NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Tuesday, 4 October 2016

lαвαrí dα dumí dumínѕα:вuhαrí чα ѕα jírgín ѕαmα gudα вíчu α kαѕα

Ina masu bukatan siyan Jirgin sama - BUHARI ya sa nasa guda biyu a kasuwa.
Fadar shugaban Kasa ta sanar da sa jiragen saman shugaban kasa guda biyu a kasuwa.
Jiragen wanda suna daga cikin 10 da ofishin shugaban kasar ya ke amfani da su sun hada da Falcon 7x da Hawker 4000.
Me za kuce akan hakan

Za a kaddamar da sabon kwamiti nazarin zabe a Najeriya

A wannan talatar ake saran kaddamar da wani sabon kwamiti a Najeriya da zai yi nazari kan dokokin zaben kasar ya kuma bada shawara kan yadda za a inganta su dan samun zabe mai sahihanci a kasar.
Kwamitin zai yi aiki ne a karkashin tsohon shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ken Nnamani.
Wannan dai ba shine karo na farko ba da ake kaddamar da irin wannan kwamiti, ganin na Justice Mohammed Lawal Uwais da ya yi irin wannan aikin bada dadewa ba.

Monday, 3 October 2016

(MP3)ALBUM ALFANDA GAMJI NA SARDAUNA BY AMINU ALAN WAKA

BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
ASSALAMU ALAIKUMU WARAHAMATULLAH
Barka da asuba da fatan kowa ya tashi lapia
a yau sadeeqmedia taxo muku da wakokin shahararen gwarzon mawakin nan wato AMINU ALA wanda yayi wa mazan jiya ,wadanda suka nemo muna incin arewa da kuma Nigeria wato
domin ka saukar da wanannan wakokin sai da danna duk inda kaga /kiga sunan wako mai dauke da kalar rubutu blue
  direct download
     click here
         
    ALFANDA
SIR AHMADU BELLO SARDAUNA OF SOKOTO
         click here
               
BURATAI ARMY STAFF
                click here
                    
PREMIER NA AREWA SARDAUNA
                 click here
                      
TAMBARI  ALFANDA
             click here
                  
GAMJI MAZAN JIYA
  
ENJOY
ku kasance da sadeeqmedia a ko wane lokaci
daga dan uwanku Abubakar Rabiu Yari

FATAWAR RABON GADO (60)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (60)
tambaya
Assalamu akaikum. Malam mutum ne ya mutu ya bar mahaifiyarsa da 'yar'uwarsa shakikiya da kuma 'yan' uwansa li'ummai ?
Amsa
Wa alaikumus salam za'a raba abinda ya bari 12, abawa mahaifiyarsa kashi biyu, 'yan'uwarsa kashi:6, 'yan'uwansa li' ummai a ba su kashi: 4
Allah ne mafi sani

Amsawa Dr jamilu zarewa.

Sunday, 2 October 2016

BREAKING :AN KORI RAHAMA SADAU DAGA MASANA'ANTAR FIM

AN KORI RAHAMA SADAU DAGA MASANA'ANTAR FIM
A yau ne Kungiyar masu shirya Fina-finan hausa mai suna (MOPPAN) ta kori jaruma Rahama Sadau daga harkar Fim kwata-kwata, sakamakon wata wakar bidiyo da ta yi da wani mawakin Turanci mai suna Classiq. Wakar da ta jawo cece-kuce wurin al'umma. Har ta kai ga wasu daga cikin jaruman masan'anatar ta Kannywood sun fito fili karara suna goyon bayan a hukunta ta bisa laifin da ta aikata.
A da zu ne dai kungiyar ta zartar da hukuncin karkashin jagorancin shugabannin kungiyar kamar yadda sakataren kungiyar Moppan Salisu Muhammad officer ya sanar. A cewar sa Rahama ta taka doka shi ya sa suka kore ta daga harkar fim kwata-kwata. Sannan yace akwai amincewar sauran kwamitocin da ke karkashin kungiyar ta Moppan kafin Su zartar da hukuncin.
KARIN BAYANI: Sai dai manzarta da masu lura da al'amurran yau da kullum na masana'antar ta Kannywood suna ganin wannan hukuncin dai dai yake da kwance igiyar goro. Wargajewa zai yi ba zai yi tasiri ba. Saboda In dai ba a manta ba a ranar 4th ga watan mayu na shekara da ta gabata 2015 an taba dakatar da jarumar daga harkar Fim na tsawon Wata shida. In da a wancan lokacin wasu daga cikin furodusoshi da daraktoci su kayi fatali da hukuncin sannan suka ci gaba da sanyata a fina-finansu. Kuma suka ci bulus.
A gefe guda wasu kuma suna ganin babu adalci kan dakatarwar da aka yi jarumar saboda akwai wadanda suka yi abinda ya fi na ta muni kuma hotunansu su ma sunyi yawo kamar wutar bazara. Amma aka zuba masu ido ba tare da an dauki mataki akan su ba.
Yanzu haka dai kura naci gaba da tashi a industiri dangane da korar da aka yi wa Rahama sadau Inda wasu suke ganin hukuncin da aka yanke mata ya yi dai. Wasu kuma suna ganin kwata-kwata ba ayi mata adalci ba.
Madogara: Kannywood Exclusive Instgram Page.

‘Yar wasar Kannywood Rahma Sadau zata fuskanci takunkumi

– Za’a sanya ma Rahma Sadau takunkumi
– Rahma Sadau tayi abin kunya a
sabuwar bidiyon ta da wani mawaki
– Wannan abu ya jawo cece-kuce cikin
al’umma
Yan wasan kwaikwayon Kannywood na kungiyar Motion Pictures Association of Nigeria na wata ganawa domin zantar da ukuba akan yar wasa, Rahma Sadau, akan wata bidiyon wakan da ta yi wanda ya tada kura a cikin al’umma.
Rahama Sadau haifaffoyar yar jihar Kaduna ce amma tayi rijista da kungiyar yan wasan kwaikwayon jihar Kano.
Wannan abu na faruwa ne lokacin da ake tuhumar yan kamfanin Kannywood da rashin halin kirki da kuma kunya ta al’adan hausawa wanda yayi sanadiyar da’awar Malamai a jihar Kano na haramta yin Alkaryan Fim a jihar Kano.
ku kαѕαncє dα ѕαdєєqmєdíα.ml dσmín kαwσ muku cíkαkkєn lαвαrí αkαn чαddα kαrѕhєn αвun zαí kαчαh

Saturday, 1 October 2016

yadda zakka more free browsing AIRTEL,GLO,ETISALAT WITH TWEAK KIT

BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
barka da zuwa wanannan dandali mai albarka a yau nazo muku da yadda zaka more free browning
wanda wananna wani applicatuon ne mai suna tweak kit wanda zakayi amfani da shi wajen free browsing da etisalat,glo and airtel
ka danna nan domin kayi download din wanannan application
zaka iya amfani da hada
√ free glo 0.00k
√free etisalat 0.00k
√1.20GB AIRTEL AS N300
ALLAH YA BADA SA'A