Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba - NewsHausa NewsHausa: Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba

Pages

LATEST POSTS

Saturday 21 July 2018

Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba

Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba
Malaman kimiyyar halitta a jami'ar Queensland ta kasar Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba.

Daya daga cikin malaman kimiyyar Bryan Fry ya ce sun je wani yanki don gudanar da bincike kan macizan da ke rayuwa a cikin teku inda suka samu wani maciji da ke rayuwa a karkashin kasakuma sun yi mamakin ganin sa.

Fry ya ce, sun gano macijin a tsibirin Cape York kuma yana kama da dangin macizai da ke rayuwa a karkashin kasa.

Masanan Kimiyyar halittar na tunanin jiragen ruwa ne suka turo macijin zuwa gabar teku.

Sun bayyana cewa, ba kasafai ake ganin irin wannan maciji ba.
trthausa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment