July 2018 - NewsHausa NewsHausa: July 2018

Pages

LATEST POSTS

Monday, 30 July 2018

Kalli sabuwar motar Jaruma Amina Amal


 Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal kenan a wadannan hotunan nata inda take tsaye kusa da sabuwar motarta, muna tayata murna da fatan Allah ya tsare.


Thursday, 26 July 2018

Kalli zafafan hotunan Maryam Yahya

Kalli zafafan hotunan Maryam Yahya Muna yi mata fatan Alaheri





Kalli zafafan hotunan jaruma Rahma sadau Guda 5

zafafan hotunan jaruma Rahma sadau Munayi mata fatan alkairi




Wednesday, 25 July 2018

Bani da niyyar sake tsayawa takarar Sanata ( Kwankwaso ya gayawa Buhari )

Bani da niyyar sake tsayawa takarar Sanata ( Kwankwaso ya gayawa Buhari )

Tun bayan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da dan majalisa mai wakiltar al’ummar Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwso ne dai jama’a ke ta hasashen abubuwan da jiga jigan biyu suka tattauna.

Wannan tattauna tsakanin Buhari da Kwankwaso ta wakana ne a daren Litinin, 23 ga watan Yuli a gidan shugaba Buhari dake fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, inda shugaban APC da wasu gwamnonin jam’iyyar su hudu suka halarta.

Daily Nigerian ta ruwaito shugaba Buhari yayi nufin ganawa da Kwankwaso tare da sauran Sanatocin dake korafi tare da barazanar ficewa, amma sai gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru ya bashi shawarar ya gana da Kwankwaso a lokaci na daban shi kadai saboda muhimmancinsa.

Oshiomole ne ya fara bude taro, inda ya bayyana ma Buhari irin kokarin da yayi na lalamar Kwankwaso, tare da tabbatar da cigaba da zamansa a jam’yyar, bayan nan sai Buhari ya dauka, inda shima ya bayyana ma manufarsa na magance matsalar, tare da yi masa tayin cigaba da zama a jam’iyyar don sake taka takarar Sanata a zaben 2019.

“Zamu shiga tsakani a rikicinka da Ganduje, zamu kawo karshen wannan matsalar, don haka ba sai ka fita ba, musamman duba da irin gudunmuwar da ka bayar wajen kafa wannan jam’iyya.” Inji Buhari.

Sai dai a nasa jawabin, Kwankwaso ya bayyana kaduwarsa da yadda yake ganin kamar shugaba Buhari ya nuna bashi da masaniya game da hatsaniyar dake cikin jam’iyyar da kuma rikicinsa da Ganduje.

“Da farko dai kamar yadda na fada ma Oshiomole, bani da burin sake tsayawa takarar Sanata, bani bukatar sake komawa majalisar Dattawa, idan zaka tuna Ya Shugaban kasa, sau uku muna tattauna wannan batu, amma baka dauki wani mataki ba.” Inji Kwankwaso.

Duk kokarin da gwamonin dake wajen suka yin a tausar Kwankwaso tare da bashi hakuri, inda suka nuna masa matsayinsa a jam’iyyar da irin gudunmuwar da ya bayar, amma hakan ya ci tura, haka dai aka tashi baram baram, ba tare da wani tabbaci daga Kwankwaso ba akan ko zai zauna a jam’iyyar.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan zama akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na Borno, Kashim Shettima, na Ogun, Ibikunle Amosun, da na jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

Yawan saduwa da juna ta hanyar jima’I nau’i ne na tabuwar hankali – Inji WHO

Yawan saduwa da juna ta hanyar jima’I nau’i ne na tabuwar hankali – Inji WHO
Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa mutanen dake yawan son yin jima’I a kowani lokaci nau’i ne na samun tabuwar hankali. WHO ta bayyana cewa muddun mutum baya cin abincin da ya kamata sannan ya mai da yin jima’i rigar sawar sa wato kullum yana tare da mace to tabbas hakan zai kawo masa matsala a lafiyar sa sannan zai yi ta fadawa cikin hadarukkan kamuwa da cututtuka dabandaban.

Bayanai sun nuna cewa yin juma’i na gajiyar da mutum saboda haka domin gujewa irin hakan ya sa bayan an kammala saduwa da juna yake da kyau mace ko namiji ya/ta samu ta hutu tare da cin abincin dake gina jiki domin hakan ne zai inganta kiwon lafiyar mutum sannan ya kare ka da ga fadawa irin wannan matsala.

 WHO ta ce rashin kiyaye wadannan sharudda na jefa mutum ciki irin wannan nau’i na tabuwar hankali.

A yanzu dai kungiyar WHO ta ce yawan son yin jima’I a kowani lokaci matsala ce sai dai bata da tabbacin ko illar ta kai irin ta cha-cha ko ta shaye shayen miyagun kwayoyi. Duk da wannan bincike da WHO tayi akwai kuma ingantattun bayanai da suke nuna cewa saduwa da juna tsakanin namiji da mace na inganta lafiyar masoya.

Saduwa da zumman jima’i yakan kara wa namiji karfin mazakuta, sannan ya sawwake wa mutum matsanancin damuwa, kuma asamu barci mai nagarta. Bayan haka kuma a kan samu kariya daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, sannan yana rage kamuwa da cutar sankara da ciwon siga. A karshe kuma akwai bayanai da suka nuna hakan na ingantawa da kara dankon zumunci a tsakanin masoya da ma’aurata.

Tuesday, 24 July 2018

Abubuwan mamaki 10 game da jaruma Hadiza Gabon

Abubuwan mamaki 10 game da jaruma Hadiza Gabon
Danna kan Hoton dake kasa domin kallon Videon kai tsaye a YouTube channel din mu.

Kada ku manta idan kun shiga ku danna subscribed domin samin sabbin shirye shiryen mu


Monday, 23 July 2018

DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 63 AREWA24

DADIN KOWA SABON SALO EPISODE 63 AREWA24
Domin kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya wuce ku kasance damu domin kalla.
A Cikin wannan SatinYayin da Adama ta ci gaba da tsintarkanta a tsaka mai wuya, Bayan daKamaye ya iy mata korar kare daga gidansa a yanu ta faral aluben hanyar da zata bi domin ganin an sulhunta tsakaninsu sai dai yunkurin neman sulhun tana kokarin jefa kanta a cikin wata sabuwar sarkakiyar mai wuyar fita.

Danna hoton dake qasa domin kallon cigaban Shirin


kada ku manta ku danna subscribed domin sami sabbin shirye shiryen mu cikin sauki

Kalli Hotunan Manyan kyawawan Matan Kannywood Guda 5 Da Basu Da Aure Har Yanzu

Jerin Manyan Kyawawan Matan Kannywood Guda 5 Da Basu Da Aure Har Yanzu


Masana’antar Kannywood na da albarkattun kyawawa kuma kwararrun yan wasa mata da suka amsa sunansu na kyawawa.

Baya ga kyawu da wadannan mata ke da shi sun kasance masu kwazon aiki.
Munyi amfani da wannan dama wajen kawo maku kyawawan matan Kannywood da ke kasuwa har yanzu wato basu yi aure ba tukuna.

1. RAHAMA SADAU

Rahama Sadau ta kasance matashiya wacce aka Haifa a ranar 7 ga watan Disamba, 1992 a jihar Kaduna. Tana da digiri a fannin kasuwanci. Tana daya daga cikin shahararrun yan matan Kaannywood, wacce ta shahara tun bayan bayyanarta a wani fim mai suna “Gani ga wane”. A kullun jarumar na mafarkin kasancewa shahararriya kuma mafarkinta ya zama gaskiya.

2. HADIZA GABON

Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta kasance daya daga cikin matan Kannywood mafi kyau, tana da fuska mai matukar kyau da daukar hankali. An haifi Hadiza a ranar 1 ga watan Yuni 1989 a Libreville, a jumhuriyyar Gabon. Ta shaharane bayan ta fito a fim din Äli yaga Ali”.

3. NAFISAT ABDULLAHI

Nafisa ta kasance daya daga cikin kwararrun jarumai da ked a kwazon aik. An haife ta a ranar 23 ga watan Janairu a garin Jos, Jihar Plateau. Nafisa ta kasance kyakyawa. Ta shahara a fim dinta na farko a 2010 wato “Sai wata rana.”

4. FATIMA ABDULLAHI WASHA

Fatima Washa ta kasance kyakyawar jaruma da ta fito a fina-nai da dama ciki harda Rariya. An haifi jarumar mai taushi Magana a ranar 21 ga watan Fabrairu 1993.

5. HAFSAT IDRIS

Hafsat Idris wacce aka fi sani da sunan wani fim da ta fito wato ‘Barauniya’ ta kasance daya daga cikin hadaddun matan kannywood. An haife ta a garin Shagamu amma yarasalin jihar Kano ce.

Saturday, 21 July 2018

Kalli hotunan Maryam Yahaya da suka birge

Kalli hotunan Maryam Yahaya da suka birge

Jarumar fina-finan Hausa, me tashe, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da suka birge, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.



Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba

Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba
Malaman kimiyyar halitta a jami'ar Queensland ta kasar Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba.

Daya daga cikin malaman kimiyyar Bryan Fry ya ce sun je wani yanki don gudanar da bincike kan macizan da ke rayuwa a cikin teku inda suka samu wani maciji da ke rayuwa a karkashin kasakuma sun yi mamakin ganin sa.

Fry ya ce, sun gano macijin a tsibirin Cape York kuma yana kama da dangin macizai da ke rayuwa a karkashin kasa.

Masanan Kimiyyar halittar na tunanin jiragen ruwa ne suka turo macijin zuwa gabar teku.

Sun bayyana cewa, ba kasafai ake ganin irin wannan maciji ba.
trthausa.

Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haifeta

Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haife ta


Wata jaririya da aka haifa a jihar Texas ta kasar Amurka ta shigo Duniya da kafar dama inda ta samu aikin yi ranar da mahaifiyarta ta haifeta, iyayen wannan yarinya, Robert Griffin da mahaifiyarta,

Falon Griffin suna kan hanyarsune ta zuwa Asibiti sai Falon taji cewa tana bukatar shiga bandaki.

Mijin ya tsaya a kofar wani sananen gidan sayar da abinci me suna, Chick-Fil-A amma sun tashi aiki da yake cikin darene, haka dole ya kwankwasa musu suka bude, saboda matar tashi ta bayyana cewa abinda take ji, ba zata iya jira har sai sunje Asibitin ba, matar tashi ta shiga ban dakin gidan sayar da abincin.

Jiyo ihun Falon daga bandakin yasa Robert yayi gaggawar kaimata dauki, yana shiga sai yaga ai haihuwace zatayi, har kan jaririyar ya fara fitowa, kamar yanda ya bayyana a labarin daya bayar a shafinshi na Fcebook.

Robert yace ganin haka yasa ya tabbatar da cewa babu inda zasu iya zuwa daga nan, sai ya fara gaya mata maganganun kwarin gwiwa a haka har ta haihu a cikin bandakin, inda yayi amfani da rigarshi a matsayin zanin rike jaririyar, ya kuma lura cewa, cibiyar jaririyar ta nade mata wuya har sau biyu, anan ma yayi dabara a warware mata.

Ma'aikatan jiyya sun iso gurin daga baya sannan aka tafi da jaririyar da uwarta Asibiti, a wajan rubuta takardar haihuwarta, an rubuta sunan mahaifin nata Robert a matsayin wanda ya bayar da gudummuwa wajan haihuwarta.

Su kuwa gidan sayar da abincin wanda sanannene yayi alkawarin ba jaririyar abinci har tsawon rayuwarta sannan kuma da zarar takai shekaru 16 zai dauketa aiki.

2019: Wata mace ta sake kaddamar da takarar shugabancin kasa a Najeriya

2019: Wata mace ta sake kaddamar da takarar shugabancin kasa a Najeriya

Wata mace mai suna Mrs Eunice Atuejide, ta kaddamar ta da bukatar ta na tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2019 a karkashin jam'iyyar National Interest Party, a yayin da take jawabi ga magoya bayan a jiya a Abuja, tace Najeriya ta gaza cigaba ne saboda 'son kai na wasu tsiraru'.

Atuejide, wacce yar asalin jihar Enugu ne, tace kasar na bukatar shugabani wanda za su mayar da hankali wajen kawo cigaba a kasar da abinda kasar ta mallaka ba tare da nuna banbanci tsakanin mutane ba.

'Yar takarar mai shekaru 39 a duniya ta kuma bayyana cewa ba rashin ilimi, tsare-tsare ko shugabanci ne matsalar Najeriya ba, tace kawai shugabanin da muke dashi a yanzu galibu suna mayar da hankalinsu kan wasu mutane tsiraru ne.

shugaban rikon kwarya na jam'iyyar, Azeez Oladapo yace jam'iyyarsu ta mayar da hankali ne wajen zakulo matasa masu shekaru 21 zuwa 45 don basu damar rike madafan iko a kasar saboda samun cigaba a kasar.

Ashe tsohon shugaban kasar Libiya, Gaddafi na nan da ranshi be mutuba

Ashe tsohon shugaban kasar Libiya, Gaddafi na nan da ranshi be mutuba

Dan tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi, Saiful Islam ya fasa kwai game da batun wafatin gyatuminsa.

Kamar yadda wasu kafafan labaran kasar Ivory Coat suka rawaito,a watan da ya gabata, wata mata mai suna Zayraf Aya hafaffiyar kauyen Gaddafi ta bayyana cewa,tsohon shugaban kasar Libiya wanda aka ce an kashe a shekarar 2011, mahaifi ne na 'yarta, kuma da ransa,bai mutu.

Matar mai shekaru 35 da haifuwa ta ce Gaddafi na nan da ransa amma ya rasa kafa daya sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai masa, a lokacin aka nemi hambarar da mulkinsa.

Ta kara da cewa, a yanzu Gaddafi yana jinya amma da zaran ya samu lafiya zai koma kasarsa don ceto al'umarsa.

Da maneman labaran jaridun na Ivory Coast suka nemi ganawa da Saiful Islam sai ya ce da su,

"A hakikannin gaskiya a shekarar 2011, mahaifina ya jikkata, amma bai mutu ba,yanzu haka yana ci gaba da jinya.Ba zan taba gaya muku takaimaime inda yake ba,don gudun kar a cutar da shi.An mika mana mahaifinmu yayin da zuciyarsa ke ci gaba da bugawa,sai muka garzaya da shi asibiti a wani wuri na sirri, inda kawo yanzu yake ci gaba da jinya".

Milyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya, sun kalli bidiyon yadda aka yi wa Muammar Gaddafi kisan wulakanci.An yada bidiyon a shafukan intanet da na sada zumunta.Amma da yawa daga cikin 'yan adawan tsohon shugaban kasar Libiya,sun tabbatar da cewa wannan ba komai ba ne face farfagandar magoya bayan Gaddafi da nufin shafa musu kashin kaji.

Lokaci zuwa Lokaci iren iren wadannan labarai kan Muammar Gaddafi na kunno kai a wasu shafukan farko na jaridun nahiyar Afirka da ma kasashen Yamma,amma kawo yanzu babu wanda ya taba tabbatar da sahihancinsu.
Ayar tambaya a nan ita ce, shin da gaske ne Gaddafi na raye ?
TRThausa.

Kalli tsohon hoton Shugaban kasa Mohd Buhari tare da matar sa

Kalli tsohon hoton Shugaban kasa Mohd Buhari tare da matar sa
Kalli tsohon hoton mohd buhari tare da matar shi Aisha Buhari

Rangeela Jahilin Malami Fassarar Algaita Dub Studio 2018

Rangeela Jahilin Malami Fassarar Algaita Dub Studio 2018
.
Danna Rubutun Hoton Dake kasa domin kallon videon
.
kAda Ku manta ku danna SubscrSubscribe domin samin sabbin shirye shiryen mu
.

Please subscribed our channel 


Dadin Kowa Sabon Salo Episode 62 AREWA24


Dadin Kowa Sabon Salo Episode 62 AREWA24
Dadin Kowa Sabon Salo Episode 62 AREWA24 
Kada Ku manta kuyi subscribed domin samin sabbin shirye shirye.

Wednesday, 18 July 2018

Kalli hotunan Fati Shu'uma da suka birge

Kalli hotunan Fati Shu'uma da suka birge

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Shu'uma kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.



Kalli wasu kayatattun hotunan Hadiza Gabo

Kalli wasu kayatattun hotunan Hadiza Gabo

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, tasha kyaiu, muna mata fatan Alheri.