NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Thursday, 10 August 2017

Tir ! Banji Dadin Abinda Kunayi Yimin Ba ! Cewar Shahararen Jarumin Kannywood Ali Nuhu

Biyo bayan wallafa wani labari a shafin Hausa Times mai taken an kama Ali Nuhu da makamai jarumin ya maida martani.
Jarumin ya sanya hotonsa da yan sanda da makamai a zube gabansa wanda hakan ya jawo ra’ayoyi daban-daban a shafinsa.
Hausa times ta dauki hoton a inda ta wallafa sai dai jama’a sunyi masa gurguwar fahimta wanda hakan bai yiwa jarumin dadi ba.
Bayan tattaunawa Hausa times ta baiwa jarumin hakuri tare da daukar mataki akai.
Kodayake dai ba yaune farau ba, akan tallata fina-finai da karawa tauraruwar jaruman fina-finan haske.
Ko a baya BBC ta wallafa wani labari mai taken anyi garkuwa da jaruma Rahama sadau domin tallata wani fim dinta.
Sai dai ganin yadda sakon ya jawo cece kuce jarumin ya aikewa Hausa Times aikakken sako yana nuna rashin jin dadinsa yana mai cewa “kunyi kuskure” a inda Hausa times ta bashi hakuri.
Jarumai sukan wallafa hotuna wanda ke barin masoyansu cikin zullumi da wasa kwakwalwa misali Hotunan jarumi Sani Danja da sojoji sunyi masa jina-jina da hoton jaruma Nafisat anyi mata aski da dai sauransu.
Kawo yanzu dai masoyan jarumin ya bar hoton a shafinsa a inda masoya keta tafka muhawara.
Daga Hausa Times

Wednesday, 9 August 2017

Kaf Kannywood Ba Mai Kyan Fati Muhammad

Kaf Kannywood Ba  Mai Kyan Fati Muhammad 

Ra'ayin Aliyu Ahmad

Yarda ko kada ka yarda a tarihin Kannywood ba a taba mai kyau da shaharar Fati Muhammad ba.

Kalli hotuna kamar haka






Ku kasance da www.hausaloaded.com a ko da yaushe

Tuesday, 1 August 2017

Bamu Da Masaniyar Dawowar Shugaban Kasa A Yau, Cewar Masu Magana Da Yawun Shugaban Kasa.



Biyo bayan wasu rahotanni da suka mamaye kafafen sadarwar zamani a daren jiya, kan batun dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren jiya ko safiyar yau Laraba, sashin watsa labarai na fadar shugaban kasa sun ce basu da masaniya kan wannan batu.

Batun dawowar shugaban kasar dai ya zafafa ne bayan rahotannin da aka samu na cewar jirgin dake jiran shugaban kasa wacce kwanaki baya aka dauko hoton ta a filin fakin na filin saman birnin London ta tashi zuwa Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce shi bashi da masaniya akan wannan rahoto. Haka zalika shima Femi Adesina ya ce idan har shugaban kasa zai dawo ana sanar dasu, amma izuwa yanzu basu da wani rahoto dangane da batun.

Yanzu dai ta tabbata cewar babu wani ingantaccen bayani kan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a yau Laraba

Yadda na ji rauni a fim din Dakin Amarya —Aisha Tsamiya



Aisha TsamiyaHakkin mallakar hotoAISHA TSAMIYA
Image captionAisha ta ce tana daukar fim a matsayin sana'a

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa BBC cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar "Dakin Amarya".
Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama - ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.
"Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin. Kai har kwanciya na yi a asibiti", in ji Aisha Tsamiya, a hirar da ta yi da Nasidi Adamu Yahaya.
A cewarta, "Na dauki yin fim a matsayin sana'a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa."


Aisha Tsamiya da Ali NuhuHakkin mallakar hotoYOUTUBE
Image captionAisha Tsamiya ta ce tana jin dadin yin fim da kowane dan wasa

Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta "kuma ina zaune da kowannensu lafiya".
"Jarumai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni", in ji Aisha Aliyu.
Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.
Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.


Halima Atete

Hakkin mallakar hotoYOUTUBE
Image captionHalima Atete ce uwar gida a fim din "Dakin Amarya"
© bbhausa.com

Duk wanda ya kara cewa na ciwo HIV Allah ya isa – Zainab Indomie




Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina finan Hausa wadda tauraruwar ta ta dan kwanta watau Zainab Indomie ta ce duk wanda ya kara cewa tana fama da ciwon kanjamau Allah ya isa.

Jarumar wadda a kwanan bayanan nan hotunan ta suka rika yawo ta rame ta tsomale bayan ta sha fama da matsananciyar rashin lafiya mai tsawo.

Hausaloadedblog dai ta samu labarin cewa alokuttan bayan dai da jarumar Zainab Indomie bata da lafiya mutane da dama musamman yan masana’antar fim din sunyi ta tofa albarkacin bakinsu akan rashin lafiyar tata.

Wasu daga cikin jaruman suna tsogumin cewa kanjamau AIDS ko HIV Zainab ta jajibowa kanta wasu kuma suka ce asiri sababbin jarumai mata suka yi mata.

Ba Fim ba ko Aure ne A Gabana ba ,Karatu ne A Gabana Inji Aisha Aliyu Tsamiya



Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya ta fito fili ta sanarwa duniya sirri da burin cikin ranta, wanda ya yi daidai da ra’ayinta. Jarumar ta bayyanawa jaridar Premium Time cewa, ita yanzu karatune agaban ta ba fim ko aure ba.
Domin wannan shine kudirinta.
Tabbas, bani da niyar yin aure yanzu, duk da nasan hakane ya dace da ni.

Kuma bawai ina nufin natsani aure ko bazan aure ba, a’a, ina nufin a yanzu karatune agabana ba aure ko fim ba. Wannan shine yanayin yanda na tsara rayuwata.
Amma kuma, bance dole sai hakan tafaru ba, Allah yanayin duk abinda yaso.
Idan baiso ba ko karatun ba zanyi ba.
Ni dai kawai na fadi ra’ayinane, kuma kowa yana da yanda ya tsara rayuwarsa. Inji Aisha Tsamiya.
Jarumar taci gaba da karatu ajami’ar A.B.U Zaria. domin yin degree Political Science.

Takaittacen Tarihin Jaruma Hadiza Gabon


Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da “Hadiza Gabon” wata Jaruma ce a masana’antar fina finan Hausa na Kannywood a Najeriya. An haifi Jaruma Hadiza Gabon a ranar 1 ga watan Yuni na shekara ta alif dari tara da tamanin da tara (1 June 1989) a garin Libreville nakasar Gabon.

Yawan chin mutanen kannywood da ma wajen ta baki daya kan kalli Hadiza Gabon a matsayin “Sarauniyar Mata”. Ta kasance mace mai kamun kai a masana’antar gami da girmama na gaba da ita. Bugu da kari ba’a taba samun ta da wani ashararanci ba irin wanda akan zargi fitattun Jarumai mata da shi.
Hadiza kan yi shiga irin ta mata a addinance. Sannan kuma bata nuna al’aurar ta a waje. Wajen tafiyar ta al’amura kuwa na rayuwa, Hadiza Gabon ba’a bar ta a baya ba, inda shima ta kasance daya tilo.
Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo masu yawa a masana’antar Kannywood. Sannan ta kasance Jakadiya ta kamfanin MTN a Najeriya. Bugu da kari ta kasance mace ta farko da ke tafiyar da gidauniya mai zaman kanta a masana’antar Kannywood mai suna Gidauniyar HAG (HAG Foundation) wanda kan bayar da tallafi ga yara kanana da mata marasa galihu a fannin ilimi, ciyarwa, lafiya da dai sauran su.

Kuruchiyar Rayuwar Gida Data Yan Uwa
Jaruma Gabon haifaffiyar garin Libreville ce na kasar Jamhuriyar Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu ya kasance dattijo dan asalin Gabon. Ta bangaren mahaifiyar ta kuwa ta kasance Bafulatana daga jihar Adamawa a kasar Najeriya. Tayi karatun piramare gami da sakandare a kasar Gabon inda tayi jarrabawar gaba da sakandare da sha’awar zama lawya inda ta fara karatun digirin ta na farko a kan fannin lauyanci. Hadiza ta fice daga neman ilimin lawyanci a shekarar farko saboda wadansu dalilai da suka hana ta cigaba. Amma daga bisani ta samu kammala karatun difloma a harshen Faransanci wanda kuma hakan ya bata damar koyarwa a wata makaranta cikin harshen na Faransanci.
Hadiza Gabon na da ‘yan uwa wadan da suka hada da Malam Aliyu (mahaifi), Hajiya Halima (mahaifiya), Muhammad Umar (dan uwa), Aisha Umar (dan uwa), Zakari Ali (dan uwa), Issa Ali (dan uwa), Hamidou Ali (dan uwa), Hachimu Ali (dan uwa),Muhammad Ali (dan uwa), Dahirou Ali (dan uwa) da kumaAdam Ali (dan uwa).
Kasancewa Jaruma
Hadiza Gabon ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood a yayin da ta shiga garin Kaduna daga jihar Adamawa bayan samun sha’awa da tayi a citin masana’antar ta Kannywood tare da wata ‘yar uwarta. A wannan lokaci ne ta samu haduwa da Jarumi Ali Nuhu inda ta nemi taimakon sa gami da hadin kai domin zama Jaruma. Hadiza ta samu fita a shirin fim ta farko a rayuwar ta a cikin fim din Artabu a shekara ta 2009.

Lambar Yabo
Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo dana girma kala kala a masana’antar Kannywood. Ciki harda Fitacciyar Jaruma a masana’antar Nollywood a shekara ta 2013 a fim din ‘Babban Zaure’ da kuma Jaruma a taron ban girma na biyu a masana’antar Kannywood wanda akayi a shekarar 2014 a fim din ‘Daga Ni Sai Ke’. Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso shima ya samu baiwa Jaruma Hadiza Gabon lambar yabo a shekara ta 2013.
Jaruma Hadiza Gabon ta dauki lambar girmamawa daga Kannywood AWA 24 Film & Merit Award a shekarar 2015 a fim din ta na ‘Ali Yaga Ali’. Sai kuma taron African Hollywood Awards shima data samu na fitacciyar Jaruma a shekara ta 2016 a fina finan Hausa na nahiyar Africa a cikin yaren Hausa.
Hukumar Gidan Malamai da aka fi sani da Kano State Senior Secondary Schools Management
Board ita ma ta samu karrama Hadiza Aliyu Gabon a shekara ta 2016 a bisa gudummawar da ta kam bawa ilimi a Jihar Kano karkashin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sai kungiyar Start Up Kano ina ta karrama Hadiza a shekara ta 2016 a bisa babbar gudummawa akan bayar da jari ga marasa aikin yi.
Aikin Gidauniyya
Hadiza Gabon ta fara aikin kafa gidauniya a shekara ta 2015 wanda kuma a cikin shekara ta 2016 tayi mata ragista. Gidauniya mai suna HAG Foundation anyi ta ne domin tallafawa mata da kananan yara marasa galihu a fannin ilimi, lafiya da abinci. Hadiza Gabon ta kasance mace ta farko a masana’antar Kannywood da ta fara bayar da irin wannan gudunmawa.
A watan Maris na 2016, Hadiza Gabon ta ziyarci gidan ‘yan gudun hijira a Jihar Kano wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa dasu inda ta raba kayayyaki da suka hada da kayan abinci da sutura dama sauran ababan more rayuwa.