NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 8 August 2018

Kalli yanda akai ma Rabiu Rikadawa kwalliyar mata

Kalli yanda akawa Rabiu Rika yanda akawa Rabiu Rikadawa kwalliyar mata

Tauraron fina-finan Hausa, Rabiu Rikadawa kenan  a wadannan hotunan inda aka mai kwalliya irin ta mata a cikin wani shirin fim da ya fito, da yawan mutane basu ganeshi ba a kallo na farko.




Kalli Yadda Wata Amarya Ta Yanke Al'Aurar Mijin ta Da Hakorin ta

Ta cizge al-aurar mijinta da hakori bayan da ya kamata da farkanta
'Yan sandan kasar Indiya sun cafke wata mace da ta yanke al'aurar mijinta tare da aran na kare da farkanta.

A cewar labarin da kafar AFP ta rawaito,a ranar 30 ga watan Yulin bana,a garin Vellore na yankin Tamil Nadu, wata mace mai suna Jayanthi mai shekaru 45 da haifuwa da mijinta, sun yanke shawarar zuwa gidan kallon wasan kwaikwayo,inda daga bisani ta sulale don ganawa da farkanta.

Bayan minti 30, sai maigidan ya dukufa neman ta.Can bayan wani lokaci sai ya yi kacibus da ita da farkanta a wani lambu.Nan take fada ya barke.

Yayin da ake fafata rikici tsakani mai gida da farka, wandon mijin Jayanthi ya fadi kasa.Abinda yasa ta yi hanzari ta saka baki ta guntsire al'aurarsa tare da aran na kare da farkanta.

Mutanen garin Nadu sun garzaya da mijin wanda jinin jikinsa ke ci gaba da malala,zuwa asibiti mafi kusa.

An cafke matar a ranar 1 ga watan Agustan da ya gabata,mijin kuma ana ci gaba da
jinyar sa a asibiti,inji helkwatar 'yan sanda.
A cewar jaridar The Times ta India,an garkame Jayanthi wacce ta karbi laifinta a kurkukun mata na Vellore.
TRThausa.

Tuesday, 7 August 2018

'Yar fim din Hausa ta fito neman takarar gwamnan Kano

'Yar fim din Hausa ta fito neman takarar gwamnan Kano

A karin farko, a zaben shekarar 2019, an samu jarumar fina-finan Hausa, Maryam Isah Abubakar ta fito ta bayyana ra'ayinta na tsayawa takarar gwamnan jihar Kano karkashin wata jam'iyya me suna RP.

Maryam dince da kanta ta wallafa wadannan hotunan dake dauke da bayanin tsayawar takarar ta ta.

Saidai bata yi wani cikakken bayani akan wannan lamariba

Monday, 6 August 2018

Kalli Zafafan Hotunan Jaruma Fati Washa Wanda suka Birge


Wannan wasu sababbin hotunan jaruma fati washa ne da ke yawo a shafin sada zumunta a instagram wanda sun dauki hankalin mutane sosai.






Sunday, 5 August 2018

Alamomi guda 10 da zaki gane mace 'yar madigo

Alamomi guda 10 da zaki gane mace 'yar madigo

A makon da ya gabata mun fara tabo batun bala’in da wasu mata ke jefa kansu a ciki ta dibi’ar madigo inda muka yi shimfida kan masifun da abin ke jawowa da kuma yadda ake bata wa iyaye yara ta hanyar jefa su a muguwar dabi’ar bayan sun ba su kyakkyawar tarbiyya. A wannan makon ma har yanzu dai muna kan maganar ta mata ‘yan madigo. Hakika duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan jarabawa ta madigo to tana cikin fitinar rayuwa, ita kanta ba wai don tana jin dadin samun kanta a ciki ba ne, domin da yawansu sun san wannan abu ba abu ne me kyau ba ta kowacce fuska. Yana da kyau iyaye mu kula da rayuwar yaranmu mata don guje wa fadawa ire-iren wannan dabi’ar. A duk lokacin da uwa ta fahimci yarinyar ta tana da kawa da suke yawan ziyartar juna, to ta yi kokari ta yi bincike sosai. Ko ta gan ta da sabon wani abu da ta san ba ita ta saya mata ba ta binciket a inda ta samo, saboda wacce duk ke son rinjayar yarinyarta to tana iya mata kyauta ta bajinta. Alamomi Da Ake Gane Mace ‘Yar Madigo: Akwai alamomi masu tarin yawa wanda ake gani da ma wanda sai su kadai suke gane kansu. Kadan daga cikin wanda muke gani a zahiri sun hada da : 1. Suna da son yin kyauta ta bajinta ga mata musamman wadanda suka gani suna so. 2: Suna da mugun son yin dinkin riga matsattse me bayyana nononsu.

3: Idan sun hadu da wacce ta yi musu sun dinga yi ma ta farin ido wurin yi mata magana kenan don son jawo ra’ayinta. 4: Suna da son yabawa structure (kyan diri) na mace musamman wacce suke son jan ra’ayinta. 5: Sun fi koda kyau na mace fiye da namiji 6: Suna da mummunan kishi 7: Ba su damu da yin mu’amala da maza ba, kullum sun fi son su rabi mace cikin nuna sha’awa. 8: Suna da son kyalli da tsabta ta fitar hankali. 9: Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka. 10: Suna son saka sarka a kakarsu da zobe a yatsar kafar, duk da yanzu kusan an mayar da yin hakan gaye amma nasu na musamman ne.

Wadannan su ne kadan daga cikin alamomin da za a iya gane ‘yan madigo da su, amma ba su kenan ba. Kamar yadda na fadi a sama, akwai wasu alamomin da sai su da ke cikin muguwar dabi’ar ke iya ganewa ko kuma idan an yi la’akari da abubuwan da suke aikatawa da zarar sun hadu a tsakaninsu.

Iyaye sai mu kula a duk lokacin da muka ga wata alama makamanciyar wadannan ga yaranmu ko wacce ke mu’amala da yaranmu mata sai mu yi kokari mu yi wa tufkar hanci. A karshe wadanda suka samu kansu cikin wannan ibtila’i ta madigo muna yi musu addu’a da fatan nan gaba Ubangiji ya yaye musu ya raba su da ita, Allah ya shirya mu, ya tsare mu da sharrin mutanen zamanin namu, amin. . Copyright @Leadershipayau

A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai

A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai
A kwanakin bayane, cikin watan Azumin Ramadana, jarumar fina-finan Hausa,

Amina Amal ta taba saka wannan hoton nata a dandalinta na sada zumunta da muhawara, hoton ya jawo cece-kuce sosai inda da dama, ciki hadda wasu daga cikin masana'antar fim din hausa ta Kannywood suka yi Allah wadai dashi.

A wancan lokaci, Amina ta kare kanta inda tace tana kan wani aikine da aka bata.
A karo na biyu, jarumar ta sake saka wannan hoto a dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa tuna bayane.

Wannan karin ma mutane basu kyale ba, da dama sunyi Allah wadai dashi.

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton kamar haka:




Thursday, 2 August 2018

Kalli wasu zafafan hotunan Zainab Indomie

Kalli wasu zafafan hotunan Zainab Indomie

Adam A. Zango na ci gaba da wallafa hotunan abokiyar aikinshi, Zainab Indomie a dandalinshi na sada zumunta inda a jiya yace yana taimaka matane saboda duk sauran wanda suka moreta sun yi watsi da ita, shine kadai ya rage mata a masana'antar.

A nan ma wasu hotunan nata ne da Adamun ya wallafa.