu, ko da mafarkin ya nuna maka annabi ne to ba shi ba ne, tun da hakan ya sabawa siffarsa a hadisi, wannan ya sa idan mutum ya zo ya cewa :
Muhammad dan Siirin RA, ya ga Annabi s.a.w a mafarki yakan ce masa siffanta min shi, in ya fadi kamannin da suka sabawa hadisai, sai ya ce ba shi ka gani ba, an rawaito kwatankwacin haka daga Ibnu Abbas.
Ba'a karbar wani hukunci ko wata falala daga Annabi s.aw. a cikin mafarki,
saboda hakan yana nuna tawayar addini, tare da cewa aya ta uku a cikin suratul Ma'ida ta nuna cikar addini, tun fiye da shekara dubu .
Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba : Alminhaj na Nawawy 1/50 da kuma Fathul-bary 12/386.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment