February 2017 - NewsHausa NewsHausa: February 2017

Pages

LATEST POSTS

Tuesday, 28 February 2017

Wahayin Shedan - Sheikh Yusuf Ahmad Tijjani Guruntum

Wahayin  Shedan !!!

Wannan itace makarantar shedan, Ga fatawoyin da almajiransa suka gabatar masa tare da abinda ya cusa musu na jayayya Don kange mutane daga daukar gaskiya:

Almajirai: Shin yaushe ya kamata a tsaida gemu???

Shedan:    Ana tsaida gemu ne in an tsufa, domin kar ka tsayar da shi ka kasa bashi hakkinsa.

Almajirai: Shin dole Mata su sanya Lullubi? 

Shaidan: Ai dayawa masu sanyawar suna fakewa da shi suyi barna,  Tsoron Allah Ai a Zuciya ya ke ba a Hijabi ba,  In sun matsa da bayanai Ku sanya Please call me,  ko Half Sunnah.

Almajirai : Yaya za a samu nasara kan Masu Da'awah. 

Shaidan: Ku cire musu yi Don Allah,  ku sanya musu son burge Jama'a,  Ku rabasu da yawaita Ibada Sannan Ku cusa musu son Duniya, in kuka ci nasara makamansu na yakar rundunata zai yi rauni. 

Almajirai:   Shin yabon manzon Allah da  kida halal ne??

Shedan:      Kwarai da gaske, An rawaito a rarraunan Hadisin karya cewa lokacin Hijira an  taryeshi da kida tare da 'yammata suna rawa suna juyi, Wannan salon yana daurin sanya nishadi. 

Almajirai:   Wanda ya bar tufarsa ta wuce idon sau ba don girma kai ba yayi laifi?

Shedan:      Tsoron Allah ai a zuciya ya ke ba wai a tufa ba, Annabi yace Abubakar ba ya cikin masu girman kai, In ka sanya tazarce ne kadai za ka fito dan Birni, domin irin Wannan shiga ta kan sanya a yi maka kallon dan tsanani. 

Almajirai:  Menene matsayin wanda yake satar kudin Gwamnati amma yana sadaka?

Shedan:   In baku sata ba 'yan kudu za su sata!! Kuma ai sadaka tana tsarkake Dukiya! sannan ai taimakawa Jama'ar ake yi. Ki gina Masallatai Ku taimakawa kungiyoyin addini laifukan za su karanta. 

Almajirai: In muka isar da sakon sai aka kawo mana wasu hujjoji yaya zamu yi??

Shedan:  Ku kalato rubabbun dalilai, ku kaucewa gaskiya, Ku tuhumcesu da kin Manzon Allah,  Ku ce musu 'yan tsanani, Ku jajirce kan matsayinku sannan kuyi tawilin gangan,  ku tuhumcesu da wasu karerayi sannan ku jirani in karo muku Hujja.

Allah yace cikin Qur'ani "Shaidan ya kan yi wa

Saturday, 25 February 2017

Fatawar Rabon Gadon (100) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Fatawar Rabon Gado (100)

Tambaya? 

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu,  tambaya ita ce yaya za'a raba gadon budurwa wacce ba tayi aure ba, ba uwa da uba sai Yan'uwa da uwansu daya, maza 3 da mata 3, sai kuma wanda ubansu 1, mata 4, da maza 3?                                                   Dan Allah malam a taimaka bukatar hakan ya taso ne. 

Amsa
Wa alaikum assalam
Za'a raba abin da ta bari gida uku: a bawa 'yan'uwan da suka hada uwa kawai kashi daya, su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da mace, ragowar kashi biyun kuma sai a bawa 'yan'uba su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

 Allah ne mafi sani

22/2/2017 

Dr Jamilu Zarewa

Friday, 24 February 2017

Riya Da Sunan Neman Addu'a :A Yi Hattara!!! - Dr Sheikh MuhamMuhammad Sani Umar R/Lemo

Riya Da Sunan Neman Addu’a: A Yi Hattara!

Magabata na kwarai na farko, kowane daya daga cikinsu ya kasance mai yawan kaffa-kaffa da ibadarsa, yana boya, ba ya so a sani, tare da hakan yana tsoron ko Allah ya karba ko bai karba ba. 

Amma a yau - ta kafafen sadarwa na sada zumunta (Social Media)- Shaidan ya kawata wa dadama daga cikinmu, mu rika tallata ibadunmu  ga jama’a da sunan muna neman addu’arsu. Dayanmu yakan ce, “Ga mu nan muna Umarah.. 
Ko mun kammala aiki hajji, a ta ya mu da addu’a… Ko yanzu muka kammala tahajjudi, a taya mu da addu’a Allah ya karba...”. Ko ga mu muna karatun alkur’ani… muna neman addu’arku…. Da sauran sakonni irin wadannan. 
Wannan abu ne mai hadarin gaske ga niyyar bawa musulmi. Don haka mu yi hattara!!

Thursday, 23 February 2017

Yayin Da Allah Ya Halicci Aljannah Da Wuta - Dr Sheikh Muhammad Sani Umar R/Lemo

Yayin Da Allah Ya Halicci Aljanna Da Wuta!

“Lokacin da Allah ya halicci Aljannah, sai ya ce wa Mala’ika Jibrilu, ‘Jeka ka ganta’. Yayin da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce wa Allah, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, babu wanda zai ji labarin Aljannah, sai ya yi kokarin ya shige ta’. Sai Allah ya kewaye ta da abubuwan da rai ba ta so, sannan ya ce, ‘Ya Jibrilu! Je ka yanzu ka ganta’. Da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, ina tsoron yanzu kam babu wani wanda zai iya shigarta’.

 Yayin da kuma ya halicci wuta, sai ya ce, ‘Ya Jibrilu! Je ka ka ganta’. Da ya je ya ganta, sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangjijina! Na rantse da izzarka, babu wani da zai ji labarinta, sannan ya yarda ya shige ta’. Sai Allah ya kewaye ta da abubuwan sha’awa, ya ce, ‘Ya Jibrilu, je ka yanzu ka ganta’. Da ya je ya ganta sai ya dawo ya ce, ‘Ya Ubangijina! Na rantse da izzarka, babu wani wanda zai rage bai shige ta ba’..”. [Ahmad, #8648, Daga Abu Hurairah (R.A.)].

[MP4]Ganduje Ya kira President Muhammad Buhari ( kalli Video )

Assalamu alaikum Warahamatullah,barka da yau da fatan kowa yana lafiya.
Wanannan video ne da Gwamna Ganduje ya kira Muhammad buhari inda Alhamdulilahi shugaban kasa ya samu lafiya.
Domin saurare da kuma download kayi latsa nan.

Governor Ganduje Call president Buhari

DOWNLOAD MP4 HERE

Tuesday, 21 February 2017

Na Tuba Daga Zina Yaya Iddata? -Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Na Tuba Daga  Zina, Yaya Iddata ?

Tambaya:
Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa ne ISTIBRAI din ta?

Amsa:
To 'yar'uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi sabani game da iddarta.

1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka.

2. Za ta yi jini daya kawai, saboda fadin Annabi S.a.w. "Ba'a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila daya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.

Don neman Karin bayani duba Almausu'a Alfikhiyya Alkuwaitiyya 30/341.
Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana tabbata da jini daya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina.

Allah ne mafi Sani.
Dr. jamilu Yusuf ZAREWA
22\2\2016

Monday, 20 February 2017

Dan Aljannah Ba Ya Bukatar Wani Canji!! -Dr Sheikh Muhammad Sani Umar R/lemo

Dan Aljannah Ba Ya Bukatar Wani Canji:

Allah da ya halicci dan Adam ya kuma saukar da shi a doron kasa, sai ya kimsa masa sha’awar samun canje-canje na yanayi da guri da hali. Yayin da ya dade a cikin wani yanayi ko guri daya, duk yakan ji ya gundure shi, ya gaji da shi, komai dadinsa, yana son ya ga wani canji. Wannan yanyin halitta da Allah ya yi wa dan Adam, ita ce take taimakon shi wajen kawo ci-gaba a rayuwa ta duniya, da raya kasa, da habaka ta, kamar yadda Allah ya nema daga wajensa.

 Amma a Aljanna sai Allah ya cirewa masa wannan sha’awar, ya sanya masa tsananin kauna da sha’awar zama guri guda, ba tare da ya kosa ba, ko ya rika tunanin canji daga yanayin da yake ciki na ni’ima zuwa wani yanayi daban. Wannan kuma shi ne ya fi dacewa da rayuwar dan Aljanna wanda Allah ya masa tanadin duk wata bukatarsa, ya samar masa duk wani abu na jin dadi da morewa a cikin gidan Aljannah.

Da a ce, za a bar shi da waccan sha’awa ta shi, kamar yadda take a duniya, to da ya nemi Allah ya canza masa wata aljannar ba wadda yake ciki ba, domin ya gaji da ita. Shi ya sa Allah ya ce mana, “Lallai wandanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai, ajannatan Firdausi sun tabbata masauki gare su. Suna masu dawwama a cikinsu, ba su bukatar wani canji game da su”. [Al-Kahfi, 107-108].

Allah Kasa mu shiga Aljannah don Rahamarsa.

ku kasance da sadeeqmedia blog domin samun,Fatawa,Tafseer,Wa'azi da sauransu

Sunday, 19 February 2017

Aikin Tallafi Ga Dan Adam Idan Ba Allah A cikin!!! - Dr. Sheih Muhammad Sani Umar R/Lemo


Aikin Tallafi ga Dan Adam Idan Ba Allah A Ciki….

Masu gabatar da ayyukan jinkai da taimakon mabukata da agazawa gajiyayyu, ba don Allah, ba don neman yardarsa ba, sai don neman shuhura da yabo wajen mutane, da sunan taimakon jin kai ga dan Adam, wadannan ayyukansu ba su da wani rabo na lada a wajen Allah. Sai wanda ya yi aikinsa yana mai imani da Allah, kuma yana neman sakamako a wajesa shi ne Allah zai biya shi ranar gobe kiyama.

 Akwai wani babban mai arziki a zamanin jahiliyya da ya shahara da taikon talakawa da gajiyayyu, don taimakawa baki da matafiya, amma bai yi imani da ranar lahira ba. Sai wata rana Sayyidatuna A’isha ta cewa Manzon Allah (S.A.W) “Ya Ma’aikin Allah, Abdullahi bn Jud’an a zamanin Jahilayya ya kasance mutum ne mai girmama baki da sada zumunci da fansar bayi, tare da kyautatawa makota”. Ta yaba masa sosai, sannan ta ce, “Shin hakan zai amfane shi a gurin Allah?”. 

Sai Mazon Allah ya ce, “A’a! Saboda bai taba budar bakinsa ya ce, ‘Allah ka gafarta mani kurakuraina ba ranar gobe kiyama’ ”.[ Ahmad, 2489.

Ku kasance da sadeeqmedia.com.ng domin samin karance -karance da karatutuka na Addinin musulunci

Ba Wanda Ya Kai Dan Bidi'a Wahalar Banza!!! -Dr Muhammad. Sani Umar R/Lemo

Ba Wanda Ya Kai Dan Bid’a Wahalar Banza:

Allah Ta’ala yana cewa, “Ka ce, ‘Shin in ba ku labarin wadanda suka fi kowa asarar ayyukansu. Su ne wadanda aikinsu ya bace a rayuwar duniya, alhali kuwa suna tsammanin suna kyautata ayyuka ne”.[Al-Kahfi, 103-104]. 

Magabata sun fassara wannan ayar da cewa, ana nufin Yahudu da Nasara, kamar yadda Sa’ad bn Abi Wakkas (R.A) ya yi. Yayin da shi kuma Sayyiduna Ali (R.A) ya fassara ta da cewa, su ne Khawarijawa. 

Imam As-Shatibi ya hade ma’anonin guda biyu, inda ya nuna cewa, ayar tana nufin duk wani mai aikata  bid’a a addini, sawa’un a cikin Yahudawa ne, ko a cikin Nasara ne, ko a cikin musulmi ne. Domin duk wanda yake bid’a yana daukan abin da yake yi abu ne mai kyau, tare da cewa, ya kaucewa hanyar da shari’a ta yarda da ita. 

Wannan magana ita ce, abin da Imamul Mufassirina Ibn Jarir At-Tabari ya bayyana a tafsirinsa. Allah ya tsare mu da aikin bid’a.


Daga Darulfatawa.com

Saturday, 18 February 2017

Fatawar Rabon Gado (99) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Fatawar Rabon Gado (99)


Tambaya

Assalamu alaikum malam ya za'a raba gadon wanda ya mutu ya bar 'ya'ya maza 9 da 'yaya mata 8 da matan aure 2 da 'yan'uwa shakikai?

Amsa

Wa alaiku assalam Za'a raba abin da ya bari gida:8, a bawa matansa kashi (1), ragowar kashi 7 sai a bawa 'ya'yansa Maza da mata su raba, saidai kasancewar su (26) ne, tun da kowanne namiji yana matsayin mata biyu ne, za mu buga adadinsu (26) akan asalin (8) In da zai ba mu 208, sai mu bawa matansa daya cikin (8)dinta wato (26) ta in da kowacce mace za ta samu (13), ragowar sai mu bawa 'ya'yansa, kowanne yaro zai samu (14), kowacce yarinya kuma za ta samu (7).

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR JAMILU YUSUF ZAREWA

15/2/2017

Su Wanene Yajuju Da Majuju [2] - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Su Wanene Yajuju Da Majuju? [2]

Ayoyi da ingantattun Hadisai sun mana bayanin su wanane Yajuju Da Majuju. A dunkule za mu iya cewa, Yajuju Da Maj uju su ne kamar haka:

1. Wasu kabilu ne guda biyu daga zurriyar Annabi Adam (A.S).

2. Kamannin halittarsu irin ta sauran ‘yan Adam ce babu wani banbanci.

3.  Suna da yawan gaske.
4. Kabilu ne masu yawan barna da ta’adi a bayan kasa.

5. Suna rayuwa bayan ganuwar da Zul-Karnaini ya gina domin hana su shigowa garurwan makotansu su yi musu barna.

6. Dab da tashin alkiyama wannan ganuwa za ta rushe, su fito, su kwararo ta ko-ina, su shanye ruwan koramar Tabariyya. 

7. Ba jimawa Allah ta’ala zai aiko musu annobar wata irin tsutsa wadda za ta rika shiga wuyayensu ta rika kashe su, har gaba daya su kare. Daga nan sai Allah ya aiko wasu manya-manyan tsitsaye da za su rika daukar gawawwakinsu suna jefa su cikin teku.

8. Duk wannan zai faru ne bayan bayyanar Mahdi, da saukar Annabi Isa, da kashe dujal. 

9. Da zarar sun fito, sauran manya-manyan alamomin tashin kiyama za su biyo baya da gaggawa

Thursday, 16 February 2017

[MP3]sabuwar wakar Rarara: Buhari Ya Dawo Sai Murna Gamu Talakawa,Lafiyarsa Qalau sai dae kuci kanku Yan Uwan Mayu

Asalamu Alaikun warahamatullah yan uwa a yau nazo muku da waka mai dadi shahararren mawakin zamani a fagen siyassa wato Dauda kahuta Rarara yayiwa shugaban kasa President Muhammad Buhari ,Mai taken :Buhari ya dawo sai murna gamu Talakawa lafiyasa qalau,sai dae kuci kanku yan uwan mayu.

A cikin wanannan waka ga baitutuka kamar haka:sanu da sauka baba buhari tsoho ya sauka da kwari,farin tsoho na Allah uban talakawa,gashi ya zo yai mana gyara,idan yake fadin yan borno suna murna dawowar baba buhari,sokoto na dawowar baba buhari,katsinawa na murna dawowar baba buhari,kanawa na murna dawowar baba buhari.

Har inda yan kanzagi na fito suna cewa abba ku ya zam Gawa ,to ga buhari ya dawo lafiyarsa ,tsoho ya sauka da kwari.

Inda yake cewa da anyi magana sai ace Rarara ya girmi buhari.
Bari in barku haka hausawa kance waka a bakin mai ita yafi dadi .
Domin saukar da wanannan waka sai ka latsa nan 

  DOWNLOAD MP3 HERE

A yi sauraro lafiya

[MP3] Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken:Burgu Ya Makale, Ar Burgu Yaji Wuya

Assalamu alaikum warahatullah barka da yau da  fatan Kowa Yana Lafiya.

To ina masoya Dauda kahuta Rarara wanannan sabuwar waka ce wadda yayi mai taken ku bugamana takin burgu ya gudu ,burgu ya makale ma'ana Ya ji wuya domin download sai ka shi nan


DOWNLOAD MP3 HERE

A Yi Sauraro Lafiya,ku kasance da sadeeqmedia blog

Wednesday, 15 February 2017

Ganuwar Zul-Karnaini Da Babbar Ganuwar shina!-Dr Muhammad sani Umar R/lemo

Ganuwar Zul-Karnaini Da Babbar Ganuwar Shina:

Akwai wasu daga cikin masana da suke da ra’ayin cewa ganuwar da Sarki Zul-Karnaini ya gina it ce babbar ganuwar nan da take kasar China. Wannan ra’ayi nasu yana da rauni sosai, saboda dalilai kamar haka:

1. Zul-Karnaini ya gina ganuwarsa ne domin raba tsakanin mutane da Yajuju da Majuju. Amma ganuwar China Sarakunan China ne suka gina ta, domin kare kasarsu daga hare-haren mayaka.

2. Ganuwar Zulkarnaini ya gina ta ne da guntattakin karafa da narkakkiyar dalma. Amma babbar ganuwar China an gina ta ne da duwarwatsu da laka.

3. Ganuwar Zul-Karnaini ya gina ta ne tsakanin duwatsu guda biyu, domin ya toshe hanyar da Yajuju da Majuju suke bi domin afkawa makotansu. Amma ita babbar ganuwar China an gina ta ne akan duwatsu da kwazazzabai da hanyoyi, wadda ta taso tun daga gabashin China yar zuwa yammacinta tafiyar dubunnan mila-milai.

4. Ganuwar Zul-Karnaini ba wanda zai iya fasa ta har sai wa’adin da Allah ya deba mata ya yi, wato gab da tashin kiyama. Yayin da ita kuma babbar ganuwar China ta jima da farfashewa, har mutane na shigi-da ficinsu ta samanta.

To duk wadannan dalilai ne masu nuna ganuwar da Zul-Karnaini ya gina ba ita ce babbar ganuwar China ba.

[MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn

Yadda zaka samu Kyautar 1GB Data free 

Kyauta   a layin Mtn kyau
ba wani abu bane kwae ka duba ,layin ka na mtn idan ka samu wanannan sako

Congratulations! You have been gifted  FREE 1GB data, valid for 7 days, to surf the internet. Dial *449*2# to activate your offer. Deal Zone

To kayi ta danna wanannan code kamar sau 10times.
To sai ka jira zai iya dauka lokaci kamar 1hour ba a turomaka ba amma daga bayya zaka samu wannan sako haka:

Congratulations! You have successfully activated FREE 1GB valid for 7 days. Please dial *559*4# to check balance.

To shikenan kayi Nasara ,sa a nan idan kayi *559*4# baka ga balance karka damu ka danna wannan code *5594#
nima haka na samu ka duba wannan hoto.


Allah Yasa Adace Amen

Tuesday, 14 February 2017

Karbar Na-Goro A Ma'aikatun Gwamnati!!!- Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Karbar Na-Goro A Ma'aikatun Gwamnati!!!

Tambaya ?

Assalamu alaikum malam ni ma'aikacin ne da nake aiki a ma'aikatar binciken kudi (state audit), ina cikin team, akwai wasu kudi da ma'aikatar da aka turamu bincike suke bayarwa, kamar haka:

1.kudin Refreshment, maimakon duk rana su kawo mana abinci, sai duk wata sai su bamu dukiya har mu qare aikinmu.
2.kudin sallama. Idan muka kammala sai ma'aikatar ta bamu kudin a matsayin  sallamar bakinta.
3. Wasu kudin da ban san ta ina suke fitowa ba, sai dai kawai team leader namu ya kira ni ya bani, dama kuma ko wadancan nau'i 2 da na fada, kirana kawai yake, ya bani abinda zai bani, ba tare da na san a hannun wa ya mso ba, nawa ya amso, ko makamancin haka.
4.Akwai wadanda na san wani mai karin kudi ne ya bayar don a bar shi  da karin,  suma idan naga sanda ya bayar zai bani, wani wanda ban san sunyi shirinsu ba ba zai ba ni ba. 
5. Akwai wadansu mutane da shekarunsu sun kai su aje aiki, ko wasu masu qarin kudi ko ma wasu ghost workers ne babu su wasu ke cin kudin, sai idan nazo rubutu report sai yace kada nayi musu query ya sanda su.
6. Akwai wadanda ake riqe albashin su idan basu zo sukayi verification ba, tanan ne ake, idan mutum yazo sai ayi clearing nashi a bashi salary dinshi, idan bai zo ba ghost workers ne, wani ne ke cin kudin shi, sai a dinga rabe wannan albashin kafin a rubuta report a debe shi a payroll. 
7. Shin ya matsayin daukar mataki akan mai qari da yawa kamar mai karin step 7 ko 6 a kyale mai 1? 
8. Ko alfarma na shiga ta wannan aikin don kawai sanayya, amma ka dauki mataki ga wanda baka sani ba? 

Amsa

  Wa alaikum assalam
1. ina muku wasici da tsoran Allah a duk aikin da kuke yi.        

2. Duk kudin da kuka San ba halal ba ne ku nisance su, hakan Shi zai sa Allah ya muku albarka a rayuwarku.

 3. Bai halatta ma'aikacin gwamnati ya amshi kowanne irin lada ba akan aikinsa da yake amsar albashi akai ba, saboda Fadin Annabi S.a.w. (Duk Wanda muka ba Shi aiki kuma muka ba Shi lada akan haka, to duk abin da ya amsa bayan haka ya zama haram ) kamar yadda  Abu Dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (2943).

 4. Amsar kudin-goro a wajan masu laifi da niyyar suturta su yana daga ha'inci da kuma rashawar da Allah ya tsinewa mai amsarta, kamar yadda hadisin Tirmizi mai lamba ta: (1336) ya nuna Hakan.

5. Duk wanda ya kiyaye Allah, tabbas zai kiyaye shi, wanda ya keta dokokinsa zai same shi a Madakata, tsarkake abinci na daga cikin hanyoyin karbar addua.

6. Kudin gwamnati haķki ne na jama'ar kasa, taimakawa wani ya ci ba bisa ka'ida ba magudi ne da zai sa su tsaya da shi ranar Alkiyama a gaban Allah .

7.Zunubi Shi ne abin da ka yi amma yake maka yawo a rai  kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai.

 8. Duk kyautar da aka yiwa ma'aikaici saboda kujerarsa, idan ya amsa ya ci haramun, wannan yasa Annabi S.A.W. ya fusata ya kuma yi kakkausar magana ga IBNU AL-LUTBIYYA lokacin da ya aike Shi amso zakka Amma kuma aka ba Shi kyauta ya amsa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a Sahihinsa. 

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA


12/02/2017

Allah kasa mu dace ku kiyaye Harkukinmu na Yau da Kullum amen

Monday, 13 February 2017

Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al'umma - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al'umma:

Wajibi ne shugaba ya zama mai kamewa daga taba dukiyar al'ummarsa.kada ya zama mai kwadayi akanta.Idan yana da wadatar dukiya ya yi musu aiki ba tare da ya karbi haraji daga hannunsa ba.Yin hakan yana daga cikar adalci da karamci da shugaba na kwarai zai nuna .Ka dubu Zul-karnaini yayin da jama'a suka yi masa tayin su biya shi lada,don ya yi musu ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju ,masu shigowa gari suna musu barna da ta'addanci. Sai ya nuna musu cewa,abin da Allah ya hore mishi ya ishe shi,ba sai ya karbi na hannunsu ba.

Don haka ya yi musu katanga mai karfi ta kare da narkakkiyar dalma,ba tare da sun biya ko kwabo ba,in banda ma'aikata da wasu kayan aiki da ya nema daga wajensu.Allah ya bamu labarin hakan inda yace ,("suka ce,"Ya Zul-karnaini! lallai Yajuju da Majuju masu barna ne a bayan kasa,shin mu baka wani lada ka gina ganuwa tsakaninmu da su."sai yace ,"Abin da ubangijina ya ba ni ya fi mini Alheri ,amma ku taimaka min da karfi don in sanya muku ganuwa ta kankare tsakaninku da su."[Al-kahfi,94-95]

Sunday, 12 February 2017

Shin Watanni Nawa Miji Zai Iya Kauracewa Matarshi Ta Sunna ?- Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Shin Watanni Nawa  Miji Zai Iya Kauracewa  Matarshi  Ta Sunnah ?

Tambaya:
Tambaya  ita ce؛ shin Tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya kaurace wa matar shi ta sunna kuma wani Mataki ya dace ta dauka in har ya wuce period din da sharia ta halatta?.

Amsa:
Wa'alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara aya ta: 226. 

Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin surar ta nuna hakan.                          

In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo mata ko kuma ya sake.                           

Allah ne mafi Sani

Amsawa

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

10/02/2017

Yada Hoton Gawar Dan Uwanka Mumuni Ba Aiki Ne Na Masu Sanin Ya kama ta-Dr Muhammad Sani Umar R/lem

Yada Hoton Gawar Dan Uwanka Mumuni Ba aiki Ne Na Masu Sanin Ya Kamata Ba

Wadanda suke dauko hutunan gawawwakin 'yan uwansa musulmi suna yadawa a dandalin sadarwa, wai don su sanar da rasuwarsu ko su yi ta'aziyyarsu, masu yin haka ba sa kyautawa ko kadan. Yin haka alama ce ta rashin wayewa da karancin fahimtar addini. 

Gawar dan uwanka tana da alfarma da mutunci, bai kamata ka keta masa wannan mutuncin ba bayan mutuwarsa. Shi ya sa ko wankan gawa ba kowa ake sa wa ba sai wanda aka yarda da shi.

 Ka duba, mutum ko barci yake yi ba zai so a dauki hotonsa ana yadawa ba, saboda ba lalle ne ya kasance cikin yanayin da zai so a gansa a cikinsa ba. Ka dubi yanayinka kai kanka, idan za a dauki hotonka kakan shirya don ganin hotonka ya yi kyawon kama, to don menene za ka rika baza hoton gawar dan uwanka bayan mutuwarsa? Kuma shin ba za a yarda da labarin mutuwarsa ba ne sai ka sa hotonsa?

 Abin takaici ma wani lokaci wani ya jima da rasuwa amma idan wani ya zo magana a kansa sai ya sako gawarsa a cikin wani yanayi wanda bai dace ba sam, kuma shi mamacin da yana da rai ba zai so a gan shi a wannan yanayin ba.

 Wani lokaci 'yan uwa za su yi hadarin mota suna kwance kace-kace cikin jini, sai wani sakarai ya dauko hotunansu yana bazawa wai shi a tunaninsa daidai yake yi, tir da irin wannan aiki na rashin nutsuwa. 

Mu kiyaye hakkin yan uwanmu bayan mutuwarsu kamar yadda muke kiyaye shi a lokacin rayuwarsu. Allah ka ba mu kyakkyawar fahimta. Amin.

Allah Ya karemu Daga Yada abinda Baikamata ba,Allah Yayi mana Karshe na Kwarai .

KAYI SHARE ZUWA GA YAN UWA MUSULMI A FACEBOOK OR WHATSAPP.

[MP3] Rayuwar Aure - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano

Assalamu alaikum warahamatullah
Barka da Asuba da fatan kowa yana lafiya amen



A yau lecture mu mai Taken :RAYUWAR AURE .

muke tafe da ita wanda Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya gabatar 


Domin Download sai ka latsa nan


      DOWNLOAD MP3 HERE


AYI Sauraro lafiya

karku manta share to ur friends 

Saturday, 11 February 2017

Fatawar Rabon Gado (98) -Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Fatawar Rabon Gado (98)



Tambaya


Assalamu alaikum,Allah ya qara wa Dr imani da iklasi,Dr tambaya ce muke da ita,mutum ne ya rasu bai taba aure ba ,sai yan uwa, wadda suke uwa daya uba daya su biyu mace da namiji, sai kuma wadda suke uba daya suma maza biyu da mata biyar, amma iyayen su sun rasu, to yaya za'a raba wannan gadon,shin iya wadda suke daki dayane suke da gadonsa ko sauran ma wadda uba ya hadasu suma suna da gadon?  Nagode

Amsa

Wa alaiku assalam, shakikansa, wadanda suke uwa daya, uba daya, su ne kawai za su ci gado a nan, duk namiji ya dau rabon Mata biyu

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR JAMILU YUSUF ZAREWA                   7/2/2017

05/01/2017


ku kasance da sadeeqmedia ako yaushe domin yada addinin musulunci

Friday, 10 February 2017

Domin Nagarta Aiki: Shugaba Ya Yi Tarayya Da Ma'aikatansa - Dr Muhammad sani Umar R/lemo

Domin Nagarta Aiki:Shugaba Ya Yi Tarayya Da Ma'aikatasa

Yana da kyau shugaba idan ya bayar da wani aiki,ya rika samun kasancewa tare da masu yi aikin,ko ya zamo mai sa ido akan aikin da ya bayar ,domin yin haka zai taimaka wajen karawa ma'aikata kuzari da karashin gudanar da aikinsu.

kamar yadda hakan na iya taimakawa musu wajen inganta aikinsu da zartar da shi yadda ya kamata.Dubi sarki zul-karnaini yadda ya kasance tare da ma'aikatansa,ya zamanto daya daga cikinsu,ana gudanar da aikin ginin ganuwa tare da shi,kuma karkashin umarninsa,kamar yadda Allah ya ba mu labarinsa inda yake cewa,zul-karnaini yace,"(ku kawo min guntattakin karafa.,".Har sai da ya daidaita (gini) tsakanin duwatsu nan guda biyu,sai ya ce,"ku hura wuta".Har sai da ya mayar da shi (kamar) wuta, sai ya ce,"ku kawo min narkakkiyar darma in zuba a kansa").[Al-kahfi,96].

Allahu Akbar ,Ya Allah ka bamu ikon aikata Alkhari da kuma yan uwa su gane cewa dan ka bada aiki ka tsaya ba rashin amincewa ne ko yarda ba.

[MP3] Khudba :Hakuri Da Zama Da Mutanen Kirki - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Assalamu Alaikum warahamatullah ,barka da juma'ah da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

A Yau nazo muku da khudba wanda mallam yaga gatabar wato

 Sheikh Dr Muhammad sani Umar R/lemo,ya gabatar.


Taken khudbar :Hakuri Da Zaman da Mutanen kirki

wanannan khudba ce mai matukar amfani wanda yana da kyau duk musulmi ya zamo mai hakuri da juriya.


sannan kuma ya zamo abokanansa mutanen kirki ne,wanda a yanzu idan ana so a tambaye halayen mutum to a Tambaye abokinsa ko abokanansa .

domin zama da muaten kirki shine ke nuna alama mutumin kirki, zama da mutenen banza ko shashashu shi ke nuna mutumin banza ne.


Domin ka samu wanannan khudba da mallam ya gabatar sai ka latsa nan,idan ka latsa a opera zai baka zabi biyu kamar haka:CANCEL and SAVE ,sai ka latsa SAVE .shikenan


    DOWNLOAD MP3 HERE


A Yi sauraro lafiya

Dan Allah kayi share zuwa ga Abokananka na Facebook or whatsapp ko wata kafa labarai.

Thursday, 9 February 2017

Gwamnati da 'Yan kasa: sai An Hada karfi Da Karfe -Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Gwamnati  Da 'Yan kasa:Sai An Hada karfi da Karfe:

Duk Yadda daula take da karfin tattalin Arziki da wadatar ma'adani,idan har ana son wannan kasa ta ci-gaba wajen ayyukan raya kasa da gina al'ummarta dole ne jama'ar kasa sai sun taimaka mata;kowa daidai gwargwadon abin da Allah ya hore masa,wani da iliminsa ,wani da karfinsa,wani da dukiyarsa ,kowa da  abin zai iya ,to sai ka ga wannan kasa ta ci-gaba,rayuwar al'ummarta ta yi kyau.

Dubi sarkil zul-kurnaini, duk da abin da Allah ya bashi na karfin mulki, ya hore masa na duk wani abin da mai mulki yake bukata don gudanar da mulkinsa ,amma duk  da haka ,lokacin da wadannan kabilu masu makotaka da kabilun Yajuju da Majuju suka nemi agajinsa da ya gina musu ganuwa tsakaninsu da Yajuju da Majuju,sai da ya nemi su taimaka masa da karfinsu don ya yi musu wannan aiki.

Ga abin da Allah ya fada mana ya gudana tsakaninsu :
(suka ce ,"Ya zul-karnaini! lallai Yajuju da Majuju masu barna ne a bayan kasa,shin mu ba ka wani lada ka gina ganuwa tsakaninmu da su." sai yace ,"Abin da ubangijina ya ba ni ya fi mini alheri ,amma ku taimaka min da karfin don in sanya muku ganuwa ta kankare tsakaninku da su." [Al-kahfi,94-95].


Allah Akbar kaji manya masu imani wadanda suke biyayya ga Allah da ka'idojin mulki ,Allah ya bamu shuwagabani masu imani.


Dan Allah kayi share zuwa ga abokanan arziki domin ka samu mai yadaa alheri a al'ummarka/ki

[MP3] Wacece Mijinta Yafi -Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Kano [Rahamahullah]

Assalamu alaikum warahamatullah barka da yau da fatan kowa yana lafiya tare da mun wuni lafiya

A Yau munzo muku da wata lecture wanda mallam ya Gabatar mai Taken: Wacee Mijinta Yafi

wanda sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Kano [Rahamahullah]

To fah yan uwana musulmi mata ga lecture wanda a gareku tamkar competition ne sanin miji nagari

Haka zalika ku kuma yan uwana maza ,ku saurari wanannan lecture domin ka shirya ka gyara ga matan ka ,idan kuma kana irina  mabukaci To sai mu shirya mu kiyaye


Domin download wanannan lecture sai ka latsa nan da kasa zai nuna maka zabi biyu biyu a opera SAVE and CANCEL ,sai ka zabi SAVE.


           DOWNLOAD MP3 HERE

A yi sauraro Lafiya ,ku kasance da sadeeqmedia

Dan Allah kuyi share zuwa ga yan uwa musulmi domin ka samu lada yada Alkhari

Wednesday, 8 February 2017

Dole A samu Tarjama Domin Ci-Gaban kowace Al-umma!!!- Dr Muhammad sani umar R/Lemo

Dole A Samu Tarjama  Domin ci-Gaban kowace Al-umma:

Domin ci-gaban kowace irin al-umma akwai bukatar a samu masu tarjama a cikin wanannan al-umma.Yana kuma daga alamun ci-bayan al-umma ya kasance a cikinta babu wadanda suka  san harasan wasu al-ummomin na waje,domin karantar ilimin dake cikin wannan yaren nasu da al'adunsu ,don daukar al'adunsu masu kyau,da ci-gabansu na rayuwa.

Shi yasa Allah da ya ba mu labarin mutanen da  zul-karnaini ya gina musu ganuwa a garinsu,domin kare su daga hare-haren Yajuju da Majuju , da ya tashi nuna mana koma-bayansu a rayuwa sai nuna mana basa fahimtar da yaren kowa sai nasu.

Allah yace , "Har sa da ya kai tsakanin wasu duwatsu guba biyu,sai ya samu wasu mutane kafin duwatsun biyu, da kar suke fahimtar magana." [ Al-kahfi,93].





Allah kasa mu dace da wannan Tafseer ,Allah ka bamu ikon aikata daidai ,



Dan Allah ka yi share zuwa ga Al-ummar musulmi domin samun ladah yada alkhairi.

[MP3] Yadda Ake Godewa Allah Ta'allah Da Ni'ima Da Ya samu Mutum -Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah

Assalamu Alaikum Warahamatullah barka da yau da fatan kowa yana lafiya .

A Yau nazo muku da wa'azin mallam wato sheikh Musa Yusuf Asadus sunnah.

wanannan wa'azin yana da matukar amfani saboda yakamata kowa yasan wanannan tatakai na nuna farin ciki da ni'imar da Allah ya baiwa bawasa dan Adam,domin da yawanmu bamusan matan da ake yi godiya ga Allah .

To Alhamdulillahi yau kam ga shi mallam yazo muku da wanannan wa'azi mai taken:


Yadda Ake Godewa Allah da Ni'imar da Mutum Ya samu


Domin Download sai ka latsa nan ,idan ka latsa zai baka zabi biyu CANCEL and SAVE ,sai kayi SAVE.


                DOWNLOAD MP3  HERE


Ayi sauraro lafiya


Dan Allah kayi share zuwa ga abokanka na Facebook ko wata kafa yada labarai domin ka zamo mai yada alhairi 

Tuesday, 7 February 2017

Mulki Baya Dorewa Sai Da Abu Biyu!!!- Sheikh Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Mulki Baya Dorewa Sai da Abu Biyu:

Mulki baya kafuwa ya yi karko ya dore sai da abubuwa biyu:

Na Farko: JARUMTA ,Wadda itace,hukunta duk wani mai laifi ba sani-ba -sabo,Wanda yin hakan Zai jefa Tsoro a Zuciyar da wani mai shirin yayi barna.

Na Biyu: KARAMCI,Wanda yake nufin kyautatawa da ihsani ga duk Wani Wanda ya cancanci  kyautatawa da ihsani saboda kyawawan Ayyukansa da kwazonsa.

Yayin da aka rasa wadannan abubuwa biyu ko aka rasa daya daga cikinsu to mulki ba zai dore ba,ko kuma bazai kyau ba.

Dubi JARUMTAR Zul-kKarnaini,inda yake cewa ,"To amma wanda yayi Zalunci,to zamu Azabar da shi ,yi masa Mummunar azaba."[Al-kahfi,87]

Sannan dubi KARAMCINSA, A Maganarsa da yake cewa,"Amma kuma duk Wanda Yayi Imani,kuma yayi aiki na gari ,to yana da kyakkyawan sakamako,kuma za mu fada masa tattausar magana game da al'amarinmu."[Al-kahfi,88]


Allah ka baiwa shuwgabaninmu wanannan abubuwa guda biyu ,domin su zamo masu amfani da ayoyin Allah.

Dr Muhammad sani Umar R/lemo -Yayin da yake Karba Kyauta Daga Madina(cikin hoto)

Sheikh Dr. Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo kenan yayin da yake karbar kyautarsa daga Sheikh Abdurrahman Arragdadiy Shugaban sashen Shari'a na Jami'ar Musulunci ta Madina, daren jiya Litinin 06 Feb 2017.

Monday, 6 February 2017

Zul-karnain Wanene Fitowa ta 2? - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Zul-karnain Wanene 2

A cikin ayoyin goma sha bakwai (17) da Allah ya labarta mana kissar Zul-kurain,wasu sifofi sun bayyana wadanda sune za su zama amsa game da tambayar "Wanene Zul-karnaini."  Ga su kamar haka:

1. Sarki ne mai kadaita Allah ,wanda kuma yayi imani da ranar lahira

2.Allah ya ba shi karfin mulki ,wanda ya ci garuwa masu yawa da yaki;

3.Allah ya bashi duk wani abu mai mulki yake bukatar samunsa a zamaninsa domin kafa mulkinsa, da tabbatar da adalci a kasa.

4. Ya kasance mai kira zuwa ga bautar Allah shi kadai  da yaki da bautar wanin  Allah .

5. Ya karade duniya da yawo, ya isa yammacin Duniya daga nan ya dawo ya danna yammacinta,inda har ya kai wajen da ya gina  babbar ganowa tsakaninsu Yajuju da Majuju da sauran kabilu makotansu.

6. Yana karbar umarninsa ne t hanyar wahayi da ake yi masa kai-tsaye (idan shi Annabi ne) ko ta hanyar wani Annabi dake tare da shi a cikin sojojinsa.


Allah kasa mu dace ,Allah ya sakawa mallam da Alkhairi .karka manta dan uwana kayi share zuwa ga yan uwa musulmi domin ka samu ladah yada abun alkhairi

ku kasance da sadeeqmedia

[MP3] Rayuwar Musulmi A Musulunci - Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Kano [Rahamahullah]

Asslamu Alaikum Warahamatullah Yan Uwana Musulmi Barka da Wanannan Rana mai Albarka.

A Yau nazo muku wani Wa'azi mai matukar amfani wanda musan Yadda zamuyi rayuwa a cikin addinimu mai matukar dadi a al'umah wanda yake baiwa haqqinsa.


Wannan wa'azinmai taken


RAYUWAR MUSULMI


Wanda mallam sheikh Ja'afar Mahmoud Adam kano [Rahamahullah]

Domin download wanannan sai ka latsa nan ida ka latsa zai baka zabi biyu CANCEL and SAVE  ,sai ka latsa  Save.

            DOWNLOAD MP3 HERE


A Yi sauraro Lafiya.


Dan Allah kayi share zuwa ga abokanka  a Facebook ko whatsapp.

Sunday, 5 February 2017

[MP3] Muhimmancin Tauhidi da Iklasi A Ayyukan Musulmi -sheikh Abubakar Gero Argungu

Assalamu Alaikum warahamatullah barka da yau da fatan kowa yana lafiya barkamu da yau da fatan kowa yana lafiya.

A yau muna dauke da muhaddara mai Taken:

Muhimmancin Tauhidi da Iklasi a Ayyukan Musulmi

wanda mallam Sheikh Abubakar Gero Argungu 

Ya gabatar wanda yana da kyau yan uwa musulmi mu san wadanda muhimmanci ne aiki da Tauhidi da iklasi a Rayuwar ta musulmi.

Domin samun wannan lecture sai ka latsa nan indan ka latsa zai baka zabi CANCEL anda SAVE ,sai ka latsa Save shikenan

                  DOWNLOAD MP3 HERE


A yi Sauraro lafiya 

Tarihin Muhammad Auwal Abu Abdirahaman Albaniy Zaria[Rahamahullah]

Tarihin Muhammad Auwal Adam Abu Abdirrahaman Albaniy [Rahamahullah]



Sunana: Muhammad Auwal
Sunan mahaifina :Adam
Sunan mahaifiyata: Saudah
Abu Abdirrahman shine Alkunyata
Albaniy shine laqabina

An haifeni a unguwar Muciya sabon garin Zaria a shekarar 1960.

Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi litattafan da akeyi a zaure na fiqhu dana Lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai mabanbanta a kasata Nigeria da kasashen waje inda na koyi Qur'ani da dukkan kira'o'insa, hadisi da musdalah dinsa, tafsiri da usul dinsa, harshen larabci da fannoninsa, fiqhu da usul da Qawa'id dinsa d.s.

Nayi makarantar firamare a sabon garin Zaria
Nayi sakandare a kwalejin barewa Zaria
Nayi Diploma akan:

Law

Computer science

Mass Communication

Hausa Language

Nayi Degree akan ICT

Nayi Masters akan Islamic studies

Ni Professional journalist ne

Ni Certified microsoft engineer ne

Ni Linguistic ne

Na karanci library science

Nayi programme na N+ akan Computer

Nayi Programme na A+ d.s

Ina da company wanda yake gabatar da ayyuka a fannoni dabam-dabam
Na karantar da litattafai kusan dari a rayuwata a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da laccoci dabam-dabam a gida Nigeria da kasashen ketare
Na fassara litattafai na musulunci masu yawa.

Nayi tahqiqin litattafai da dama
Na gina cibiya mai suna Darul-Hadeethissalafiyyah Zaria Nigeria (DHSN) wadda a karkashinta akwai makarantu kamar:

Albaniy science international Academy (pre-nursery, nursery, primary da secondary) na bangaren maza dana bangaren mata

Daaru Ibn Katheer Litahfeezil Qur'an
Sheikh Nasiruddeenil Albaniy College of Higher Islamic studies.

Na fara gina jami'a mai suna Albaniy University of Information and Communications Technology

Na fara gina gidan marayu

Na samar da inda zan gina asibiti

Na samar da inda zan gina gidan rediyo da talabijin.

Na samar da dakin karatu (library) domin anfanar malamai da daliban ilmi

Ni mutum ne mai son cigaban al'ummata ta hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allah (saw) shine mai gidana
Banayin sassauci ko daga kafa akan duk abinda ya sabawa Qur'ani da sunnah a bisa manhajin magabata na kwarai, amma ina yin hakan tare da duba yanayi, wuri da kuma halayen mutane
Daga cikin sana'o'ina akwai:

Dinki

Kanikancin computer (computer engineer)

Mashawarci a harkar computer (computer consultant)

Computer networking

Aikin jarida

Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce d.s

Duk abinda na assasa a rayuwata da kudina na samar dasu domin ban dogara da kowa ba bayan Allah Mahaliccina, sannan sai sana'o'in da nakeyi
Nayi waqafin abubuwa dana assasa baki dayansu gareni domin anfanar al'ummar musulmi

Babban manufata shine sharewa musulmai hawaye game da matsalolin da suke fama dasu na addini da rayuwa a fannoni daban-daban a karkashin mahanga na addinin musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu indawo duniya in bayyanasu ba! Amma Ubangijinmu yana nan a madakata yana jiranmu a inda ranar Alkiyamah zan shako wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allah Sarkin sarakuna ince Ya tambayesu don me yasa suka kashe ni....?

Ina rokon Allah Yajikaina
Yayi mini rahma
Ya yafe mini kura-kuraina
Ya karbi shahadata
Ya hadani da Maigidana Manzon Allah (saw) a Aljannar Firdausi da sauran musulmi baki daya.
Ameeen.

Saturday, 4 February 2017

Zul-karnain wanene? - Dr Muhammad. Sani Umar R/Lemo

Zul-karnain wanene?


malaman Tafsiri sunyi maganganu dayawa game da zul-karnain wanda Allah ya bamu labarinsa a cikin suratul kahfi.Dadama daga cikinsu suna cewa,shi ne Alexander dan Philip mutumin macedon ta masarautar Greek.kuma babban wazirinsa shine shaharraren malamin falsafar nan mai suna "Aristotle ".sai dai wannan magana babban kuskure ne, saboda:

1. zul-karnaini sarki ne mumini wanda ya yi imani da Allah  da ranar lahira. Alexander kuwa mushiriki ne mai bautar gumaka da taurari.

2. Alexander ba a kiransa da sunan "zul-karnaini",

3. yake -yaken Alexander  ba su kai kasashen Turkawa ba, iyakacinsu kasar farisa;

4. Alexander ba shi ne ya gina babbar ganuwa tsakanin Yajuju da majuju da sauran kabilu makotansu ba;


5.Alexander ya rayu ne gabanin haihuwar Annabi isah da kimanin shekaru dari uku.Yayin da zul-karnaini ya shude da dadewa

[MP3] Matsalolin Ma'aurata - Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Kano [Rahamahullah]

Assalamu alaikum warahamatullah barkamu da warahaka da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Yau kuma nazo muku da muhaddara mai amfanin gaskia ga yan uwa musulmi domin sanin matsalolin Ma'aurata da kuma hanyoyi da za'a magance su.

wanda mallam ya gabatabar mai taken MATSALOLIN MA'AURATA.
shine mallam

Sheikh ja'afar Mahmoud Adam kano [Rahamahullah]
Domin yin download wanannan muhaddara sai kayi click a nan

idan kinka yi click zai nunomaka CANCEL AND SAVE,sai kayi click on Save.

DOWNLOAD MP3 HERE

Dan Allah kayi share zuwa abokan arziki Facebook or whatsapp.


Friday, 3 February 2017

Mai Da'awa zuwa ga Gaskiya Dole ya shirya wa Duk wani kalu-bale - Dr muh'd sani umar R/lemo

Mai Da'awa zuwa Gaskiya Dole ya shirya wa Duk wani kalu-Bale:

Duk wanda zai shiga aikin da'awa ,da kiran mutane zuwa ga gaskiya,dole ne ya shirya wa duk wani kalu-bale ,ya sani cewa, za a fuskance shi da tambayoyi daban-daban ,wasu da niyyar neman karuwa,wasu kuma da zimmar kure da muzantawa ,Don haka dole ne mai da'awa ya kasance mai yawan karance-karance  domin ilimantar da kansa da kuma fuskantar irin wancan kalu-balen .

Dubi yadda kuraishawa suka tasa Annabi (S.A.W) gaba da tambaya  game da labarin zul-karnaini don su kure shi su tozarta shi. Allah yace ,

"Suna ta tambayarka game da zul-karnaini .kace, ba  da dadewa ba zan karanta muku labarin sa".[Al-kahfi,83].


Dan Allah kuyi share zuwa ga yan uwa musulmi domin kai ma ka samu lada ya da Alkhairi.


[MP3] Tsayuwa Akan Sunnah - Sheikh Abubakar Gero

Assaalamu Alaikum Warahamatullah barka da yau da fatan kowa yana yana lafiya.

Barka da juma'at mubarak ,Allah ya bamu Alkhairi da ke cikinta.

Ayau zazo muku da wa'azin mallam shahararen mallamin nan na Nigeria wanda shine sunkayi gwagwarmaya wajen wa'azi a Nigeria wanda har ake masa take da SOJAN TURNUKU NA AFRICA. 

wanannan mallamin dae shine 

SHEIKH ABUBAKAR GERO ARGUNGU

wannan wa'azi mai Taken :Tsayuwa ga Sunnah

kaji yadda mutanen kirki nayi tsaye a sunnah da hakuri da juriya da sunkayi a tsayawa ga Qalallahu Qala rasulallahi,

Domin download wananna wa'azi sai ka latsa nan . idana latsa zai nuna maka CANCEL AND SAVE sai kayi click on SAVE.

DOWNLOAD MP3 HERE


Dan Allah kayi share zuwa ga Abonkai na Arziki a Facebook or whatsapp

ku kasance da sadeeeqmedia

Thursday, 2 February 2017

Yarda Da Kaddara A Rayuwar Mumini - Dr Muhammad sani Umar R/lemo

Yarda Da Kaddara A Rayuwar Mumini:!!!

Duk abubuwan da suka faru a hannun khadir (A.S) sun faru ne cikin kaddarar Allah.kuma ya nufi faruruwarsu ne domin ya sanar da bayinsa cewa yana iya kaddara wa bawa abin da ba zai yi masa dadi ba, amma bai sani ba daga karshe zai zame masa alkheri  ga addininsa,kamar yadda ya faru a lamarin kashe wannan yaro ga iyayensa .ko ya zamo maslaha ne a gare shi a duniyarsa,kamar yadda ya faru a batun hudu jirgin ruwa.

wannan zai koyar da bawa hakuri da rungumar kaddarar Allah,domin fatan ta zame masa alheri a rayuwarsa ta duniya da ta addini.



  • Dan Allah zaka iya share ga yan uwa musulmi a Facebook or whatsapp

[MP3] Tarihin Shi'a da Aqidunnta Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano [Rahamahullah]

Assalamu alaikum warahamatullah yan uwana musulumi barka da yau da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.


masha Allah dukkan godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wa ta'alah da ya bamu lafiya da imani da yayi mu musulmi a yau nazo muku da karatun mallam a sound mai Taken:Tahirin shi'a da Aqidunnta ,wanda babban mallamin sunnah yayi wato 


Sheikh ja'afar mahmud Adam kano (Rahamahullah).


Domin sauraren wananna lecture da kunnen Basira domin kasan asalinta da kuma manufufinta wanda wasu muna 'yan shi'a basu sani ba to sai ka biyomu domin Download din wananna lecture sai ka latsa nan


          DOWNLOAD MP3 HERE


Ayi sauraro lafiya 

Dan Allah kayi share zuwa ga abokanka a Facebook or whatsapp.

Wednesday, 1 February 2017

Ladabi Ga Allah !!! - Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Ladabi Ga Allah!!!

Allah shine mahaliccin kowa da komai ,alheri da sharri .Amma yana  daga cikin ladabi ga Allah Ta'ala ba jingina masa komai sai abu mai kyau .Dubi khadir (A.S) lokacin da yake bayanin huda jirgin ruwa na wadannan mikinai,sai ya dangana wanannan aikin ga kansa, saboda a zahiri ba abu ne mai kyau ba,sai ya ce,

 "sai na yi nufin na lalata shi." 

Amma lokacin da yake bayanin garun da ya mikar, sai yace ,

"To sai ubangijinka ya nufi  su kai ganiyar karfinsu, su fito da dukiyarsa." 

sai ya danganta wannan aikin kai tsaye zuwa ga Allah Ta'ala.[Dubi Al-kahfi,79, da 82].

Dan Allah kayi share zuwa ga yan uwana abokanan arziki na Facebook ko whatsapp

Daga Dan uwanku Abubakar Rabiu

Fatawar Rabon Gado (96) Dr jamilu Yusuf Zarewa

Fatawar Rabon Gado (96)
                 
               Tambaya


Assalamu alaikum warahamatullah mallam.Don Allah ya za'a raba gadon matar da ta mutu ta bar mijinta da diya  macce 1. sai kuma kanne da yayye maza 4,da mata 2,
ka huta lafiya.

   Amsa

wa'alaikum assalam warahamatullah ,za'a raba gida hudu, a bawa mijin kashi daya, Diyar  kashi biyu ragowar sai a bawa 'yan'uwanata su raba,in darajarsu daya kuma karfinsu daya, duk namiji ya dau rabon mata biyu.


               Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

29/01/2017